Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta ayyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda ya zo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024.
Da take bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano da ke Mambayya, Farfesa Halima Abdulƙadir Ɗangambo wanda Shugaban kwamitin gasar ya bayyana a madadin ta ya bayyana labarin Bahaushiyar Al’ada wanda marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara Kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar.
Haka kuma, ya bayyana labarin gadon gida saida Horo wanda Danladi Haruna (Zakariyya) ya rubuta a matsayin wanda ya zo na biyu, Sai labarin Hauwa Shehu Mai taken Bahaushe Mai arziƙi ne a matsayin wanda ya zo na Uku cikin labarai 50 da suka fafata a gasar.
Dubban marubuta, da mawaka, da taurarin fim ne suka halarci taron, yayin da mawaƙa da dama suka nishaɗantar da taron da waƙoƙin masu sanyaya rai.
A nashi jawabin shugaban hukumar Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa kan yadda gasar ta gudana tare da taya wanda suka yi nasara murna. Ya yi fatan alhairi ga mahalarta taron tare da addu’ar Allah ya bar zumunci ya sa kowa ya koma gida lafiya. Haka nan shugaban hukumar ya ayyana 31 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar marubutan jihar kano, ko bayan ya bar kan kujerar shi.
Hukumar ta ba wa wanda ya zo na farko kyautar Naira dubu ɗari biyar sai na biyu Naira dubu ɗari uku a yayin da ta uku ta samu kyautar Naira dubu ɗari biyu.
Don karanta manufar rayuwar duniya danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu