Kamar yanda aka sanar ranar Asabar aka buɗe gari, ba ƙaramin daɗi wannan buɗewar ta yi wa Mustapha ba. Tun waje ƙarfe takwas ya shirya sannan ya shirya yaran gaba ɗaya, sai dai da ya duba lokaci ya ga safiya ta yi da yawa ya bari zuwa wajen tara da rabi sai su fita; domin so yake su je su ɗauko Khadeeja sannan idan ya kawo ta gidan ya bar su ita da yaran ya wuce gidan hajia ya gaishe su.
Sai wajen goma saura sannan suka kama hanya. Tun kafin ya gama tsayar da motar yaran suka ɓalle ƙofofi suka fice suka shiga gidan da gudu, bayan sun gaida Mommy wadda take zaune a parlor tace su shiga ɗakin Anti Nabila su taso Antin tasu inda take barci.
Jin su kawai ta yi a kanta suna shewa, ba shiri ita ma ta miƙe. Nan take aka shiga ba ta labarin abubuwan da suke faruwa a gidan. Ita ma ta yi kewar yaran kuma ta ji daɗin ganinsu sosai. A farfajiyar gidan Mustapha ya tsaya sai da Mommy ta tura Nabila ta shigo da shi, ta buɗe parlor ɗin baƙi ta yi masa iso inda Baffa yake jiransa don shi ma fita zai yi jin isowarsu ya sa ya tsaya.
Bayan sun gaisa Baffa ya tambaye shi wajen su Alhaji sai ya yi gyaran murya yace ‘Yauwa, ina ga za ka bar Khadeejan ta ɗan ƙara kwana biyu don mahaifiyarta tace akwai abubuwa suke yi na gyara wanda al’ada ta tanada. Don haka ina ga ka bar ta ta ɗan ƙara kwana biyu mu gani.’
‘Eh, kuma da zuwa muka yi mu tafi da ita Baffa.’ ‘Allah sarki, ina ga a ɗan ɗaga musu ƙafa su gama shirye-shiryensu, ba za su ɗauki lokaci ba su ma na sani in sha Allah.’ Babu yanda ya iya kwarjinin Baffa ya sa ba zai iya yi masa wani dogon musu ba, don haka sai kawai ya sunkuyar da kai.
Baffa ya yi masa sallama ya fice ya bar shi a nan cike da taƙaici; yaya Baffa zai yi masa haka? Wannan ɗin shawarar Mommy ce ko kuwa dai Khadeejan ce ba ta son ta koma? Amma dai bari Khadeejan ta fito ya ji daga bakinta. Ya gyara zama ya haɗiye malolon da ya tokare masa maƙogoro ya daɗa saita fuskarsa da ya ji motsi ana taɓa ƙofar daga cikin gida, ya miƙe ya koma kan kujerar zaman mutum ɗaya ya zauna.
Khadeeja ce ta shigo da sallama, bayan ya amsa ta nemi guri ta zauna a kan three seater ta gefen da ya fi kusa da shi, bayan sun gaisa tace ‘Ya kuke kai da yara? Sun ce min ku kaɗai ne a gida ko gidan Hajia ba ka kai su ba. To ina zan kai su gari yana kulle, dole haka muka zauna mu kaɗai; don ma dai Ummi tana taimakawa, jiya ne kawai da shekaranjiya aka ce ba ta da lafiya.’
‘Allah sarki ai iyayenta suna mana kirki gaskiya, Allah ne kawai zai biya su.’Suka yi shiru na ɗan lokaci; idan ma da yana da niyyar gaya mata wasu kalamai masu daɗi to Baffa ya goge masa haddarsu, yanzu haushin kowa ma yake ji. Sai dai fatansa ɗaya ya ga ko zai iya tsara Khadeejan ta canza wanna tsarin don yana jin idan tace tana son ta koma ba za a hanata komawa ba.
Yace ‘Uhm, da ni fa zuwa na yi mu tafi amma na ji Baffa yace kamar za ki yi wanka ne ko gyara wai sai an kwana biyu za ki dawo.’ Ta ɗan gyara zama ‘Eh, Mommy tace a bar ni sai na yi wankan jego kuma dai da ‘yan gyare-gyare na ƙara hutawa sai na koma.’
‘Wai ba ki gayawa Mommy cikin bai ƙarasa wata uku ba ma, na zata haihuwa ake wa wankan jego. Ke dai idan akwai wani dalili ki gaya min sai mu ga yanda za a yi.’ Ta yi ‘yar dariya ‘Shi ne dai dalilin ga shi na gaya maka, don ka ga har yanzu ma ban gama jini ba kusan kwana biyar kenan.’
‘Uhm! To yanzu babu yanda za ayi mu koma yau, na san ai duk wani gyara ba zai gagare ki ba tunda kin sami lafiya ga laulayin ma yanzu babu. Gaskiya ka yi haƙuri kawai mu yi yanda Baffa ya faɗa, kwana nawa ne za ka ga ma na dawo gidan. Ya sunkuyar da kai; tabbas wannan tsarin na Khadeeja ne sai dai bai san laifin me ya yi mata ba take son ta yi purnishing ɗinsa haka.
Muryarta ce ta katse masa tunani ‘Kada ka damu in sha Allahu zuwa bayan sallah zan dawo, ka ga kafin nan ma Mommy ta samo min mai aiki. Bayan sallah? Haba! Wajen sati uku fa kenan? Ai na zata duk inda aka kai nextweek kin gama hutawar. Kuma mai aiki ai Habi za ta dawo bayan sallah ko?’
‘Ban sani ba, wai dai don kada ta ba ni mamaki gara a samo min wata tunda ga aikin gida ga hidimar yara sannan ga makaranta zan koma idan an buɗe gari ka ga ina buƙatar taimakon mai aiki ko.’ Sai a lokacin ma sannan ya tuna ashe tana zuwa jami’a; amma dai shi har yanzu bai gane dalilin da yasa ba za ta koma yau ɗin ba har sai nan da sati biyu.
Ya dai fahimci so take kawai tace aikin gida da na yara ya mata yawa, kuma shi bai ga wani wahala a ciki ba tunda Ma’u ma ko sau ɗaya ba ta taɓa ɗaukan mai aiki ba haka take komai da kanta. Kawai dai ya fahimci Mommyn Khadeeja tana da son zuciya da iko shi ne take son ta juya shi kamar yanda take juya Baffansu, kuma gaskiya shi ba zai ɗau wannan ba.
Haka dai ya gama kwana-kwanarsa ya tashi ya kwashi yaransa suka wuce gidan Hajia cike da takaicin Mommy Khadeeja wadda duk ita ya ɗorawa laifi, gani yake kamar ita ce take juya Khadeeja da Baffan gaba ɗaya.Tuni Mommy ta ba da umarni a samo mata ‘yar aiki.
Ransa a ɓace ya shiga gidan Hajia. Yana shiga ya tarar da Yaya Jidda a gidan ita da yaranta, suna zaune a parlor ɗin Hajia suna hira. A gaggauce yaran suka gaisa da Hajia da Yaya Jidda suka shige wajen Baffa da gudu inda yake zaune yana jiran Kamal ɗan autan gidan ya dawo daga shan mai ya kai shi unguwa.
A nan Mustapha ya zauna wajen Hajia da yaya Jidda, bayan sun gaggaisaya dubi Yaya Jidda yace ‘Ke Yaya sai kace jira kike a buɗe gari ki taho, har ma kin riga ni zuwa.’ Ta yi dariya tace ‘Ni dama babu ni a lockdown in dai gidan nan ne kullum sai na zo, Alhaji ma ya gaji ya bar ni.’
Hajia ta dube shi tace ‘Ya jikin Khadeejan?’ Ya ɗan karkata kai yace ‘Da sauƙi. Jiya ma mun yi waya da Mommyn tata ai, ta dawo gidan ko sai kun fita daga nan za ku ɗauko ta?’ ‘Mtseww!’ Ya ja gajeran tsaki sannan ya cigaba ‘Daga can muke, wai Mommyn tace ba ta gama hutawa ba kuma sai an mata wanka da gyara za a dawo da ita zuwa bayan sallah.’
Hajia ta gyara zama ta kama haɓa ‘Ikon Allah, to kai kuma sai kace me?’ To Hajia ya zan yi da su; shi ma baban nata bayan tuni muka gama magana da shi yace nazo na ɗauke ta ina zuwa kuma ya canza zance; yace wai na bar ta. Ita ma kuma Khadeejan kamar haka ta zaɓa, kin ga kenan babu yanda zan yi da ita. Da a ce ma ta ba ni haɗin kai ne da za ta iya canzawa Mommyn ra’ayi don na kula kamar wannan shirin duka nata ne.’
Kafin Hajia tace wani abu Yaya Jidda tace ‘Ai kuwa lallai shiri, ɓarin ne sai an yi wani wanka da gyara? Lallai matan nan, ni fa dama shi yasa yaran ‘yan bokon nan ba sa wani burge ni, ciki fal iyayin tsiya.’ Hajia tace ‘To me suke nufi? Wannan duk ranar da ta haihu ai sai ta shekara sun gyara sannan za su ba ka ita. To yanzu ya suke so ka yi da waɗannan ‘yayan, ko kuwa don ba ita ta haife su ba?
Tunda ai da nata ne haɗawa za su yi da su ko kuma ita da kanta ma ba za ta yarda ta tafi ta bar su ba. Wannan ai ba tsari ba ne ba ma, sai dai da yake dama an bar gidan a hannun mace ai dole a ga son zuciya irin wannan.’ Ya gayara zama yace ‘Hmmm! Su suka sani kuma.’
‘To yanzu ya za ka yi da yaran? Ko kuwa haka za ku haƙura ku yi zamanku tunda dama babu fita?
Ko kuma nan za ka bar mini su sai mu yi zamanmu, ka ga na sha allura a wajen Dr. Nasreen. Ya dubi Yaya Jidda sannan yace ‘Da tunani nake na bar su wajen Yaya Jidda sai na koma na ɗauko musu kayansu, in ya so sai a bar su iyayen Khadeejan mu ga lokacin da zasu dawo da ita.’
Har hajia ta buɗe baki za ta yi magan Yaya Jidda ta tari numfashinta ‘Eh to kuma ka ga da sai mu yi zaman mu, sai dai ka san gidan namu ƙarami ne wajen kwanan zai iya yi musu kaɗan gaba ɗaya da nawa yaran. Ko nan ɗin ma ka bar su wajen Hajiyan ai duk muna tare tunda kullum ni nake zuwa na tsaya a kan hidimar gidan.’
Suka yi shiru na ɗan lokaci kowa da abinda yake tunani, jiamwa kaɗan hajia tace ‘To hakan ma ai ya yi, ka bar min su a nan tunda ga Baito nan tana nan za ta iya duk wata hidimarsu. Tunda ka ga ai ba ma tsari a ce kana zaune a gida daga kai sai yaranka yaran ma mata.’
‘Ba damuwa, zan je na ɗauko kayansu kafin biyar ɗin ta yi. Ya tashi ya fice wajen Alhaji. Yaya Jidda ta bi bayansa da kallo; ya ba ta tausayi amma gaskiya ba za ta karɓi su Afaf ba, gara dai a nan ɗin. Can gidanta ita ma ga nata yaran waɗanda idan ta ga dama nan take turosu wajen Hajia su ci abinci su yi komai sannan kuma a ƙara mata wasu? Gaskiya ba za ta iya ba.
Sai da la’asar ta kusa sannan ya fita yaje gidan ya haɗo musu kayansu ya kawo sannan ya koma ya bar su a nan
Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Takwas
Edita@rumasau-kallamu









