MOHAMMED BALA GARBA
(Ɗan jaridar da aka kashe ta hanyar aika masa wasiƙa mai ɗauke da bam a ciki)? Yau shekaru 37 ke nan da mutuwar ɗan jarida Dele Giwa, babban edita kuma jami’in kamfanin Newswatch, wanda aka kashe ta hanyar aika masa wasiƙa mai ɗauke da bam.
An haifi shi a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 1947 a garin Ile-Ife. Ya halarci Makarantar Local Authority Modern School da ke Lagere a garin Ile-lfe. Lokacin da mahaifinsa ya koma Kwalejin Oduduwa da ke Ile-Ife a matsayin mai wanki, Dele ya samu gurbin karatu a Kwalejin. Daga nan ya samu damar tafiya Amurka domin yin digiri inda ya yi digirinsa na farko a kan Turanci a Kwalejin Brooklyn a 1977.
Ya samu damar yin digiri na biyu a Jami’ar Fordham duk dai a Amurkan. Ya yi aiki da jaridar The New York Times a matsayin mai taimaka wa ‘yan jaridu na tsawon shekara huɗu kafin ya dawo gida Najeriya ya kama aiki da jaridar Daily Times. Dele ya rasu a ranar 19 ga watan Oktoban 1986 ta hanyar wani bam da aka haɗa da ambulak wanda aka kai masa gida a zamanin mulkin soja na tsohon shugaban mulkin soja, Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
An kashe shi a lokacin da yake karin kumallo tare da abokinsa Soyinka a gidansa da ke 25 a unguwar Talabi ta Ikeja da ke birnin Lagos. Ya rasu yana da shekaru 39 a duniya. Idan muka dubi yadda mutuwar tasa ta kasance, mutuwa ce a gidansa ta hanyar fashewar bam, wanda hakan shi ne abu mafi damuwa fiye da mutuwar. Wannan na iya zama dalilin da ya sa hatta bayan mutuwarsa ba a daina tambayar wanene ya kashe shi ba? Kuma me ya sa? Tambayar da har yau ba a daina yi ba.
Abin takaici ne ƙwarai da gaske yadda ‘yan jaridar Afirka suka fuskantar keta haƙƙoƙi da ‘yanci saboda bayyana gaskiya ko ‘yancin faɗin albarkacin baki ta hanyar tsorata su ko tsangwamarsu ko barazana gare su da hare-hare da duka har tsarewa ba bisa ƙa’ida ba; da kuma kamawa ko ɗauri tare da ƙwace kayan aikinsu a wasu lokutan.
Waɗannan suna cikin matsaloli da ‘yan jaridar Najeriya suke fuskata a lokacin da suke aikin tono wata gaskiya ko kuma almundahana. A Najeriya akwai wasu ‘yan jaridu da suka rasa rayukansu a yayin da suke tona asirin miyagu waɗanda suka aikata ba daidai ba.
Dangane da kisan Dele kuwa, Janar Ajibola Kunle Togun (tsohon shugaban SSS na lokacin) ya ce, “Akan Dele Giwa aka fara amfani da bam ɗin takarda wajen kashe mutum a Najeriya.” Ya bayyana hakan a lokacin da ya yi hira da Ridwan Kolawole na Jairdar Legit.ng a Abuja.
Ɗalibinku,
Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
08098331260
Marubuci/manazarci.
10 Ogusta, 2023.
Karanta Asalin Yadda Aka Samo Sunan Hausa Bakwai Da Banza Bakwai
Edita@rumasau-kallamu