Ko da yake masana da manazarta da ɗaliban al’adun Hausawa sun bayyana ma’anar magani da waɗanda ke bayar da shi a ƙasar Hausa, yana da matuƙar muhimmanci a sani, wanzamai suna daga cikin waɗanda ke bayar da shi ga waɗanda suke buƙata (Bunza, 1990:132-134).
Bayar da magani a wurin wanzamai al’amari ne wanda suka gada daga wurin iyaye da kakanni, kuma sai wanda ya zauna wurin mahaifinsa ko wanda ya koya masa wannan sana’a ne yake sanin ire-iren itatuwan da ake harhaɗawa don yin magani. Akwai hanyoyi da dama waɗanda wanzamai suke bi don gane cututtuka da kuma bayar da maganin kowace irin cuta.
Hanyoyin da Wanzamai Suke Gane Cututtuka
Wanzamai suna bin hanyoyi da dama wajen gane irin cutar da ke damun mutum. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da duba wurin da cuta take, wato idan aka duba wurin da ciwo yake za a iya fahimtar irin cutar, misali, belun-wuya da cututtukan cikin farji da sauransu.
Wasu cututtukan kuma ana gane su ta hanyar taɓa wurin da cutar take, misali, ciwon ɓalli-ɓalli da ciwon saifa da sauransu. Haka kuma wanzamai suna gane irin cutar da ke damun mutum ta hanyar bayanin wanda yake da cutar ko wanda yake tare da shi kamar jarirai da yara ƙanana waɗanda ba su iya bayanin abin da ke damun su. Ire-iren waɗannan cututtuka sun haɗa da ciwon zuciya da ciwon sanyin jiki da sauransu.
Ire-Iren Magungunan da Wanzamai Suke Bayarwa
Wanzamai suna ba da magunguna iri daban-daban ga jarirai da yara ƙanana don maganin cututtuka irin su ciwon sanyin jiki da saifa da ciwon kai da ciwon ƙazamin goyo da ciwon damsai da ciwon tamalmala da ciwon cibiya. Haka kuma wanzamai na ba mata masu ciki magunguna don renon ciki da kuma waɗanda suka haihu don tanadin abin da aka haifa.
Bayan waɗannan wanzamai suna ba maza da mata magungunan cututtuka iri daban-daban waɗanda suka haɗa da maganin ciwon zuciya da maganin ciwon haƙori da maganin ciwon kunne da maganin amosanin ƙashi da maganin amosanin ciki da maganin amodari da maganin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar saduwa tsakanin maza da mata da maganin ƙarin ƙarfin azzakari da dai sauransu.
Wannan babi an duba irin yadda aka gudanar da sana’ar wanzanci a jiya dangane da yadda ake yin aski da gyaran fuska da cire belun-wuya da kaciya da ƙaho da wasu ayyuka da ake yi a farjin mata da tsaga wadda ta haɗa da ta gado da ta kwalliya da ta magani da kuma magungunan gargajiya waɗanda wanzamai suke bayarwa.
Don karanta Yadda Wanzamai Suke Tsaga danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu