An haifi Alaramma Surajo Yunusa a ranar 07/03/1966 a garin Kudan, cikin ƙaramar Hukumar Kudan, Jihar Kaduna, Nigeria. Sunan Mahifiyarsa Maimuna, sunan mahaifinsa Liman Yunusa. Ya rasu a ranar Alhmamis 06/04/2017 dai-dai da 9/7/1438 A.H.
Kuma ya bar mata biyu, ya bar ‘ya’ya’ guda goma sha biyu (12), Maza bakwai (7) da Mata biyar (5). Allah Ubangiji ya amince masa ilimai, musamman wajen warware sarƙaƙiya ta ɓangaren rabon gado, wanda har sai da ya yi shura tun daga ƙaramar hukumar Kudan har zuwa Zaria akan wannan fannin da sauransu.
Karatun Addinin / Litattafai
A ranar Litinin 06/02/1984 dai-dai 5/5/1404 ya fara rubutun Alƙur’ani. Ranar Laraba 9/09/1984 dai-dai 24/12/1404 ya kammala rubuta Alƙur’ani. Ranar 11/12/1986 ya kai Alƙur’ani gida, Kudan. Ranar Litinin 19/09/1984 dai-dai 24/12/1404 ya fara karatu wajen Malam Musa Ƙofar Nasarawa jihar Kano.
A ranar Laraba 24/4/1991 dai-dai 11/10/1411 ya fara karatu da Malam Lawal Jinjin. Ranar 06/05/1991 dai-dai 23/10/141, ya fara karatu da Malam Mammada gidan malamai Kudan. Ranar 12/08/1991 dai-dai 2/2/1412 aka ɗauke shi aikin koyarwa a Model Primary School, Kudan. Ya tafi aikin Hajji a ranar Lahadi 15/11/2009 dai-dai 27/11/1430.
Ya dawo ranar Alhamis 10/8/2012. Ya jagoranci sallar juma’a na riƙo na tsawon sati shida a rayuwarsa. Ya fara a ranar 10/08/2012. Sannan kuma ranar litinin aka ba shi muƙamin (S.A.S) a ƙaramar hukumar Kudan, wato Senior Arabic Supervisor (Shugaban Malaman Arabiya Na ƙaramar Hukumar Kudan).
Karatun Zamani
Ya halarci makarantu kamar haka;
1. Model Primary School Kudan, Kaduna (Sep, 1973 – June, 1978).
2. School For Arabic Studies, Kano (S.A.S) (1983 – 1989).
3. Institute of Education, Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria (1985 -1989).
4. Jama’atu Institute of Arabic & Islamic Education, Zaria (2000 – 2002).
5. Institute of Education, Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria (2000/2002 Session). Allah Ya amshi rayuwarsa a ranar Alhamis 06/04/2017 = 9/7/1438 A.H, Allah Ya gafarta masa zunubansa, Amin.
Don karanta al’adar Bahaushe danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu