An haifi Aliyu Sani a garin Kudan kuka wanda aka fi sani da suna “na annabi” a ranar talata 12/4/1982, ya taso a cikin garin Kudan, ya yi karatun firamare da sakandire duk a garin Kudan, sannan kuma ya yi karatun allo a Zaria, bayan ya yi sauka, sai ya wuce makarantar koyar sana’o’i wacce take birnin gwari a Dogon dawa a cikin jihar Kaduna, wacce take koyar da ilimin noma da kiwon dabbobi (Agric Training School). A yanzu kuma yana aiki a hukumar Kastelea ta jihar Kaduna.
Dalilin da ya sa ya fara bege shi ne, wata rana a makarantar allo yana bacci, sai ya yi mafarki an tara masa mutane da yawa sai aka ba shi amsakuwwa (lasafika) yana rera waƙa, amma kuma ba zai iya tuna irin waƙar da yake rerawa ba, bayan ya farka daga baccin, sai ya roki Allah ya cika masa burin sa, aiko Allah ya amsa muradin sa, saboda ya rera bege da yawa daga cikin su akwai ;
1.Na riƙe Mustafa annabi Ɗaha.
2.Lale-lale mauludi.
3.Ni dai gaskiya ina ƙaunar manzo.
4.Mai daraja da muƙami.
5.Almukhtari.
6.Almadani.
7.Ba zan bari ba.
8.Oyo-oyo maulidi ya zo.
9.Mu muna son manzonmu.
10. Maulidin annabi sai mun yi.
11.Marhaba ɗan Amina shugaba.
12. Ya Muhammadu shugaba na.
13. Rasulu bege a gunka soyayya ce.
14. Azzahara’u ‘yar ma’aiki.
15. Halin rayuwa.
16. Mu yi nazari.
17. Mai ilimi.
A ƙarshe kuma, ya yi aure yana da mata guda ɗaya da ‘ya’ya guda huɗu.
(Mun samu wannan bayanin ne daga Aliyu Sani na annabi Kudan, wanda ya turo min ta waya ta a ranar Alhamis 17/06/2020 da misalin ƙarfe 6;33 na dare).
Danna nan don karanta tarihin marigayiya Hajiya Gude
Edita; Rumasa’u M. kallamu