Salam alai dangina, Ku amsa domin ƙauna, Allah daɗo tsiran na, ga Shugaba Manzona, Mai son sa ba ya gaba.
- Tsira, aminci ƙara,
- Ga sahiban nan jera,
- Mai son su ba ya ƙyara,
- Sai so da ƙauna jera,
- Daɗo aminci Rabba.
- ———————————
- A yau akwai wani zance,
- Ku bi ni, kar da na mance,
- Batu na murna kunce,
- Na bayyano ba ƙifce,
- A zaurukan nan babba.
- ——————————–
- Lasan na yo tattaki,
- Cikin aminci ɗoki,
- Domin halartar fa biki,
- Na tsara baitin baki,
- Na jera murna babba.
- ———————————
- Abokanai sun zo wa,
- Ta ko’ina ba ƙiwa,
- Domin su nuno sowa,
- Cikar mutunta da yawa,
- Su shaidi ƙauna babba.
- —————————–
- Da safe in yai wanka,
- Ran Juma’a ba shakka,
- Da yamma yai tattaka,
- Gare ki sai sam-barka,
- Domin ku zazzaga hira.
- —————————–
- ƙarshen ta cuta mutuwa,
- haka ƙarshen gani soyewa,
- kuma ƙarshen fa so aurewa,
- A dabdale bidirewa,
- A so a kore gaba.
- —————————–
- Nura abokin kaina,
- Aurenka nai wa murna,
- Na tsara baitin ƙauna,
- Domin gabatarwana,
- Aure zumunci babba.
- —————————-
- Fa Nura kare haƙƙi,
- Ka bi su kar ka yi raki,
- Tuwo, tufafi ɗauki,
- Ka ba ta har fa a baki,
- Da rangwaɗar nan duba.
- ———————————
- Auren ga sunnar Manzo,
- Ku raya domin ƙwazo,
- haka Ku yi shi har ku yi tozo,
- Dan Ku amsa kiran Manzo,
- Don Ku zazzago so babba.
- ————————–
- Amarya zan yo kanki,
- Ki tsara kanki da kanki,
- Biyayya ba yin birki,
- Mijinki shi ne angwanki,
- Gare ki tamkar Baba.
- —————————
- Ki lallaɓa shi a komai,
- Danginsa so su da sosai,
- Ki tausaya mai ji nai,
- Ki toshe kunnen son rai,
- Allah ya kawo riba.
- —————————-
- Nayaya na tsara,
- Baiti fa sha uku jera,
- Hanyar zuwa nat tsara.
- NWAN uwa mai gyara.
domin samun karanta waƙoƙi danna koren rubutun nan