SALMANU FARISS ADAMU
An haifi Mujahid Abdullahi a ranar 29/03/1987 a unguwar Zaɓi, wacce take kusa da unguwar Saidawa a garin Kudan, kuma cikin ƙaramar hukumar Kudan, a Jihar Kaduna. Ya fara karatun sa ne a Model Primary School Kudan a shekara ta 1995-2000. Ya yi karatu a Barewa Collage Zaria a shekara ta 2000-2006, ya yi karatun digirin sa na farko a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) a shekara ta 2007-2012 ɓangaran Hausa.
Haka kuma ya yi karatun digirin sa na biyu a jami’ar Ahmad Bello (ABU) ɓangaren Hausa a shekara ta 2014-2017. Bugu da ƙari kuma sashin addinin ma ya yi karatun sa dai-dai gwargwado.Har ila yau, ya koma jihar Katsina, don yin digirinsa na uku. Wanda a ranar Alhamis 20/02/2025, ya samu damar kammala digirinsa na uku (PhD).
Koyarwa/aiki
1.Ya yi aiki a sashin koyar da harsuna na jami’ar Kaduna (KASU) a matsayin mataimakin malami (assistant Lecturer) a watan takwas shekara ta 2018 zuwa yau (August 2018 to Date).
2.Ya yi aiki na wucin-gadi da DFID/UKAID a matsayin mai tallatawa haɗi da wayar da kai (Mobilizing for Development Project) daga August 2013- December, 2017.
3.Ya yi aiki a sashin koyar da harsuna na jami’ar Kaduna (KASU) a matsayin mai kula da ɗakin karatu na Jami’ar daga watan September 2012 zuwa June 2013.
4. Ya zama mataimaki na bincike akan harkan yaɗa labarai na yanar gizo-gizo ga shugaban Ƙaramar hukumar Kudan daga watan August 2016 zuwa March 2017. Da sauran su
Muƙalolin sa
1. Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa a ƙarni na Ashirin Da ɗaya.
2. Bugun Gaɓa a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).
3. Ɓurɓushin Nakasa a Adabin Hausa: Tsokaci Daga karin magana”.
4. Bara Cinikin Su Makaho.
5. Tubalin Samuwar Ilimin Boko Da Rubutaccen Zuben Hausa”. (haɗin gwiwa da Malumfashi, I)
6. “The Impact of International Organizations in Promoting Local Governance in Nigeria.
7. Hankaka Mai Da ɗan Wani Naka.
8. Adabin Bara.
9. Salon Tallace-Tallacen Magungunan Gargajiya a Kasuwar Maƙarfi (wannan takardar ba a bugata ba).
Lambobin yabo
1.Kwamitin dattijan malamai na Jami’ar KASU sun ba shi lambar girmamawa da jajircewa wajen tsayawa tsayin daka da kawo ci gaba ga ɗalibai na ajin farko da na aji na biyu da kuma na aji na uku (100 Level, 200 Level and 300).
2. Ɗalibi mafi ƙwazo a ɓangaran Hausa a makaranatar Barewa College Zaria, 2006.
3. Ɗalibi mafi ƙwazo na biyu a makarantar Model Primary School Kudan, 2000.
4. Ɗalibi mafi ƙwazo a ɓangaran harshen Hausa da Turanci, Model Primary School Kudan, 2000. Da sauran su.
(Mun samu waɗannan jawaban ne daga bakin Mujahid Abdullahi Kudan ta hanyar rubutawa da ya yi ya turo min ta WhatsApp a ranar Alhamis 15/10/2020)
Danna nan don karanta Manufar Rayuwar Duniya
Edita:@rumasau-kallamu