Babahabu49
GABATARWA
Alaƙar da ke tsakanin Hausawa da Fulani dangantaka ce mai zurfi da ke da tarihi mai tsawo. Tsawon lokacin da aka shafe ana cuɗanya da mu’amala tsakanin waɗannan kabilu biyu ya sa har ana ɗaukar su a matsayin ƙabila ɗaya, wato HausaFulani.
Wannan dangantaka ta samo asali ne daga cuɗanya ta fuskar siyasa, addini, ilimi, kasuwanci da zamantakewa, lamarin da ya haifar da ƙarfafa haɗin kai da juna har ma da cakuduwar al’adu da harsuna. Wannan rubutu zai yi bayani kan asalinsu, yadda suka haɗu, irin mu’amalar da ke tsakaninsu, da kuma yadda harsunansu suka shafi juna.
TAƘAITACCEN TARIHIN CUƊANYAR HAUSAWA DA FULANI
Cuɗanyar da ke tsakanin Hausawa da Fulani na ɗaya daga cikin manyan dangantaka da suka daɗe a tarihin Arewacin Najeriya. Wannan hulɗa ta samo asali ne tun kafin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, inda Fulani ke shigowa yankunan Hausa domin kiwo da kasuwanci.
A farkon zuwansu, Fulani sun kasance makiyaya masu yawo (Fulani na jeji), suna kiwon shanu da cinikayya da Hausawa, musamman kan gishiri, nono, da kanwa. Wasu daga cikin Fulani sun zauna cikin garuruwa (Fulani na soro), suka rungumi ilimi da addini, har suka zama malamai da limamai a tsakanin Hausawa.
Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a ƙarni na 19 ya ƙarfafa cuɗanyar da ke tsakanin su, inda Fulani suka karɓi ragamar mulki a yawancin garuruwan Hausa, amma suka yi hakan ne cikin harshen Hausa da tsarin rayuwar Hausawa. Wannan ya janyo cakuɗuwar jini, harshe, da al’adu tsakanin ƙabilun biyu.
Hausawa da Fulani suka fara yin aure da juna, suka zauna tare a gari guda, suka fara cin moriyar juna ta fuskar ilimi, addini da siyasa. Wannan haɗin kai ya haifar da samuwar kalmar “Hausa-Fulani”, domin nuna cewa su ƙabilu ne guda biyu.
Asalin Fulani da Haɗuwarsu da Hausawa
A cewar Bunza (2008), asalin Fulani ya fara ne daga yammacin Afirka, musamman a yankin Senegal. A halin yanzu ana samun Fulani a ƙasashe da dama kamar Chadi, Kamaru, Gambiya, Sudan, da Habasha. Fulani sun riƙa yawo a ƙasashe daban-daban har suka iso ƙasar Hausa, kuma wannan hijira ba ta da cikakken tarihi da ke bayyana lokacin da suka fara hulɗa da Hausawa.
Wasu masana sun danganta Fulanin farko da Toronkawa – waɗanda ake ganin su ne tushen asalin Fulani. An ce sun zauna a dutsen Durisinin bayan fitowa daga yankin Sham, sannan suka ci gaba da sauka a ƙasashen Misira, suka nufi yammacin Afirka har suka iso ƙasar Hausa.
Muhimmiyar alama ta haɗin kai ita ce Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a ƙarni na goma sha takwas, wanda ya zama wata babbar hanya ta haɗin Fulani da Hausawa, musamman ta fuskar addini da shugabanci.
Cudanya da Mu’amala Tsakanin Hausawa da Fulani
Daga cikin manyan hanyoyin da suka ƙarfafa alaƙar Hausawa da Fulani akwai:
Kalmar “Hausa-Fulani” a siyasa da zamantakewa sakamakon haɗin rayuwa da juna, an fi amfani da kalmar Hausa-Fulani wajen bayyana haɗakar waɗannan ƙabilu, musamman a fagen:
Siyasa: Jam’iyyun siyasa da shugabanni sukan jingina da Hausa-Fulani.
Zamantakewa: Auren juna da haɗin kai ya haifar da cakuɗa ta na rayuwar yau da kullum. Misali: A lokacin mulkin Obasanjo, an riƙa cewa mataimakinsa Atiku Abubakar ya fito daga yankin Hausa-Fulani, duk da cewa shi Bafillace ne a cewar wasu.
1. Addini: Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya kawo sauyi wajen ƙarfafa Musulunci a ƙasar Hausa, tare da mayar da Hausawa da Fulani ƙarƙashin shugabanci guda na addini da siyasa.
2. Kasuwanci: Fulani, musamman makiyaya da masu noma, sun kasance cikin hulɗa da Hausawa a fannin ciniki. Fulani sun riƙa kawo madara, nono, da shanu, yayin da Hausawa ke samar da kaya kamar gishiri, ƙanwa, da kayan masarufi.
3. Zamantakewa: Ana samun Fulani a birane da dama a Arewacin Najeriya kamar Sakkwato, Gombe, Taraba, Adamawa, Yobe da sauransu. Wasu daga cikin Fulani suna rayuwa ne irin ta Hausawa, suna karatu da karantarwa. Misali, Malam Musa Jakallo, kakakin Shehu Ɗanfodiyo, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka taimaka wajen haɗin gwiwa da zamantakewa.
4. Sadarwa da kalmomi: Cuɗanyar Fulani da Hausawa ta sa ana samun cakuɗuwar kalmomi daga harshe zuwa harshe.
Tasirin Fulatanci a Harshen Hausa
Wani babban tasiri da dangantakar Fulani da Hausawa ta haifar shi ne cuɗanyar harsuna. Hausa ta aro kalmomi da dama daga Fulatanci musamman bayan nasarar jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Wasu daga cikin kalmomin sun haɗa da:
FULATANCI HAUSA
Kindirmu Kindirm
Bukkare Bukka
Burtal Burtali
Jalloru Jallo
Bappa Baffa
Kaawu Kawu
Goggo Goggo
Kaaɗo Kaɗo
Ndottijo Dattijo
Nagge Nagge
Donngol Dangwali
Waɗannan kalmomi sun nuna yadda harshen Hausa ya ƙara faɗaɗa a sanadiyyar hulɗa da Fulatanci.
Tasirin Hausa A Kan Fulatanci
Baya ga Hausa ta karɓi kalmomi daga Fulatanci, ita ma Fulatanci ta aro kalmomi daga Hausa, musamman a lokacin da Hausa ta samu karɓuwa a matsayin harshen kasuwanci da hulɗa a Arewacin Najeriya.
Wasu Daga Cikin Kalmomin Hausa Da Fulatanci Ya Aro Daga Hausa:
Hausa Fulatanci Kalmomin Fulatanci Na Asali
Abinci Abinci Nyaamdu
Anguwa Anguware Ɓaade
Aya Ayaje Waccuje
Gero Geeroori Mumri
Iri Iriri Awdi
Makwabci Makobciiji Keddo
Fili Filire Nokkuure/yayre
A wasu lokuta, Fulatanci ta karɓi kalmomi duk da tana da nasu, sakamakon sauƙi da ƙarɓuwa da waɗannan kalmomi suka samu daga H
Tasirin Cudanya ga Harshen Fulatanci
Ga wasu kalmomi daga Fulatanci suka sauya ma’ana ko lafazi saboda tasirin Hausa. Misali: Wannan lamari na harshen da ke tasiri kan wani yana da alaƙa da abin da Weinrich (1953) ya bayyana da cewa yana faruwa ne a tsakanin masu jin harsuna fiye da guda ɗaya. Shi kuwa O’Mally da Chamot (1995) sun danganta hakan da “rikiɗa” ko “transference” daga harshe zuwa wani.
Hausa/Fulatanci mai tasirin Hausa Daidaitattun Fulatanci
Jiya da daddare Kenya jimma Hanki
Sa takalminka Waatu padema Fada padema
Sa rigarka Waatu taggurema Borna taggurema
Sa hularka Waatu hufneera ma Hufna
Yana cin karas Emo yakka karas Emo nyaama karas
Kammalawa
Ƙarshe, cuɗanya tsakanin Hausawa da Fulani ta haifar da alaƙar da ta wuce haɗin
zamantakewa kawai. Wannan alaƙa ta shafi harshe, addini, siyasa da al’adu. Bugu
da ƙari, harshen Hausa ya ɗauki wasu kalmomi daga Fulatanci, haka nan Fulatanci
ya karɓi kalmomi daga Hausa, wanda hakan ke nuna haɗin kai da fahimta a
tsakanin ƙabilun biyu. Wannan gamayya ita ce ke haifar da fassarar Hausa-Fulani
a matsayin al’umma guda, duk da bambance-bambancen asali da harshe.
MANAZARTA
Yakasai A.S (2023). Aro da Ƙirƙira a Hausa, Amal Printing Company, kaduna.
Bunza, A. M. (2008). Al’adu da Harsunan Gargajiya a Najeriya. Cibiyar Nazarin Al’adu da Harsunan Najeriya, Sakkwato.
Gusau, S. M. (1993). Harshe da Al’adu. Ahmadu Bello University Press, Zaria.
Ibrahim, M. K. (2006). Tarihin Hausawa da Fulani. Jami’ar Bayero, Kano.
Balogun, S. A. (1980). History of Islam in West Africa. Lagos: Longman.
Weinreich, U. (1953). Languages in Contact: Findings and Problems.
Danna nan don karanta Ɓacewar Harshe (LANGUAGE EXTINCTION)
Edita@rumasau-kallamu