NAZARI NA FARKO
Daula – kamar yadda masana hukuncin dauloli da kundin tsarin mulki na zamani ke bada ma’anarta – shi ne jama’ar mutane, dake rayuwa a kowane irin yanki ta fuskar dauwama, masu ƙarfin hukuncin dake ɗaukar nauyin tsara al’amuransu da jujjuya harkokinsu na ciki da waje.
Kuma kamar yadda ya zo cikin waɗansu mu’ujaman Larabci na zamani: Taron mutane mai yawa dake zama wani yanki ta hanya dauwama, masu cin gashin kansu na tsare-tsaren mulkinsu da yancin siyasarsu.
Wannan ma’anar Daula kenan ga isdilahi na zamani, amma wata ƙila ba zai yi daidai da ma’anar da malaman Larabci suka ambata ba, duk da cewa mafi yawa ga al’ada a kan tsamo ma’anar isdilahi ne daga asalin kalma, to, da za mu koma ga littafan Larabci da mu’ujamomi a kan tafsirin gundarin Kalmar (Daula) me za mu tarar? Suna cewa:
Kalmar Daula na nufin jujjuyawar zamani da kai komon dukiya, idan aka ce IDALA, – wadda kalma ce da aka tsamo daga Kalmar Daula – tana nufin rinjaye .
Kuma na daga cikin ma’anoninta shi ne; wata jama’a ta yi galaba a kan wata, a bisa wannan ma’anar ne hadisin Abi Sufyan na hirakla yake cewa a kan sha’anin Manzon Allah (SAW):
“za mu yi galaba a kansa, shi ma zai yi galaba a kanmu“
(1), amma Abu Ubaid ya ce: idan aka ce (Dulatun) da rufu’a a bisa dalun, sai ma’anar ta canza ta zama; wani abin dake jujjuyawa tsakanin mutane, yau a hannu wannan, gobe a hannun wancan, a bisa wannan ma’anar ne kuma maganar Allah Maɗaukaki ta zo: (domin kada ya zamo abin jujjuyawa tsakanin mawadatanku kaɗai) .
Idan muka dubi waɗannan ma’anoni, za mu ga ba su zo daidai da ma’anonin da masana kundin tsarin mulki da masana siyasar shari’ah suka bayar ba a kan ma’anar Daula, sai dai wataƙila ta hanya ɗaya daga cikin hanyoyi masu zuwa:
Na ɗaya: lura da abin da suka ambata na ma’anar ɗaukaka da rinjaye, za mu ga da yawan daulolin da suka gabata, sun kafu ne ta hanyar ƙarfi da galaba na mulki, tun daga Marwan Binl Hakam har ya zuwa wannan zamani namu, musamman ma idan muka ɗauki mazhabar masu cewa Khalifanci ta kafu ne ta hanyar ƙarfin iko da rinjaye da kuma wasu ababe daban, kuma wannan mazhaba ce mai zaman kanta, domin tana da masu ɗaukakata daga malaman fiqhu da na tafsiri daga malaman ahlussunnati wal jama’ah.
Na biyu: Duba ga abin da aka ambata na littafan Larabci na ma’anar abin da ake jujjuyawa, tare da lura da cewa, hukunci ba ya taɓa tabbatuwa a hannun mutum ɗaya har abada, sai dai kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:
(kuma waɗancan ranaku muna jujjuya su tsakanin mutane) (Suratu Ali-Imran: 140),
kuma wanda ke lura da sunnonin Allah a bayan ƙasa zai iya tabbatar da hakan;
(ba za ka taɓa samun wani canji ga sunnonin Allah ba, kuma ba za ka taɓa samun wani sauyi ga sunnonin Allah ba) (Suratu Fatir: 43).
To kamar yadda lafazin (Daula) a wajen malaman hukunci da kundin tsarin mulki, ke nuni a kan hukumar ƙoli, wadda ke sarrafa al’amuran mutane, kuma take hukunci tsakaninsu, haka za ka tarar da irin wannan ma’anar a cikin fikhunmu da kuma harshen Larabci.
Kamar yadda akan ambaci daula da khalifanci ko jagoranci ko imamancin (shugabancin) Ƙoli, kai waɗannan kalmomi ma da malamanmu suka saba amfani da su, har suka wallafa littafai da su yayin da suke magana a kan shar’antattar siyasa, sun fi gasgantawa da bayyana ma’anar Daula.
Ta inda za mu ga ma’anar Daula a harshen Larabci na kai mu zuwa ga ma’arta ta isdilahi cikin sauki, misali Kalmar Imara a cikin littafin Lisanul Arab tana nufin: sarki mai mulki mai gudanar da al’amuransa, asalin kalmar daga Imaratun ne, haka kuma Ulul amri su ne: shuwagabanni da malamai.
Haka ma isdilahin kalmar Imamanci yake a bayyane, kamar yadda Ibn Sidah ya ce: shi Imam shi ne wanda ake bi sarki ne ko waninsa, Aya ta zo a Alkur’ani:
(sai ku yaƙi sarakunan kafirci) (Surat Al-Tauba: 12)
kuma Imamin komi shi ne mai gyara shi, mai kafa shi, haka kuma khalifa shi ne Imamin mabiyansa, Imamin sojoji kuwa, shi ne jagoransu.
Amma kalmar khalifanci kuwa, ita ce ta fi wanzuwa a littafan magabata, sobada harshen zamaninsu yana taimakawa wajen amfani da ita, kamar yadda takan zo a Alkur’ani mai girma cikin ma’anar Imamanci da Mulki, Allah madaukakin Sarki yana cewa:
(ya Dauda (AS) haƙiƙa mun sanya ka wani khalifa ne a bayan kasa, sai ka yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya) (Suratu S: 26).
Imamul kurdabi (Allah ya yi masa rahama ya ce a kan ma’anar ayar: “Mun saka ka mai mulki don ka yi umurni da kyakkyawan aiki, ka kuma yin hani da mummuna, sai ka maye makwafin waɗanda suka gabace ka na Annabawa da Imamai salihai” .
Haka kuma kamar faɗar Annabi Musa ga ɗan uwansa Annabi Haruna (AS):
(Ka khalifance ga mutanena kuma ka yi sulhu, kada ka bi hanyar masu ɓarna) (Surat Al-a’raf: 26)
Ibni Manzur Ba’afrike yana cewa: “Khalifa shi ne wanda ke maye gurbin magabacinsa” amma Sibawaihi kuwa yana cewa: “An ɗaura lafazin kalmar ne a kan lafazin (fa’iil) ta yadda ba ya kasancewa sai ga namiji kaɗai” .
Idan muka zam mun gane ma’anar kalmar Daula a harshen Larabci da baMbancinta da kalmomin khalifanci, imamanci, jagoranci, shugabanci, za mu gane dalilin da ya sa Alkur’ani da Sunnah suka kauda kai ga amfani da kalmar Daula a kan ma’anar hukunci da mulki, haka kuma, don me ba mu sami wata alamar ta ba ga littattafan magabata yayin da suke magana a kan hukunci da abin da ya shafe shi na haƙƙoƙi da wajibai.
Idan kuwa har babu rowa ga ma’anar isdilahi, kamar yadda malaman usulu ke faɗa, to ni ban ga laifi ba, idan na yi amfani da kalmar Daula a rubutuna ba, duba ga harshen zamani wajen nuni a kan mulki da shugabanci da imamanci, da hukuma, musamman ma ba ni ne na farkon wanda ya fara amfani da hakan ba, akwai waɗanda suka rigaye ni daga cikin manyan malamai da masanan fikhu na wannan zamanin .
Idan kuma har haka ne, to ba zan sha wata wahala ba wajen fassara ma’anar Daula ba, fassara ta shari’ah duba ga cewa tana da haɗin gwuiwa da kalmar “khalifanci da Imamancin ƙoli da sarautar Musulunci, kalmomi ne guda uku masu bayar da ma’ana ɗaya”, kuma babu laifi mu ƙara kalmar Daula don ta cika ta huɗu da ma’ana ɗaya.
Domin karanta Mahangar Siyasa A Musulunce danna koren rubutun nan