Idan al’ada tana daɗewa ba ta zo ba sai bayan watanni 3 zuwa 6, wannan shi likitoci suke kira “amenorrhea”. A gaskiya wannan yanayin bai kamata a ce mace tana fama da shi ba. Idan kuma ya auku, to, yana nufin cewa mace tana da matsala kenan.
Amenorrhea ya kasu gida biyu kamar haka:
1. Primary amenorrhea: Wannan yana nufin daɗewa na farko ko kuma daɗewa na asali wanda al’ada take yi ba ta zo ma mace ba. Abinda yasa ake kiransa daɗewa na farko ko na asali shi ne yana faruwa ne ga mace budurwa wacce ba ta taɓa yin al’ada ba a rayuwarta, sai ya kasance ta kai munzalin da ya kamata a ce ta fara al’adar, to, amma sai ba ta zo mata ba.
Mafi yawanci budurwa tana fara al’ada ne tsakanin shekaru 9 zuwa 13. Don haka idan budurwa ta kai shekaru 16 zuwa 18 ba ta fara al’ada ba, to, wannan shi ne primary amenorrhea.
2. Secondary amenorrhea: Shi kuma wannan yana nufin daɗewar da al’ada take yi ba ta zo ba har na tsawon watanni 3 zuwa 6 ga babbar mace, watau ba budurwa ba.
Da primary amenorrhea da secondary amenorrhea suna faruwa ne saboda dalilai masu yawa, waɗanda suka haɗa da:
1. Yanayin da Allah ya halicci tsarin jiki kamar ɗaukar ciki, shayarwa, nisan shekaru (menopause) da sauransu. Idan mace tana cikin ɗaya daga cikin waɗannan yanayin, to, za ta fuskanci ɗaukewar al’ada.
2. Shaye-shayen magunguna kamar na family planning ko kuma domin warkar da wata cuta da take damun mace.
3. Lahani wanda ya sami tsarin jikin mace na haihuwa (reproductive system defects) kamar jakar da take ɗauke da ƙwaya-ƙwayan haihuwa (ovary) ko mahaifa (uterus) idan suka sami matsala.
4. Rashin daidaiton zubar sinadarai a cikin jiki (hormonal imbalance).
5. Yin ayyuka na wahala.
6. Damuwa (stress).
7. Kasancewar mace ta zamo mai tsananin ƙiba ko tsananin sirantaka.
Hanyar kaɗai da za a iya magance amenorrhea ita ce idan aka tuntuɓi likita ya yi bincike mai zurfi domin gano wasu daga cikin dalilan da suke haifar da shi, daga nan sai a bayar da maganin da ya dace.
Karanta Yadda Tsiron Mahaifa Yake
Edita@rumasau-kallamu