Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya

0
24

Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa adabin kasuwa ko na yayi yana tafiya ne kafaɗa da kafaɗa da gangariyar adabin al’umma. Shi gangariyar adabin yana kasancewa ne tsakanin masu ilmi ko hannu da shuni ko kuma iyayen ƙasa. Duk wani abu da ba na wannan gungun mutane ba ne, yawanci shi ake wa laƙabi da adabin kasuwa ko yayi.

Alal misali kusan duk yawancin ayyukan adabi da suke da wannan siffa a Turai ko Amurka ko sauran sassan duniya an samar da su ne tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18, daidai lokacin da fasahar ɗab’i ko buga littattafai ta yi tashe a duniya.

Kamar yadda bayanai suka yi nuni, yawancin jama’a da masana idan ana maganar adabin ƙarni na 16 da 17 da na 18, ana maganar gangariyar adabi ne ko na masu ilmi ko mulki ko dukiya, amma ba su kaɗai ne suka kwashi nasu kason ba daga rayuwar adabi, akwai adabin talakawa ko na kasuwa, wato na kowa da kowa, adabin da aljihun talaka zai iya biya, ya saya don karantawa.

Wannan dama ta samu ne domin an samar da injinun buga littattafai na bakin hanya da suka ba talaka damar ya sami gurbin da zai buga nasa adabin. Ire-iren waɗannan ayyukan adabin su ne ake ba sunaye daban-daban da suka haɗa da Grub Street Literature ko Chapbooks. Waɗannan laƙabobi sun wanzu ne saboda la’akari da irin yadda aka samar da adabin ko wuraren da ake samar da littattafan ko kuma yanayin bugawa da sayar da su.

Su dai Grub Street Literature su ne ayyukan adabin da aka samar daga wuraren buga littattafai da ke kan Titin Grub a Landon. Da yake a tsakanin ƙarni na 16 da 17 da na 18 an samar da marubuta na ƙwarai, sai dai rubutun nasu ya fi mayar da hankali ne ga masu-faɗa-a-ji, bai ta’allaƙa ga sauran jama’a ba, ga shi kuma sun fi sauran jama’ar yawa, wannan ya sa aka shiga neman wasu da za su agaza da nasu rubutun.

Sai dai yawancin irin waɗannan marubuta ba su da sanayya ta zamani game da fasahar rubutu da ƙaga labarai, shi ya sa idan sun yi rubutu ake biyan su kuɗaɗe kaɗan, wannan ya sa suke rayuwa a cikin talauci da ƙunci.

Shi kansa inda suke zama a bakin titin domin yin aikin nasu na adabi, wuri ne na ƙazanta da yawan lalata da tashin hankali; nan ake samun ɓarayi da mabarata da dai ire-irensu; nan ne marubutan da injinan buga ayyukansu suka ɗaura aure.

Su kuwa Chapbooks littattafai ne da ake wa laƙabin littattafai masu arha, su ne ayyukan adabin da suka kasance na yayi ko na jama’a a karo na farko a wancan zamani na ƙarni na 17 da 18.

Ba ruwansu da kamfanonin hukuma ko na gwamnati, ba kuma ruwansu da manyan kamfanonin ɗab’i da ke neman ƙazamar riba. Ana kuma shirya da buga irin waɗannan littattafai domin isar da saƙo ga talakawa ko masu sha’awar adabi, amma ba su da kuɗin sayen gangariyar adabin da ke wanzuwa a lokacin.

Wannan damar ce marubutan da masu karatu ke amfani da ita domin su isar da saƙo ga sauran jama’a ba tare da kamfanin ɗab’i ya sa baki ba, yawancin abubuwan da ake samarwa sun haɗa da waƙe-waƙe da labarai da ayyukan addini da saƙonnin siyasa da makamantansu.

Tarihi ya nuna cewa ko da hada-hadar ɗab’i da rubuce-rubuce ta kankama daga ƙarni na 15 da na 16 akwai ire-iren waɗannan ayyuka masu arha, yawancinsu sun fita kasuwa ne daga ƙarni na 17 da na 18 a Ingila, an nuna sun kai ƙoƙoluwa ne a shekarar 1775 ta yadda ake samar da littattafai sama da 200,000 a kowace shekara.

Waɗannan littattafai sun taimaka wajen raya ayyukan adabin Ingila a wancan lokaci, sun sanya son karatu ga waɗanda ba su yi nisa a karatun ba, ko suka yi karatun suka watsar daga baya.

Yawancin waɗannan littattafai ba su da yawan shafi, ba a yi musu bugun ƙwarai, sa’annan ana sayar da su da arha, daga wannan titi zuwa wancan, a maimamkon wuraren da aka tanada domin sayar da gangariyar adabi. Domin ganin yadda wannan fasali ya kasance, bari mu dubi yadda na zamanin Elizabeth ya kasance a Ingila.

Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

Don karanta Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa danna nan 

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa
Labarin na GabaAdabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.