Mijin Marigayiya Babi Na Shida

0
6

khairatu.shehu

A gajiye ya shiga gidan wajen ƙarfe tara na dare, yana shiga yaran suka taso da gudu gaba ɗaya tun kafin ya gama rufe ƙofar motar suba cewa ‘Abba ina Anti Khadeeja?’ Ya ɗauki shukura ya kama hannun Nasreen yana cewa ‘Tana asibita, likita ya kwantar da ita, amma gobe in sha Allahu zan je na taho da ita.’

Ya tattara su suka shige cikin gidan. Yana shiga bayan Ummi ta yi masa sannu da zuwa ya sallame ta ya fito ya raka ta sai da ta shiga gida ta kirawo masa babanta ya yi godiya sannan ya koma gida. Sai da ya biya sallar Magriba da Isha’I duk da yunwar da yake ji sannan ya zo ya zauna a parlor a gajiye, ya dubi Afaf wadda take kwance tana yin game a tab ɗinta yace ‘Afaf ɗauko min flask da kayan shayi.’

Ta miƙe ta shiga kitchen ɗin, jimawa kaɗan ta fito ɗauke da kayan shayin bayan ta ajiye tace Abba babu ruwan zafi a flask ka jira na dafa maka, wanda Anti ta zuba mun sha shayi da shi mu da Ummi.’

‘No, bar shi kawai. Ɗauko min zoɓo ki kawo min ragowar abincin da kuka ajiye na ci, yunwa nake ji.’ Kafin ta ba shi amsa Habib yace ‘Abba ai tun kafin ku fita zoɓon ya ƙare a nan, ka manta? Kuma dama shi kenan wanda Anti ta zuba ragowar na jiya ne.’

Kafin yace wani abu Afaf tace ‘Abba babu fa abincin ma sai dai ragowar rice and stew, gaba ɗaya dankalin muka cinye kuma da peppersoup ɗin, amma akwai ragowar watermelon a fridge. Ko na dafa maka indomie?’

Ya kalle ta yana shafa kai na ɗan lokaci, ya ma rasa me zai ce mata saboda yanda gaba ɗaya ya jigata saboda yunwa, coke kawai ya samu a asibiti da wani guntun burodi ya ci. Ya zata za su rage abincin amma wai duk sun ciye. Muryar Afaf ce ta katse shi tana cewa ‘Bari kawai na dafa maka indomie ɗin Abba.’

‘No, bari na shiga kitchen ɗin na gani.’ Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ya ɗan ɗauki yana kallon kitchen ɗin bai ma san ta inda zai fara ba; har ya ɗauki tukunya zai dafa indomie sai kuma ya tuna ai akwai cereal, don haka ya mayar da tukunyar ya ajiyeta a muhallinta.

Ya zuba ruwan zafi a kettle ya tafasa ya haɗa cereal, ya ajiye ya fiddo kankana daga fridge ya yanka sannan ya ɗauko ya dawo parlor ɗin. Yana zama Shukra ta matso tana dariya ‘Abba zan sha golden morn ɗin.’Ya bi ta da kallo da cokali a hannunsa; ba ta taɓa ba shi takaici ba kamar a wannan lokacin don ya tabbatar sun ƙoshi tunda gashi sun cinye duk wannan uban abincin da Khadeeja ta dafa.

Ya dubi Afaf yace ‘Tashi ki ɗauko cereal, ki haɗo min da tea flask da komai na haɗa mata.’ Kafin Afaf ta dawo Nasreen tace ‘Abba ni ma zan sha.’ Don haka tana kawowa ya sa ta koma ta ƙaro kofi, ya haɗa musu cereal ɗin su biyun.

Babu wadda ta sha cokali uku a cikinsu, suka tashi suka bar masa a nan. Kafin ya gama cinye nasa abincin duk sun fara gyangyaɗi don haka ya sa Afaf ta ɗauko musu kayan baccinsu ya shirya su bayan ya raka su sun yi brush sun yi fitsari. Bayan sun kwanta sannan Afaf da Habib su ma suka shirya, Afaf ta zauna a gefen gado ta yi tsuru-tsuru shi ma Habib sai ya hau katifarsa ya kwanta yana zare ido.

Yana tsaye daga bakin kofa yace ‘Yaya dai Afaf? Ki kwanta mana, ko akwai wata damuwa ne?’ Ta jijjiga kai tace ‘Kawai tunawa na yi da Mommy, ita ma muna bacci ta mutu.’ Ya gaji sosai ga kansa yana sarawa, babu abinda zai iya yi musu na lallashi, ya buɗe baki a gajiye yace ‘In sha Allahu babu abinda zai sami Anti, ku yi addu’a ku kwanta ku yi bacci kawai.’

Habib shi ma ya tashi zaune yana share ƙwalla ‘Wallahi Abba ni ba zan ma iya baccin ba, Allah ya sa dai kada Anti Khadeejan ma ta mutu ta bar mu. Har yanzu idan na tuna Mommynmu sai na yi kuka.’ Kafin ya yi magana ita ma Afafa ɗin hawaye ya fara bin fuskarta, ta sunkuyar da kai ta sa masa kuka har da shassheƙa.

Ji ya yi kamar ya ɗora hannu a ka ya sa ihu; ina ma yaran nan za su bar shi ya huta, yanzu ya zai yi da su? Manyan cikinsu da yake ganin su ne ba za su bashi matsala ba su ne suke so su hana shi bacci. Ya ƙarasa ya zauna a kusa da Afaf ya rungumota yana cewa ‘In sha Allahu babu abinda zai sameta, ku daina kuka ku yi mata addu’a Allah ya ba ta lafiya. Goben nan ma zaku ga an sallamota.’

Ta fara share hawayenta, Habib wanda shi ma ya taso ya dawo kusa da ita yace ‘Abba to ka kirawo mana ita a waya mu yi mata sannu.’ Ya zaro wayarsa daga aljihu yana cewa ‘To ai da bana son kiranta saboda kar na dame ta don an yi mata allurai, ban sani ba ko har da ta bacci a ciki. Amma bari na kirawo ta sau ɗaya idan ta ɗaga shikenan idan kuma ba ta ɗaga ba sai mu haƙura da safe ma sake kira.’

Ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga. Murya ƙasa-ƙasa tace ‘Hello.’Yace ‘Hello, Khadeeja ba ki yi bacci ba?’ ‘Na ɗan yi, farkawa dai na yi kuma na ji wayar tana ringing. Ai tun ɗazu aka gama wankin cikin har na ɗan ci abinci.’ ‘Sannu. Wankin cikin ba wahala kenan?’

‘Hmmm! Akwai wahala ba kaɗan ba, kawai dai da an gama aka ba wa mutum maguguna sai ya sami relief.’ ‘Sannu. Afaf ce dama ita da Habib wai ba za su iya barci ba sai sun yi miki sannu.’ Ta yi murmushi mai sauti domin ta ji daɗi har cikin ranta, ta tabbatar cewa yaran nan suna ƙaunarta kuma da zai barta da su komai nasu zai zo da sauƙi amma shi komai gani yake kamar za ta cuce su.

Muryar Afaf ce ta katse ta bayan da Abbanta ya ba ta wayar ‘Anti.’ ‘Na’am Afaf, ya aka yi ba ki yi bacci ba.’ ‘Babu komai Anti, ya jikin naki? Ke ya aka yi ba ki yi baccin ba? Ta yi ‘yar dariya tace ‘Yanzu zan yi Afaf, kuma na sami lafiya don likitan ma ya ce gobe za a sallame ni.’ Suka ɗan taɓa hira sannan ta yi mata sallama ta miƙawa Habib wayar. Bayan sun gama gaba ɗaya ya karɓi wayar ya katse ya yi mata sai da safe. Ya yi musu sai da safe suka kwanta, har zai kashe fitilar Afaf tace ‘Abba kada ka kashe mana fitilar, in an jima ka zo ka kashe.’

Haka ya bar musu fitilar ya fice. Can bayan awa ɗaya ya gama abinda yake yana so ya kwanta saboda ya gaji ya zo zai kashe musu fitilar, yana kashewa Afaf da Habib suka haɗa baki a lokaci guda suka ce ‘Abba kada ka kashe fitilar.’ Da mamaki yace ‘Kai! Me kuke ba ku yi barci ba?’

Afaf tace ‘Abba to ni dai na kasa bacci, da ma za ka taya mu kwana.’ Habib yace ‘Eh wallahi Abba don ni wallahi tsoro nake ji.’ Takaici ya kama shi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suna zare ido ya je ya kwanta? Wannan wacce irin fitna ce a daren nan ga shi ya gaji.

Baya son barinsu su kaɗai don haka ya wuce ɗakinsa yaje ya shirya ya rufo gidan sannan ya dawo nan ɗakin; katifar Habib ƙarama ce ya san ba za ta ishe su ba don haka kawai ya gyarawa Nasreen da Shukra kwanciya ya ɗan sami waje a gefen gadon ya kwanta bayan Afaf ta kwanta a ɗaya gefen. Ya yi addu’a ya tofa musu sannan yace kowa ya rufe idonsa kada ya sake jin motsinsu.

Tunda ya kwanta yake jin wani ɗan ɗoyi haka, idan iska ta busa sai ya ji kamar ɗoyin ya buso cikin ɗaki idan iskar ta wuce kuma sai ya daina ji. A haka bai san lokacin da bacci ya ɗauke shi ba. ‘Subhanallahi!’ ya faɗa bayan ya yi firgigit ya tashi, ya kai hannunsa ya taɓa inda yake kwance daidai ɗuwawunsa ya ji shi a cikin ruwa sosai. Ya ɗaga hannun yana kallo da tsananan mamaki ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’ Ya sake fada a fili.

To fitsarin kwance ya yi ko me? Gashi yaran duk sun yi bacci balle yace wani ne ya zuba masa ruwa; tunda shi dai ya san ba ya fitsarin kwance. Motsin Shukra da ya ji a kusa da shi ne ya tabbatar masa da cewa ita ce ta yi fitsarin, ya miƙa hannu ya taɓata ya ji ta a jiƙe amma tana ta baccinta hankali kwance.

Ya kai hannu zai janye Nasreen daga kusa da ita ya jita itama a jiƙe ‘Tab!’ ya faɗa a fili. Kenan duka su biyun suke fitsarin kwance ko kuwa yau suka fara? Don shi tunda Khadeeja ta tare a gidan nan sau ɗaya ya taɓa ji an ce Shukra ta yi fitsari. Ya kalli Afaf wadda ita tana can ta takure a ƙarshen gadon tana baccinta, ya danna wayarsa ya kalli lokaci ya ga ƙarfe biyun dare.

Ba zai iya tashin yaran nan ba don haka ya lallaɓa ya sauka daga kan gadon ya fice ya shiga ɗakin Khadeeja ya samo zanin gado ya zo ya rufe su saboda kar sanyi ya dinga kaɗa su ga danshi. Bayan ya gama rufe su ya zo ficewa daga ɗakin ɗoyin da yake ta ji ya sake dukan hancinsa; wannan ɗoyin ai sai ya kumburawa mutum ciki.

Kamar daga banɗaki ɗoyin yake fitowa don haka ya koma ya buɗe ƙofar banɗakin ya shiga, ya karasa ya leka toilet din ya tarar babu komai a ciki duk da haka dai ya danna flushing ya juya zai fita. A daidai bakin kofa daga jikin bango ya ci karo da fo ɗin Shukra wanda ɗazu Afaf ta cire wandon Shukra mai ɗauke da kashi ta jefa a ciki. Pant ɗin yana nan da kashin a yanda ta ajiye har ya fara bushewa amma duk ya ɗumame bandaki da ɗoyi.

Ya ɗan ja baya kamar a firgice, to wa Afaf ta ajiyewa wannan kashin? Yanzu ya zai yi da shi ga shi duk ya ɗumame gidan da wari. Ya ɗaga hannuwansa ya zuba a aljihu, danshin da ya ji ya tuna masa cewa wandon a jiƙe yake da fitsrin Shukra ce ko Nasreen shi ma bai sani ba. Ya yi tsaki ya fito daga banɗakin ya wuce ɗakinsa yana tunanin yanda zai yi da kashin, ga shi a jikin pant yake balle ya sa a toilet ya yi flushing.

Sai da ya yi wanka ya canza kaya sannan ya fito daga ɗakin, yana fitowa ya ji warin kashin nan har parlor ɗin saboda ya bar kofar a buɗe. A fusace ya wuce kitchen ya ɗauko ƙatuwar baƙar leda ya zo ya ɗauki fo ɗin ya ƙulle a ledar, ya sake ɗauko wata ledar ya ƙara ƙullewa sannan ya ɗauki mukulli ya buɗe ƙofa ya fice ya jefa a shara; gari yana wayewa zai sami yaro ya fitar masa da sharar.

Ya san dai Shukra ta iya hawa toilet yanzu, duk da idan ta so rigima sai tace sai ta hau fo amma shi dai ya zubar don ba zai iya wankin kashi ba kuma ba zai iya bari Afaf ta yi ba ta zo ta yi musu jagwalgwalo da kashi. Yana dawowa cikin parlor ɗin ya kalli agogon bango ya ga ƙarfe uku har ta wuce, abinda ya yi masa saura bai fi awa ɗaya da rabi ba a yi assalatu.

Sai a lokacin ya tuna ba shi ma da abincin sahur, ga shi kuma ko a lokacin ma yunwa yake ji balle yace zai yi ɗore. Kai tsaye ya wuce kitchen ya ɗora indomie sannan ya tafasa ruwan shayi; nan da nan ya juye indomie ɗin a plate ya ɗumama stew ya zuba sannan ya haɗa shayi, ya kwaso ya dawo dining table ya fara ci.

Tun kafin ya haɗiye lomar farko ya fara jiyo hayaniyar Shukra a ɗakinsu, yana zuba loma ta biyu ta buɗo ƙofar ɗakin ta fito tana kuka tana ‘Antiiii..’ Ya ajiye cokalin yace ‘Menene Shukra?’ ‘Shayi zan sha Abba’ Har cikin zuciyarsa takaicinta ya kama shi, to amma ya zai yi da ita? Haka ya kirawo ta ya zaunar da ita a kan kujera, tun kafin ya gama gyara mata zamanta zarni ya cika masa hanci; sannan ma ya tuna ta yi fitsarin kwance.

Ya gyara mata zama yace ‘Bari na gama sahur sai na haɗa miki shayin.’ Ya ɗauki cokali ya zuba loma a bakinsa yayin da ita kuma ta fara mutssike ido tana kuka. ‘Menene kuma?’ ya tambayeta ‘Yunwa nake ji, shaaayiii.’ Ya duba agogon wayarsa, saura bai fi minti goma sha biyar ba a yi assalatu ga shi ba ya jin zai kai azumin nan idan bai yi sahur ba, ya kalle ta yanda take ta kuka kamar wadad aka ciza.

Bai taba jin haushin Shukra kamar yau ba, amma babu yanda zai yi. Haka ya juye mata rabin shayin da ya haɗa zai sha ya saka mata madara da milo ya miƙa mata sannan ya cigaba da cin abincin. Yana yi yana kallon lokaci saboda kar a kirawo assalatu. Haka ya ci abincin nan ya yi sauri ya kwankwaɗe shayinsa rabin kofi sannan ya ɗora da ruwan sanyi duk a lokaci guda.

Yana ajiye kofin aka fara kiran assalatu, ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana mayar da numfashi. Shukra da take kan kujera tana gyangyaɗi bayan ta shanye shayinta ta taɓo shi tana cewa ‘Abba kashi zan yi.’ A ɗan zabure ya dube ta yace ‘Kashi Shukra?’ Cikin halin ko in kula tana murje idonta tace ‘Um.’ Ta fara ƙoƙarin sauka daga kujerar da take zaune.

Ya jijjiga kai cike da takaici; su wai yara ba a hutawa da hidimarsu ne? Tunda ya dawo daga asibiti ake abu ɗaya ga shi duk yana neman fita daga hayyacinsa amma babu alamar sauƙi. So yake ma ya sami natsuwa ya turawa Khadeeja message ta whatsapp ya ga ko tana online amma ba su ba shi time ba, a halin yanzu ma kansa ciwo yake ga bacci duk kansa ya cushe bai ma san ta ina zai fara ba.

Haka ya bi bayanta har banɗaki, Allah ya taimake shi ba ta ma nemi fo ba ya taimaka mata ta hau toilet ta yi kashinta. Yana zaune a gefen gadonsu ya jiyo ta daga banɗakin tana cewa ‘Abba na gama. Gaban shi ya faɗi da ya tuna wai shi take sa rai ya yi mata tsarki; ya juya ya kalli Afaf wadda take baccinta hankali kwance.

Ya san idan ya tashe ta za ta yi mata tsarkin to amma fa ita ma bata kwanta da wuri ba. Ya jijjiga kai ya mike bayan da ta sake maimaita masa ta gama a karo na uku. Haka ya tashi ya shiga banɗakin ya wanke mata kashin ya wanko hannunsa ya fito ya canza mata kaya ya mayar da ita ya kwantar da ita a kusa da Habib saboda katifar kan gadon ta jiƙe; zuwa lokacin masallatai duk sun riga sun tayar da sallah.

Yana fitowa daga ɗakin yayi alwala ya ta-da sallah a ɗakinsa, yana zaune a kan dadduma yana azkar Nasreen ta turo ƙofa ta shigo ɗakin, ta ƙaraso ta faɗa jikinsa tana cewa ‘Abba na tashi, ba ka dawo mana da Anti Khadeeja ba?’ ‘Eh, sai an jima.’ Ya faɗa yana ture ta. ‘Ki je ki ce Ant….’ Sai kuma ya tuna Antin ba ta nan don haka ya gyara zance yana ƙoƙarin miƙewa ‘Mu je na wanke miki jiki ki canza kaya sai ki yi sallah.”

‘Abba ni yunwa nake ji.’ Ya ɓata rai yace ‘Sai an canza kaya kuma kin yi sallah.’ Haka ya yi ta fama da yaran nan, ga shi ita Afaf ma fushi take da shi saboda bai tashe ta sahur ba tunda Anti tana tashinta tana yin azuminta. Sai wajen ƙarfe takwas na safe sannan ya tashi ya koma ya roƙo Baban Ummi ta shigo ta karɓi yaran don yana son ya tafi asibiti wajen Khadeeja. Yana shiga ɗakinsa ya zauna a gefen gado ya danna mata kira.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Biyar

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAbubuwan Da Ke Haddasa Rashin Zuwan Al’ada (AMENORRHEA)
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.