Marigayi malam Mammada (wato Muhammad wanda aka fi sani da malam Mammada) an haife shi a garin Kudan a watan Azimi. Sunan mahaifinsa shi ne Malam Abdulhamid, mahaifiyar sa kuma Habiba (‘Yar gero), ya haifi ‘ya’ya goma sha shida a duniya, guda shida sun rasu kafin ya rasu.
Ya auri mataye guda biyu daga cikin ‘ya’yan sa akwai Muhammad da Suleman da Ɗayyabu da Hafsat da dai sauran su. Ya yi karatun allo a garin Kudan da kuma Zaria gidan malam na Iya. Ya kuma tafi Kano ya yi karatu a wajen malamai da dama, ya kuma tafi Azare ta jihar Bauchi, ya yi karatu a can ma.
Malam Mammada mutum ne wanda yake sana’ar siyar da garwa daga Kudan zuwa Kano, domin samun abin sa wa a baka wai ya fi a rataya in ji masu iya magana. Saboda haka malam Mammada ya samu ilimi mai zurfi a ɓangaren ilimi addinin musulunci, wanda har Alaramma malam Surajo Yunusa Kudan, wanda ya rubuta littafi akan rabon gado a wajensa ya yi karatu.
Haka kuma shi ne kusan babban ɗalibin sa, saboda duk inda zai tafi wajen koyar da karatu ko rabon gado, to da malam Surajo Yunusa Kudan yake tafiya. Haka kuma a lokacin da yake raye malam Mammada har sai ta kai matakin da dukkanin littafin da mutum ya buɗe, to malam Mammada yana kishingiɗe zai biya maka littafin ba tare da ya tambaye ka sunan littafin ba.
Haka kuma, idan mutum ya yi kuskure wajen karantowa, to sai dai ka ji kawai ya gyara ma yadda wajen yake, haka kuma Malam Shitu Bashir Kudan ya tabbatar mana da cewa idan mutum kullum zai dinga zuwa wajen malam Mammada karatu har tsawon rayuwar sa, to ba zai iya ƙure ilimin da Allah ya ba shi ba, sannann kuma shi ne wanda yake fassara alkur’ani a masallacin juma’a na garin Kudan a lokacin da yake raye, haka kuma ya rasu a watan Azimi a ranar 16/09/1440 hijira=2018
(Mun samu waɗannan jawaban ne ta hannun ɗan sa wato Suleman Muhammad wanda ya kira a waya ranar litinin 17/03/1442 hijira=02/11/2020 da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe a lokacin ina gidan Musa Gauda shi kuma yana Kaduna).
Domin karanta cinikin bayi a tarihin Afrika danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu