Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 11/7/25

0
14

Aminu Bashir

Mai huɗuba: Sheikh Dr. Bandar bin Abdul-Aziz Badila

Mai fassara: Dr. Usman Azzuhree

Huɗuba ta farko:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mai jin ƙai, Mai rahama, Mai karamci, Mai yawan baiwa. Ina yaba Masa tsarki ya tabbata a gare Shi kuma ina gode Masa, Mai yawan afuwa, Mai yalwar yafiya.

Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya; tausayinSa ya game dukkan halittu, kuma rahamarSa ta yalwaci mutane da aljanu. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, Ubangijinsa ya aiko shi a gabanin Ƙiyama da gaskiya da ma’auni, da afuwa da kyautatawa, tsira da aminci da albarkar Allah su ƙara tabbata a gare shi, da alayensa da Sahabbansa ma’abota tuba da komawa ga Allah.

Bayan haka:

Ya ku mutane! Ina yi muku wasici, da ni kaina da tsoron Allah, ku ji tsoron Allah, Allah Ya jiƙan ku, kuma kada ku ɗebe tsammanin samun rahamar Allah, kuma kada ku yanke ƙaunar samun jinƙai daga Allah: (Saboda lallai Allah Maɗaukaki yana shimfiɗa hannunSa da dare domin wanda ya yi laifi da rana ya tuba, kuma yana shimfiɗa hannunSa da yini domin wanda ya yi laifi da dare ya tuba, har sai rana ta fito daga mafaɗarta).

Muslim ne ya ruwaito.

Ya ku bayin Allah! Lallai Allah Maɗaukaki ya sanya ɗabi’u na sha’awa da karkata zuwa ga ababen so a cikin zukatan ‘ya’yan Adam, wanda hakan ya sa suka zama tushen umurni da hane-hane da aka ɗaura musu, kuma ya rubuta musu rabonsu daga saɓo domin gwaji da jarrabawa: ((Domin Allah ya san wanda ke tsoronSa a bayan ido)).

Suratul Ma’ida (94).

An ruwaito daga Anas ɗan Malik Allah Ya ƙara masa yarda, ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Dukkan ɗan Adam mai kuskure ne, kuma mafi alheri cikin masu kuskure su ne masu tuba). Imam Ahmad ne ya rawaito a Musnad.

Manufar hakan kuwa ita ce; masu tuba su koma gare Shi, kuma masu komawa su fuskance Shi, kuma masu tsoron Sa su rusuna a gabanSa, an rawaito daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda, ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa, da ba ku yi zunubi ba, da Allah ya kawar da ku, ya kawo wasu mutane waɗanda za su yi zunubi, sannan su nemi gafara daga Allah, kuma Allah Ya gafarta musu).

Muslim ne ya ruwaito.

Kuma lallai daga cikin manyan siffofin Allah Maɗaukaki akwai siffar rahama, Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Rahamata ta yalwaci komai)). Suratul A‘rāfi (156).

Kuma lallai daga cikin mafi girman sunayenSa akwai Ar-Rahmān da Ar-Rahīm, wato Mai rahama Mai jinƙai, kamar yadda Ya ce: ((Kuma abin bautarku abin bauta ne guda, babu abin bautawa bisa cancanta sai Shi, Mai rahama Mai jinƙai)). Suratul Baƙara (163).

Kuma Ya kwaɗaitar da bayinSa da su kasance masu jin ƙai ga halittu. An ruwaito daga Usāma ɗan Zaid Allah Ya ƙara masa yarda, cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Lallai waɗanda Allah Yake tausayin su cikin bayinSa su ne masu tausayi). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Kuma an rawaito daga Abdullah ɗan Amr Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Allah Mai rahama yana jinƙan masu jinƙai, ku ji ƙan waɗanda ke bayan ƙasa, Wanda yake sama Zai jiƙan ku). Ahmad ne ya rawaito a Musnad ɗinsa.

Kuma daga cikin rahamarSa tsarki ya tabbaya a gare Shi ga bayinSa akwai saukar musu da littattafai da Ya yi, kuma Ya aiko musu Manzanni, kuma bai gaggauto musu da uƙuba ba, ((Idan da Allah Yana (saurin) damƙar mutane saboda laifin da suka aikata, to, da bai bar kowane mai rai ba a bayan ƙasa, sai dai kuma Yana saurara musu ne zuwa wani lokaci ƙayyadajje)). Suratu Faɗir (45).

Kuma Ya kwaɗaitar da su zuwa ga tuba, kuma ya kira su zuwa ga dawowa gare Shi, sai Ya ce: ((Ka ce: Ya ku bayiNa waɗanda suka lalata kawunansu (da kafirci da saɓon Allah), kada ku ɗabe ƙauna daga rahamar Allah. Lallai Allah Yana gafarta dukkan zunubai. Lallai Shi Mai gafara ne, Mai jin ƙai)). Suratuz Zumar (53).

Sannan Allah tsarki ya tabbata a gare Shi Ya yi musu alkawarin gafarar zunubai da kuma kankare munanan laifuka, sai Ya ce: ((Kuma waɗanda idan suka aikata alfasha ko suka zalunci kawunansu, nan take sai su tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Kuma wa ya ke gafarta zunubai in ba Allah ba? Kuma ba sa dogewa a kan abin da suka aikata alhali suna sane)). Suratu Ali Imran (135).

Kuma Allah tsarki ya tabbata gare Shi Ya lamunce wa duk wanda ya tuba kuma ya koma gare Shi cewa zai mayar da miyagun ayyukansa su zama kyawawa kamar yadda Ya ce: ((Sai dai wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki nagari, to, waɗannan ne Allah zai mayar da munanan ayyukansu su zama kyawawa. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai)). Suratul Furƙan (70).

Kuma Ya umarci AnnabinSa da ya tausaya wa mutane, ya ji ƙansu, kuma ya karɓa daga gare su, sai Ya ce da shi: ((To, Saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zama mai tausayawa a gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai ƙeƙasasshiyar zuciya ne, to, da sun watse sun barka. Saboda haka, ka yi musu afuwa, kuma ka roƙa musu gafara, kuma ka shawarce su cikin dukkan lamura; amma idan ka riga ka ƙulla niyya, to, ka dogara ga Allah. Lallai Allah yana son masu dogaro a gare Shi)). Suratu Ali Imran (159).

Bari dai, Tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana isa har zuwa ga waɗanda suka yi masa adawa daga cikin mushirikai, saboda girman abin da ke jiran su a Ranar Alƙiyama, yana fatan su shigo Musulunci, don tsoron kada su mutu a kan shirka, sai su cancanci azabar wuta, Allah Mai ɗaukaka da buwaya Ya ce yana Mai bayyana hakan a wurare da dama cikin littafinsa: ((To ko mai yiwuwa ne za ka kashe kanka da baƙin ciki, in ba su yi imani da wannan zancen ba (watai Alƙur’ani)). Suratul Kahfi (6).

Kuma ya ce: ((Ko za ka kashe kanka ne don ba su zama muminai ba?)). Suratush-Shu’ara’ (3). Kuma ya ce: ((Kada ka kashe kanka saboda bakin ciki a kansu. Lallai Allah Masani ne ga abin da suke aikatawa)). Suratul Faɗir (8). Malaman tafsiri suka ce: Ma’ana: Kana shirin halakar da kanka saboda baƙin ciki a kansu.

To, ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah, ku kasance masu tausayi ga bayin Allah, kuma ku kyautata musu, ku tausasa musu, ku yi koyi da halin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, an rawaito daga Abū Huraira Allah Ya ƙara masa yarda cewa: lallai wani baƙauye ya yi fitsari a cikin Masallaci, sai mutane suka tashi don su afka masa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da su: (Ku bar shi, ku zuba guga na ruwa ko bokiti na ruwa a in da ya yi fitsarin, domin an aiko ku ne masu sauƙaƙawa, ba masu tsanantawa ba). Bukhari ne ya ruwaito.

Kuma an rawaito daga Abu Musa Allah Ya ƙara masa yarda, ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan zai aika wani daga cikin Sahabbansa zuwa ga wani lamarinsa, sai ya ce: (Ku yi bishara, kada ku yi kora; ku sauƙaƙa, kada ku tsananta). Muslim ne ya rawaito.

Ku yi hattara sosai! Kada mumini ya zama katanga a kan tafarkin Allah, ko mai koran mutane daga addinin Allah, ko shinge da ke hana mutane samun kusanci da Allah, alhali bai sani ba, domin zukata suna hannun Allah tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Shi ne Yake sanin abin da ke cikinsu na imani, da yaƙini, da gaskiya, da ƙauna ko ya ya kuwa bawa ya dulmiya cikin zunubai, kuma ko ma waɗanne irin munanan laifuka ya aikata.

Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina nema wa kaina gafarar Allah, da ku da dukkan Musulmi daga kowane zunubi, don haka, ku nemi gafararSa, domin Shi Mai gafara ne, kuma Mai jin ƙai.

Huɗuba ta biyu:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Yana karɓar tuba daga bayinSa, kuma Yana yin afuwa ga laifuka masu yawa. Ina yaba Masa, tsarki ya tabbata gare Shi, kuma ina gode masa, Yana yafe tuntuɓe, kuma Yana suturce aibuka, kuma Yana ƙarfafa masu rauni.

Ina shaidawa lallai babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, idan aka yi aiki kaɗan Yana ba da sakamako mai yawa. Kuma Ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, mai bishara, da kuma gargaɗi, kuma fitila mai haskakawa, tsira da aminci da albarkar Allah su ƙara tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa masu rangwame da kuma sauƙaƙawa.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah!

Kishi a kan addini, da yin fushi idan aka taɓa Shari’ar Allah, na iya jawo wasu jama’a daga cikin Musulmi ko wasu gungun Muminai, idan sun ga ana aikata mummunan aiki, ko suka samu ana aikata saɓo, su wuce gona da iri wajen yin hani da kuma ƙetare iyaka wajen inkari, wataƙila ma har wasu daga cikinsu Allah Ya kiyaye mu su shiga cikin abin da yake haƙƙin Allah Mahalicci ne, kuma abubuwan da Ubangiji kaɗai Ya keɓanta da su.

Wannan kuma, ina rantsuwa da Allah babban kuskure ne, kuma tuntuɓe ne mai haɗari.

An rawaito daga Damdamu ɗan Jaus al-Yamami ya ce: Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda ya ce da ni: “Ya kai Yamami, kada ka ce wa wani mutum: ‘Wallahi, Allah ba zai gafarta maka ba’ ko kuma ‘Allah ba zai shigar da kai Aljanna ba har abada”. Na ce: “Ya Abu Huraira, wannan magana ce da ɗaya daga cikinmu yake faɗa wa abokinsa idan ya fusata”.

Sai ya ce: “Kada ka faɗa”. Domin na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (A cikin Banu Isra’ila akwai wasu mutane biyu, ɗaya daga cikinsu ya kasance mai ƙoƙari wurin ibada, ɗayan kuwa mai yawan zunubi ne, kuma sun kasance abokan juna.

Mai ibadar yana yawan ganin ɗayan cikin aikata zunubi, sai ya ce masa: “Kai wane, ka daina”. Sai shi kuma ya ce masa: “Ka bar ni ni da Ubangijina, shin an aiko ka ne don ka sa ido a kaina?” Ya ce: Har wata rana ya gan shi a cikin wani zunubi, sai ya ga girman hakan, sai ya ce masa: “Kaitonka! Ka daina”. Sai ya ce: “Ka bar ni ni da Ubangijina, shin an aiko ne don ka sa ido a kaina?”. Sai mai ibadar ya ce masa: “Wallahi, Allah ba zai gafarta maka ba”, ko “ba zai shigar da kai Aljanna ba har abada”.

Ya ce: Sai Allah Ya aiko da mala’ika zuwa gare su, sai ya karɓi rayukansu, suka haɗu a wurinSa, sai Ya ce wa mai aikata laifin: Je ka shiga Aljanna da rahamaTa. Sai ya ce wa ɗayan: Shin ka san abin da ke cikin ilimiNa ne? Shin kana da wani iko a kan abin da ke hannuNa ne? Ku tafi da shi zuwa wuta. Ya ce: Na rantse da wanda rayuwar Baban Ƙasim ke hannunSa, lallai ya furta kalmar da ta hallaka masa duniyarsa da lahirarsa”. Imam Ahmad ne ya rawaito a cikin Musnad da Abu Dawud a cikin Sunan.

Kuma ku sani, ya ku bayin Allah cewa: Lallai ƙin saɓo da kuma inkarin mummunan aiki, ba sa cin karo da tausasa wa wanda ya aikita laifi, ko kuma tausayi ga mai aikata saɓo, bari dai, haɗuwar duka biyun dalili ne na cikar imani, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a kai.

Sannan ku yi salati da salama ga mafi alherin halittun Allah, Muhammadu ɗan Abdullahi, kamar yadda Ubangijinku ya umarce ku, sai Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku yi salati a gare shi da salama mai yawa)).

Ya Allah! Ka yi daɗin tsira da aminci da albarka ga bawanKa kuma ManzonKa, Annabinmu Muhammadu.

Kuma ya Allah Ka ƙara yarda da Halifofinsa guda huɗu, jagorori kuma tsayayyu a kan addini: Abubakar da Umar da Usmanu da Ali, Ka kuma ƙara yarda da sauran sahabbai goma da aka musu albishir da Aljanna, da waɗanda suka yi mubaya’a a ƙarƙashin bishiya, da sauran Sahabbai gabaɗaya, da Tabi’ai, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Ya Allah! Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi. Ka kare shingen addini. Ka taimaki bayinKa masu tauhidi, ya Ubangijin halittu. Ya Allah! Ka yaye damuwar masu damuwa daga cikin Musulmi, kuma Ka sauƙaƙa wa waɗanda ke cikin ƙunci, kuma Ka biya bashin waɗanda ake bi bashi, Ka warkar da marasa lafiyar mu da na sauran Musulmi gabaɗaya.

Ya Allah! Ka amintar da mu a ƙasashenmu, Ka shiryar da shugabanninmu da majiɓinta lamuranmu, kuma Ka karfafi Shugabanmu kuma majiɓincin lamurammu, Hadimin Masallatai biyu masu alfarma, da gaskiya, da dace, da aikata daidai.

Ya Allah! Ka tsawaita rayuwarsa cikin lafiya da kwanciyar hankali, da ni’ima mai yalwa, kuma Ka datar da shi da magajinsa amintacce zuwa ga abin da ke da amfani ga ƙasa da bayinKa, da ɗaukaka ga Musulunci da Musulmi, ya Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka kare sojojinmu, masu tsaron iyakokinmu da fagagenmu, Ya Allah Ka kiyaye su da idonKa da baya barci, Ka lulluɓe su da karfinka wanda ba a rinjayar sa, ya Ma’abocin girma da karamci.

Ya Allah! Ka kasance Mai taimako da ƙarfafawa da goyon baya ga ‘yan’uwanmu masu rauni, Ya Allah! Ka kasance tare da su a ƙasar Falasdinu da duk inda suke, Ka mayar da rauninsu ya zamo ƙarfi, tsoronsu ya koma aminci, talaucinsu ya zama yalwa da jin daɗi, ya Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka yi maganin Yahudawa ‘yan ƙwace ‘yan mamaya, Ka kare mu da sauran duniya daga sharrinsu, ya Mai ƙarfi. Ya Allah! Ka sanya mu daga cikin mafiya tausayin bayinKa ga halittunKa, kuma mafiya tausasawa da kyatatawa a gare su, ya Mai Rahama Mai jinƙai.

((Ya Ubangijinmu! Ka ba mu kyakkyawa a duniya, kyakkyawa a lahira, kuma Ka tsare mu daga azabar wuta)). ((Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke sifanta Shi da shi, aminci ya tabbata ga Manzanni, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai)).

Domin karanta Rubutacciyar Fassarar Idin Ƙarmara Sallah danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTarihin Dr. Yusuf Bala Usman
Labarin na GabaIlimin Ma’ana (Semantics)