Wannan babi ya duba sana’ar wanzanci a jiya wato yadda aka gudanar da wannan sana’a kafin al’ummar Hausawa su sami shigar al’adun wasu baƙi cikin al’adunsu. A nan an yi bayani a kan matsayin sana’ar wanzanci a al’adar Hausawa da kayan aikin wanzanci da kuma yadda ake gudanar da ayyukan wanzanci waɗanda suka haɗa da aski da gyaran fuska da cire belun-wuya da na mata da kaciya da tsaga da bayar da magungunan gargajiya.
Matsayin Sana’ar Wanzanci a Al’adar Hausawa
Kowane irin al’amari wanda ya danganci yadda ɗan Adam yake tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum yana da irin nasa matsayi a idanun masu yin sa da waɗanda ake yi wa. Wannan ne ya sa aka ga ya dace a duba matsayin sana’ar wanzanci a al’adance da irin yadda al’ummar Hausawa suke kallon wannan sana’a da masu yin ta.
Sana’ar wanzanci tana da babban matsayi a al’adar Hausawa, wannan kuwa ya faru ne saboda ire-iren muhimman ayyukan da wanzamai suke aiwatarwa. Haka kuma al’ummar Hausawa suna girmama wanzamai, wannan ne ya sa Alhaji Sale Gambara a cikin bakandamiyarsa yake cewa, a duk gari akwai manya uku waɗanda su ne kamar haka; shugaban da yake jagorancin mutanen garin, sai limamin garin daga nan sai wanzamin garin.
Haka kuma a fannonin adabin Hausawa akwai wurare da dama waɗanda aka bayyana muhimmancin wannan sana’a. Misali, a cikin littafin da Alhaji Nuhu Bamalli ya rubuta mai sunan “Mungo Park Mabuɗin Kwara”, wanda aka yi bayani a kan tafiye-tafiyen Mungo Park a sassan Afrika ta Yamma a shafi na 42-43 an yi bayyanin inda wannan matafiyi ya bayyana ya zama wanzami.
Haka su ma makaɗan ƙasar Hausa suna bayyana muhimmancin wanzami a idon Hausawa. A iya ganin haka a waƙar da Ɗan’anace ya yi wa Shago inda yake cewa:
“Ɗan Abdu Gazaguru,
Ai na faɗa maka goga,
Wanga kashi da kay yi ba dawa ne ba,
Kar ka kashe Na’ila wanzami na,
Ai shi ka yo muna gyara,…”
Kuma kasancewar wanzaman gargajiya masana tsubbace-tsubbace da sihirce-sihirce ne masu ban mamaki da al’ajabi da ban tsoro ya sa al’ummar Hausawa suke ɗaukar su kamar wasu dodanni ko wasu mutane da ake tsoro. Wannan ne ma ya sa ba a yi wa wanzamai gardama ko gatse ko shisshigi dangane da yadda suke aiwatar da ayyukansu, don tsoron kar su yi wa mutum wani abu da zai cuce shi.
Haka kuma al’ummar Hausawa sun ɗauki wanzamai a matsayin wasu mutane masu bayar da taimako idan wata lalura ta rashin lafiya ko bukatar maganin gargajiya ta taso. A nan ma makaɗan Hausawa sun bayyana irin rawar da wanzamai suke takawa wajen yin ire-iren waɗannan tsatsube-tsatsube.
Misali, a waƙar da Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa Ciroman Aski na Jalingo ya bayyana irin yadda wanzamai suke harbin ‘yan uwansu a lokacin da suka zo yin aski sai su riƙa yin kyarmar hannu wadda take yin dalilin a riƙa yankar wanda ake yi wa aski. Ga irin yadda ya bayyana haka cikin wannan waƙa:
“Ga wani ya zo aski,
Sun harbai hannu nai na karkarwa,
Da ya zo gun aski,
Sai na ga jini na ta zubowa…”
Haka kuma karin maganar Hausawa ya ƙara fito da matsayin wanzami a idon Hausawa kamar haka:
Kowa ya ci ladar kuturu, dole ya yi masa aski.
Kushekarar jaki sai wanzamin kura.
Wanzami ba ya son jarfa.
Waɗannan dalilai ne suka sa al’ummar Hausawa suke matuƙar kyautata wa wanzamai da dukkan abin da ya dace na kyautatawa, kuma kowane mutum ya yarda da dukkan ayyukan wanzanci, ana yi masa da dukkan iyalinsa. Idan bukatar aikin wanzami ta kama matuƙar bai zo lokacin da ake buƘatar ya zo ba, ana tarar da shi har gidansa don a gani ko lafiya? Wannan dalili ya sa yin ayyukan wanzanci a wurin Hausawa a jiya wani al’amari ne wanda ya zama dole a yi shi.
Kayan Aikin Yin Wanzanci
Wanzamai suna amfani da kayayyaki iri daban-daban domin yin ayyukan wanzanci. Ire-iren waɗannan kayayyaki sun haɗa da askar aski da kwanon aski da kalaba da ƙoshiya da ‘yaR tsaga da hantsaki da tankolo da zabira da ƙaho da kura ta cire haƙori da sauransu.
Askar Aski
Askar da ake amfani ita wajen yin aski ƙarama ce madaidaiciya kuma ba ta da tsawo sosai. Akwai bambanci tsakanin wadda ake askin jarirai da wadda ake yi wa manya aski.Ta askin jarirai ba ta kai girman wadda ake yi wa manya aski ba. Da kuma askar aski ake amfani wajen yin kaciya, ana amfani ne da irin wadda ake yi wa manya aski wato mai kaifi da nauyi wajen yin kaciya. Kafin zuwan wannan zamani ana amfani da askar baƙin ƙarfe wajen yin aski da kaciya, irin wannan aska ita wanzamai suka gaji amfani da ita, kuma maƙeran Hausawa ne suke samar ta ita ga wanzamai.
Wani muhimmin abu da ya kamata a sani a nan shi ne, askar baƙin ƙarfe ta fi kowace irin aska riƙe kaifi. Idan wanzami ya wasa askar baƙin ƙarfe sai ya yi wa mutane da yawa aski ko gyaran fuska ba tare da ya sake wasa ta ba. Akwai maƙera na daban waƙanda suke ƙerawa da kuɗar asaken aski.
Dutsin Washin Asaken Aski
Dutsin washin asaken aski dutsi ne ƙarami mai sulɓi da ake amfani da shi domin yin washin asaken aski idan kaifinsu ya dakushe, wato idan kaifinsu ya ragu. Idan kuwa kaifinsu ya dakushe duka, to sai a kai ga maƙeri domin a sake koɗa su. Ana amfani da dutse ta hanyar goga askar bisa dutsen sannu a hankali har sai an tabbata askar ta wasu.
Hanyar da ake gane aska ta wasu ita ce, sai a ɗan fera fatar hannu, idan askar ta fere fatar sosai aska ta wasu ke nan. Kafin zuwan wannan zamani duwatsu iri biyu da ake amfani da su wajen wasa asaken aski. Na farko shi ne na gatarin aradu, watan dutsen da yake faɗowa idan an yi tsawa lokacin ruwan damina.
Hanyar da ake bi domin samun dutsen gatarin aradu ita ce, da zarar an yi tsawa, aka kuma yi dacen ganin wurin da ta faɗi, sai a yi gaggawa a je a zuba madara ko nonon shanu a wurin da tsawar ta faɗi. Idan an tona sai a tarar da dutsin da ya faɗo, don kuwa madara ko nonon da aka zuba zai hana shi yin ƙasa da nisa. Dutsi iri na biyu da ake amfani da shi domin washin asaken aski shi ne na ƙanƙara mai sulɓi da ake samu a kogi ko wurin da yake da duwatsu.
Fatar Washin Asaken Aski
Fatar wasa asaken aski fatar dabbobi ce ake samu daga wajen dukawa wadda aka jeme. Ana amfani da mai faɗin misali inci ɗaya da rabi, tsawonta kuma misalin inci goma sha biyar zuwa ashirin. An fi amfani da mai kauri irin ta manyan dabbobi domin kuwa ta fi inganci da ƙara wa aska kaifi.
Amfanin fatar washin asaken aski shi ne, idan aka wasa askar da dutsi kaifinta ba zai kai sosai ba, sai an wasa da fata. A nan ne sai a shafa ruwa ga fatar a bi da askar ana shafawa bisa fatar sannu a hankali. Wannan ne zai daidaita kaifin askar yadda idan an zo yin aski askar za ta tuje gashin da sauƙi. Mafi yanwancin wanzamai suna ɗaura fatar wasa asaken askin wurin zabira daga gefe.
Kwanon Aski
Kwanon aski ana amfani da shi ne domin zuba ruwan da za a riƙa amfani da shi wajen yin aski da gyaran fuska da kaciya da tsaga. A da can kafin zuwan Turawa wanzamai suna amfani da ƙoƙo domin zuba ruwan aski. Wannan ne ma ya sa ake kiran wanzaman da suke yin aski da gyaran fuska da sunan ‘wanzaman ƙoƙo’. A halin yanzu ana amfani da kofin roba ko na ƙarfe domin zuba ruwan aski
Kalaba
Kalaba ƙarfe ne ƙarami wanda tsawonsa misalin inci shida zuwa bakwai, kuma ba shi da kauri sosai. Maƙera ne suke ƙera kalaba, ba kuma dukkan maƙeri ne yake ƙirar kalaba ba, akwai maƙera na daban masu ƙera ta. Ana yin ta ne da kaifi a gefe ɗaya na kanta sai a lanƘwasa kan ya zamo kaifi ciki. Ana yi wa gindinta kauri domin a ji daɗin riƙewa idan za a yi aiki da ita. Amfanin kalaba wajen ayyukan wanzanci shi ne a riƙa cire belin- wuya da ita.
Ƙoshiya
Ƙoshiya itace ne ƙarami ake sassaƙawa da ɗan faɗi ga kai da kuma kauri ga gindi. Tsawon ƙoshiya misali inci shida ne zuwa bakwai, faɗin kanta kuma bai kai inci ɗaya ba. A taƙaice tsawon ƙoshiya ɗaya yake da na kalaba. Ana amfani da ƙoshiya wajen wanzanci domin taushe harshen jariri a lokacin da za a cire belun-wuya. Ita ƙoshiya masassaƙa ne suke samar da ita ga wanzamai, akwai kuma wasu wanzamai da suke iya sassaƙa ƙoshiya.
‘Yar Tsaga
‘Yartsaga aska ce ƙarama da maƙera suke ƙerawa, tsawonta ya kai misalin inci huɗu zuwa biyar, kanta kuma ana yin sa da faɗi da tsini da kaifi. Ana amfani da ‘yartsaga wajen ayyukan wanzanci domin yin wasu ayyukan da wanzamai suke yi a farjin mata kamar cire angurya da yanke linzami da cire haƙoran shuwa.Ana kuma amfani da ita domin yin tsagar gado da ta magani da kuma ta kwalliya.
Hantsaki
Hantsaki ƙarfe ne da maƙera suke ƙerawa da baki a gindi da kuma tsini a kai. Ba shi da kauri sosai, kuma tsawon sa misalin inci huɗu ne. Ana amfani da hantsaki wajen wanzanci domin cire angurya a farjin mata.
Ƙaho
Wanzamai suna amfani da ƙahon sa ne domin yin ƙaho. Ana amfani da ƙaho madaidaici wanda ba babba ba ƙwarai, ba kuma ƙarami ba, ana yanka misalin tsawon inci biyar ko shida. Ana yi wa wajen tsininsa ‘yar ƙaramar ƙofa. Ana amfani da ƙaho ne domin yin ƙaho. Mahauta ne suke samar da ƙaho ga wanzamai, su ne suke fitar da shi daga kan sa da aka yanka sai su sayar wa wanzaman da suke yin ƙaho.
Jijiya
Wanzamai suna amfani da jijiyar agarar ƙafar akuya ko tunkiya domin a riƙa liƙe ƙofar tsinin ƙahon da aka kafa wa mutum domin ya liƙe a wurin da aka kafa shi a jikin mutum. Wanzamin zai sanya wannan jijiya a cikin bakinsa yana taunawa sai ya liƙa ta a wurin ƙofar, da an liƙa shi ke nan sai ƙahon ya liƙe a wurin da aka kafa shi, ba zai fita ba sai in an cire wannan jijiya. Ita ma jijiya mahauta ne suke samar da ita ga wanzamai.
Kura ta Cire Haƙori
Ita kura ƙarfe ne ake samu domin cire haƙori, yanayinta ya yi kama da abin da kafintoci suke cire ƙusa a wannan zamani, amma ita kura ba ta kai girman abin cire ƙusa ba. Wanzamai suna amfani da kura ne domin cire haƙori. Wanzami yana amfani da kura ne ya kama haƙori mai ciwo ko mai girgiɗa sai ya cire shi daga wurin da yake.
Tankolo
Tankolo ‘yar jaka ce wadda dukawa suke ɗinkawa da fatar akuya ko tinkiya domin wanzamai su riƙa sanya askar aski ɗaya ko kuma babba wadda za a sanya asaken aski masu yawa.
Zabira
Zabira jaka ce babba mai aljihuna da yawa misali uku ko huɗu. Ana yi mata maratayi domin a riƙa ratayawa. Ita ma dukawa ne suke ɗinka ta da fatar akuya ko tinkiya domin yi wa wanzamai jakar da za su riƙa sanya dukkan kayan aikin wanzanci waɗanda aka yi bayaninsu a baya.
Don karanta Matsayin Hausawa A Yau danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu