Tarihin Marubuci Nasiru Garba Ahmad

0
87

Assalamu alaikum.

Sunana Nasiru Ahmad Garba. A lokacin karatu sunan Ahmad ɗin ya koma karshe. An haife ni a unguwar ‘Yan awaki da ke cikin birnin Kano, ran Lahadi, 16 ga watan Safar, 1384, BH. (4 – 2 – 1964). Na yi karatun Alkur’ani a unguwar Ƙoki, kasancewar a can na taso, ina wurin yayata.

Ban fara karatun zamani da wuri ba, domin sai a 1981 na gama makarantar Firamare Islamiyya ta ‘Yan awaki. Na yi makarantar nazarin addinin musulunci mai zurfi (School for higher Islamic Studies) ta Shahuchi (Aliya), daga 1981-1985.

Sai makarantar nazarin shari’ar musulunci ta Aminu Kano (Legel), a 1986-1989, inda na sami Diploma a harsunan Hausa da Larabci da nazarin addinin musulunci. Daga 1993-1996, na je Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato, inda na sami digirin farko a harshen Hausa.

A 2009-2010 na yi karatun neman digiri na biyu kan adabin Hausa fannin rubutattun waƙoƙi, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A 1984, na yi karatun sarrafa keken rubutu (Typewriting) ƙarƙashin hukumar yaɗa ilimin manya ta Kano. A 1992, na halarci wani kwas da Jami’ar musulunci ta Madina ke shiryawa don horar da malaman harshen Larabci da addinin musulunci, a Jami’ar Bayero ta Kano.

A 1999, na yi karatu ƙarƙashin “Sincere Writers Club,” inda na sami satifiket kan aikin jarida. Daga Janairu zuwa Disamban 2002, na yi karatu a “Alliance Francaise de Kano” inda na sami satifiket kan harshen Faransanci. Na yi nisa a karatun Diploma kan Faransancin, amma ban sami ƙarasawa ba.

A 2006, na yi karatu ƙarƙashin kwalejin horar da ma’aikatan mulki ta ƙasa (Administrative Staff College Of Nigeria -ASCON). A 2008, na yi karatu a “I.H.D.I.T.” (Institute for Human Development & Information Technology) da ke Tarauni Kano, inda na sami satifiket, da kuma Diploma (a 2011) kan sarrafa kwamfuta.

Na fara rubuta waƙa ran 15 ga Janairun 1983. A shekarar dai na rubuta wani littafin koyon ibada ga yara cikin rubutun Ajami, na kuma rubuta wani wasan kwaikwayo, wanda muka yi ni da abokaina, muka naɗa a rikoda, muna kwaikwayon wasan kwaikwayo na rediyo.

A 1985 na shiga ƙungiyar marubuta da manazarta waƙoƙin Hausa ta Nijeriya, reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin marigayi Mal. Aƙilu Aliyu a lokacin. Bayan ita, na shiga ƙungiyar marubuta waƙoƙin Hausa ta “Hikima Club,” ƙarƙashin jagorancin marigayi Abdullahi Sani Makarantar Lungu. A 1992, na yi ƙungiyar wasan kwaikwayo ta matasan Ɗambatta, lokacin ina aiki a can.

Yanzu haka ina cikin shugabannin ƙungiyar mawallafa ta kasa (ANA) reshen jihar Kano. Memba ne ni a ƙungiyar mawallafa littafan Hausa ta HAF Kano, da ƙungiyar marubutan Hausa ta Nijeriya (HAWAN), da ƙungiyar mawallafa ta Alƙalam Kaduna, da Tsangayar Adabin Hausa

Ni malamin makaranta ne. Na yi aikin koyarwa a makarantu da dama na Firamare da Sakandare, tun daga 1984 zuwan yanzu.

WALLAFE-WALLAFE

NA ADDINI

  1. Sahabbai Goma da aka yi wa Bushara da Aljanna (Wallafa)
  2. Yaƙin Badar (Wallafa)
  3. Addu’a da yadda ake yin ta (Wallafa)
  4. Huɗubobin Annabi Goma (Wallafa)
  5. Fassarar Umdatul Ahkami (Fassara)
  6. Fassarar Risala (Fassara – Ba a buga ba)
  7. Mas’aloli 70 kan Azumi (Fassara)
  8. Fatawoyi 50 kan Azumi (Fassara)
  9. Salatin Annabi: Matsayinsa da Hukunce-hukuncensa (Fassara)

NA LABARU

  1. Antar Ɗan Shaddadu 1-2 (Fassara)
  2. Abu Firaas 1-2 (Fassara)
  3. Ra’asul Guuli (Mai kan fatalwa) 1-4 (Fassara)
  4. Sha-Alwashi 1-2 (Fassara)
  5. Hikayoyin Marowata (Ba fassara ne kai-tsaye ba)
  6. Dare Dubu da Ɗaya (Sabuwar fassara) 1-5
  7. Garin Banza…. (Ƙirƙirarren labari ga hukumar A daidaita Sahu ta Kano)

NA ILIMI

  1. Guzurin Marubucin Waƙa (Wallafa)
  2. Ƙa’idojin Rubutun Hausa a Sauƙaƙe (Wallafa)

Akwai kimanin littafai goma da ba a buga ba

Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Jakadan Allah

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTsokacin A Kan Littafin Garina Abin Alfaharina
Labarin na GabaWaƙa Mai Taken Ladubban Tsuguno
Nasiru G. Ahmad
Haifaffen jihar Kano ne a unguwar 'Yan awaki. Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan harshe da adabin Hausa. Yana cikin ƙungiyoyi da dama na marubuta a ciki da wajen jihar Kano. Malami ne kuma mawallafin littattfai da waƙoƙi.