Abubuwan Da Suke A Farkon Aure

0
94

FA’IDAR YIN AURE: Shi ne domin a samu kyakkyawan zama, soyayya da ƙauna, jinƙai da tausayi a tsakanin mai gida da matarsa. Kamar yadda Ubangiji yake cewa:

“Kuma akwai daga ayoyinsa, ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani’’. (Rum:21).

Domin karanta bayani akan Abin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa Danna nan

Idan muka duba wannan aya da kyau, za mu ga ashe mu mata ya zama tilas a kanmu, mu dinga tausayin mazajemmu. Kuma mu dinga nuna musu soyayya da ƙauna. Domin sai a wajen mace ne namiji ke samun natsuwa. Haka ma dai tilas ne ga miji ya dinga tausaya wa matarsa. Kuma ya dinga nuna mata ƙauna da soyayyarsa gare ta. Saboda duk lokacin da aka rasa soyayya da ƙauna a cikin aure, to za ka tarar rayuwar aure ta ɓaci. Don za ka tarar ana zaune amma ba daɗi wai mahaukaci ya ci kashi, abu kaɗan sai faɗa, sai munanan kalamai don ba a ganin girman juna. Wani ƙiri-ƙiri ma za ka ji yana cewa yana zaune da matarsa ne saboda akwai yara a tsakaninsu, Ita ma matar sai ka ga zaman ‘ya’yanta kawai take yi.

Saboda haka ne ma aka yi babi guda mai magana a kan abubuwan da suke ƙara soyayya, wanda aka zaƙulo mana kaɗan daga abubuwan da ke ƙara so da ƙauna a tsakanin mace da miji.

A cikin aure, akwai bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) domin Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:

Na rantse da Allah (S.W.T) na fi ku jin tsoron Allah, kuma na fi ku kiyaye dokokinsa. Sai dai duk da haka, nakan yi azumi, kuma nakan sha, nakan yi sallah (da daddare) kuma nakan yi barci, sannan kuma ina auren mata. Wanda ya yi kwaɗayin wani abin ba sunnata ba, to ba ya tare da ni”(Bukhari da Muslim)

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceAmfanin Ƙaho A Jikin Ɗan Adam
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke Ƙara Soyayya Ga Maigida