Nason Al’adun Yarabawa A Kan Wanzancin Hausawa

0
24

A wurin Yarabawa ayyuka makamantan na wanzanci Hausawa akwai mutane daban-daban waɗanda suke aiwatar da su a tsakanin mutanen wannan al’umma. Misali ‘bonjamo ko oloola’, suna ne wanda suke kiran dukkan mutumin da yake yin wasu ayyuka irin su tsagar gado da yin kaciya da makamantansu.

Haka kuma suna kiran wanda yake yin aski kawai da sunan ‘fari – fari’ ko ‘akola’. A saboda haka akwai wasu al’adun Yarabawa waɗanda suka yi naso cikin al’adun wanzanci na Hausawa.

Cire Belun-wuya

A al’adar Yarabawa ba su damu da cire wa jariran da aka haifa masu belun-wuya ba, don irin wannan aiki ba ya cikin al’adunsu. Har ma idan an sami wata matsala makamanciyar wannan, sai su ba wanda yake fuskantar matsalar maganin gargajiya ya sha ko ya shafa a wurin da lalurin yake (YASASHL, 6/2/2006).

Irin wannan al’amari ya yi tasiri sosai a wurin wasu Hausawa waɗanda suka daɗe a ƙasashen Yarabawa, domin kuwa akwai waɗanda ba a cire wa jariran da aka haifa masu belun-wuya da belun-mata musamman a wannan zamani.

Wannan tasiri ya biyo wasu Hausawa waɗanda suka baro ƙasar Yarabawa suka koma garuruwansu na asali a ƙasar Hausa, don kuwa a nan ma ko da an yi masu haihuwa ba sa kiran wanzami domin ya cire wa jariransu belun-wuya ko belun-mata (UƊ da MBT da MAHD da MAA da MAMI da HZO da MASO da MAIA da HR, 7 da 8 da 9 da 10/2/2006).

Wannan al’ada ta Yarabawa ta yi naso a kan wanzanci ne saboda ire-iren waɗanda suka yi koyi da ita ba sa bari wanzamai su je gidajensu don yin ayyukan wanzanci. Wannan al’amari ya shafi yadda ake gudanar da wannan sana’a yadda wasu wanzamai suke rasa ayyukan yi.

Nason Al’adun Yarabawa Kan Askin Jarirai na Suna

A al’adar Yarabawa ba dole ne a yi wa jaririn da aka haifa aski ba, idan ma ta kama a yi, ba dole ne a yi shi a lokacin da aka haifi jaririn ba. A wurinsu ana yin aski ne a lokacin da ake da sha’awar yin sa ko kuwa a lokacin da suma ta yi yawa, kuma ba dole ne a yi askin ƙwaryar molo ba kamar yadda al’ummar Hausawa suke yi (MGAA, 30/9/2004).

Irin wannan al’ada ta Yarabawa ta yi naso a kan wasu Hausawa waɗanda suke zaune a ƙasashen Yarabawa, don kuwa a wannan zamani akwai wasu Hausawa waɗanda suke zaune a jihohin Lagos da Oyo da Ondo da Ekiti da Oshun da Ogun waɗanda ba sa yi wa jariran da aka haifa masu askin suna.

A maimakon haka, sai dai su sanya almakashi su daddatse sumar a lokacin da ta yi tsawo (YASASHL, 6/2//2006 da UƊSA da MBT da MAHD da MAA da MAMI da HZHO da MAS da MAIA da HR, 7 da 8 da 9 /10/2006) .

Magungunan da Wanzamai Suka Samu Daga Yarabawa

Wanzamai sun sami magunguna wurin Yarabawa. Daga cikinsu akwai na maganin ciwon ela. Ciwon ela yana kama yara ƙanana ne da jarirai waɗanda ba a yaye ba. Yanayin wannan ciwon shi ne, za a ga tsakanin cinyoyin yara sun sale sun yi jawur.

Idan kuma mace ce har cikin farjinta da gefensa duk sai ya sale ya yi jawur. Wurin da ciwon yake zai ta yi wa yaran ciwo da ƙaiƙayi wanda yake tilastawa yaran su soshe wurin, a wasu lokuta a lokacin da yaran suke susar wurin sai ya riƙa fitar da jini.

Maganin ela wanda Hausawa suka samu daga wurin Yarabawa shi ne, sai a sami sabulun salo a riƙa wanke wurin da ciwon yake, daga nan sai a sami attarugu ƙwaya ɗaya a wanke bakin yaron da yake da matsalar. Bayan nan kuma sai a sami sauyoyin bini-da-zugu da ganyensa a dafa su da ruwa, idan ya huce sai a sanya yaron a cikin ruwan ya ɗauki wani lokaci a ciki.

A lokacin da aka fito da yaron daga cikin ruwan, sai a sami ƙyalle mai kyau a shafe ruwan da yake wurin ciwon, daga nan sai a sami man ja a riƙa shafawa a wurin. Za a yi ta yin haka kullum har lokacin da yaron ya warke (YASASHL, 6/2/2006).

Karanta Shigowar Yarabawa Ƙasar Hausa

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAddu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa
Labarin na GabaTarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.