Salam ya ke muradina, Da safe na antayo ƙauna, Na bayyana sirrikan raina, Gare ki ina makwancina, Zo amsa min cikin son rai.
- Abar sona abar sona,
- Ya abar ƙauna abar ƙauna,
- kin zam abar marari a rayina,
- Yau ga ni da so cikar ƙauna,
- Cikar buri cikar komai.
- Gare ki masoyiya tawa,
- Ki ji ni da zantukan baiwa,
- Na ƙaunar nan da ba tsiwa,
- Cikin mararin cikar sowa,
- Na bayyana baitukan so dai.
- Idan na gane ki don ƙauna,
- Na manta abin dake raina,
- Cikar buri ki zo guna,
- Ki amshi buƙatuwar raina,
- Ki share min duhun komai.
- Ranar wanka Bahaushe de,
- Ya ce cibi waje buɗe,
- Nufinsa a wangame buɗe,
- Kowa ya gano ido buɗe,
- A san shi a san kalar komai.
- Kin san so ba a mai yarfe,
- Ba a ƙyamar tuwon safe,
- Zoben so ba a sa ƙarfe,
- Burina na tattaro lefe,
- Na kai ki garin da ba kome.
- Kin san so ba a mai kulle,
- Gararinsa yawa na ‘yan talle,
- Shuhurarsa a zuciya zille,
- A ganta a fuska ba kyalle,
- A san ya zarce duk komai.
- Idan na taho a motata,
- Cikin tafiya ta ƙasaita,
- Idan na gane ki ‘yar auta,
- Kina tafiya ta ƙasaita,
- Na manta batu na tuƙin dai.
- Kalarki daban a mataye,
- Sunanki daban na ‘yar yaye,
- Sautinki daban a ƙaraye,
- A soyayya ana maye,
- A sonki ko za na yo komai.
- Naman da ake kira soye,
- A cakuda kafi zabaye,
- A sa naman a sa maye,
- A sa gishiri a yo soye,
- A so haka duk ake komai.
- Maimaita aji fa sai dolo,
- A so kam ba a son gwalo,
- Ba a kome cikin salo,
- Jifa kam sai da ɗan qwallo,
- A so ba a barin komai.
- Baitin ƙarshe na ce santsi,
- Ya ɗebi mutum ya yo watsi,
- Ya farfasa kai ya yo rotsi,
- A soyayya a bar kutsi,
- Aure a gare ki ne komai.
- Ni Nayaya na ce ki dube ni,
- Ki min kallon da ba raini,
- Da zai mai she ni ɗan birni,
- Na sa kaya na sa rawani,
- Na so domin na zam komai.
domin samun karanta saƙo ga masoyiyata danna koren rubutun nan