Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Uku

0
17

Yawancin cinikin Bayin da aka yi a wannan ƙarni na 16 ana ɗiban su ne ana kai su Satomi inda suke noman rake da sigari  tobacco taba kenan, sai kuma waɗanda ake kai su Elmina  ƙasar Ghana inda suke haƙo gwal, a wannan lokacin dai Bayin da aka dinga ɗiba wannan abin suka dinga yi abin bai kankama ba sosai, kuma a sauran shekaru da suka biyo baya.

Abin ya yi tsamari dalili kuwa shi ne, na farko su Spain da Portugal sun kafa sansanin su wato Colonies ɗin su a Brazil da kuma wasu ƙasashe na ƙasar Amerika, wannan ya sa sun fara neman mutane da yawa don su je su yi wannan aikin noma saboda su mutanen ƙasar Brazil ba su da ƙarfi kamar mutanen Afrika a ɗauke su su yi aikin wahala, saboda haka  wannan ya sa cinikin ya bunƙasa ana ta ɗiban mutanen Afrika ta Yamma ana kai su. 

Dalili na biyu kuma shi ne, su waɗannan Turawa masu cinikin bayi sun ta kawo kayayyakin su suna sayarwa da sarakuna na wannan ƙasashe, su kuma waɗannan sarakunan wannan dukiya da suka samu ta ƙara musu ƙarfi da kuma bindigogi da suka dinga sayar musu musamman da sarkin Dahome da Oba na Lagos da Oba na Benin da kuma Sarakunan Ifik na can kusa da Calabar.

Suna ba wa mutane suna shiga suna ɗebo musu bayi  daga  sauran ƙasashe, wannan kayan yaƙi da Turawa suka kawo ya sake ragargaza mutanen Afrika, saboda ƙarfin da suka ba wa waɗannan sarakuna su kuma suna yin amfani da shi su na ɗebo mutane, inda har ta kai aka ɗebi mutum miliyan ashirin (20 million)  a wannan lokaci. 

Waɗannan shekaru ƙarni na 17 da 18 da na 19 fiye da ƙarni na 16 inda  kawai mutum miliyan ɗaya ne (1million) aka ɗiba. Kuma su Turawan Ingila ba su shiga ba, to shigar Turawan Ingila ma shi kenan magana ta canja, saboda a wannan lokaci sun samu Amerika sun fara ɗiban mutane suna kai su Amerika suna yi mu su noma.

Sai Ingila ta zo ta wuce ma Spain da Portugal a harkar sayen bayi, saboda ita ta samu Amerika kuma wannan ya taimaka ya ƙara ƙarfin Ingila, saboda cinikin bayi shi ne tabbatar Ingila da suka yi amfani da shi suka samu ƙarfi a Amerika suka samu dukiya har suka zo suka caccanja abubuwan suka samu sauyin arzikin masana’antu (Industrial Revolution).

Kuma an ce daga Liverpool ma kawai bayin da aka ɗauka a shekara goma 1783-1793 sun kai dubu ɗari uku aka ɗiba daga gaɓarta. Dalilin cinikin bayi ma har ta zama cewa ta samu ɗaukaka a duniya, kuma su kansu Turawan nan su suka yi rubutu suka dinga ba da labarin yadda ake yin cinikayyar Bayin nan da yadda ake yi wa mutane azaba da sauran su.

Har ma akwai wani Kaftin John Adams shi ma ya rubuta littafin sa mai suna Scaches taken 10…. Of Africa between 1786 and 1800, ya yi maganar irin abubuwan da ya gani a Lagos da cewa mutane an yi faɗa ko ana yaƙi, an ɗebo Bayi waɗanda suka yi faɗa an sossoke kawunan su a kan bishiya ga shi nan kana ganin kawunan mutane, kuma ga wasu irin ɓera su ma saboda mushen mutane da suke ci sun bunƙasa sun yi yawa.

Ya ce wani lokacin ma idan Turawa sun zauna in dai ba ka ɗaga kaya ba za ka dinga ganin ɓerayen su na shigowa ta ƙarƙashin su. Akwai wani shi ma William Bossman shi ma ya rubuta littafi mai su na New and accurate description of the coast of Guinea aka buga shi a Landon a shekarar 1805.

Inda yake faɗar yadda ake yi wa Bayin nan cewa a ƙirjin su ake yi musu lamba, kuma mata ba su fi kwata ko kashi ashirin tsadar namji ba yadda ake sayar da su, idan kuma aka shiga da su ruwan ma duk kwashe musu kayan su ake yi a tafi da su tsirara, kuma jirgin ya kan ɗauki mutum 600 zuwa 700. 

Micheal Crowder ya yi lissafin irin mutanen da aka ɗiba daga nan Yammacin Afrika (West Afrika) da Angola ya ce, a ƙarni na 16 an ɗebi mutum miliyan 1, a ƙarni na 17 an ɗebi mutum miliyan 3, a ƙarni na 18 an ɗebi mutum miliyan 7. To yana maganar cewa a duk shekara a kan ɗauki mutum dubu ashirin da biyu daga ƙasar Najeriya, duk da yake cewa a ƙarni na 19 ma an hana cinikin Bayin, amma an ɗebi a ƙalla mutum miliyan 4. 

A cikin irin bayanin da wani mai suna Rossel Warren Horray ya rubuta,  ya ba da labarin yadda ake cinikin Bayi da yadda cewa mutum ɗaya daga cikin mutum bakwai ko wane zai iya zama Bawa a cikin ‘yan Afrika saboda bala’i, kuma namiji ɗaya daga cikin ko wanne maza biyar zai iya zama, mace ɗaya daga cikin kowacce goma za ta iya zama Baiwa, saboda wannan masifar da aka yi ta cinikin Bayin nan.

To cinikin Bayi ya kawo wa mutane rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya, mutane ko yaushe su na cikin tashin hankali na cewa za a iya zuwa a kame ka a tafi da kai, wannan abu ya daɗe ya shiga ƙwaƙwalwar mutane an ragargaje su, gaba ɗaya aka rusa tunanin al’umma saboda harkar Bayin nan.

Wani abu da ya faru a shekara ta 1835 inda wasu daga cikin Bayin da aka kai su Brazil suka yi tawaye, saboda sun samu wasu daga cikin su sun kasance mutanen da suka san Shehu Ɗanfodiyo ne da kuma Jihadin da ya yi, saboda haka wannan ya ba su ƙwarin gwiwa suka yi tawaye.

Don haka mutanen Brazil suka koro su suka dawo da su Lagos, wasu daga cikin su musulmi suka zo suka kafa sansanin su na musulmi, wasu ma da ba musulmin ba suka biyo su da suka ga abin da musulmi suka yi. Wannan ya kawo canji a Lagos da samun abubuwa na ci gaba inda har suka yi Unguwar ‘yan Brazil (Brazillian quarters) a Lagos, har yanzu za ka ga cewa wasu daga cikin mutanen Lagos ɗin za ka ji sunayen su irin su Codoso, Perrara su Sanchez duk wannan sun same su ne a dangantaka da irin mutanen Brazil da suka zauna a can. 

Haka kuma suka zo Lagos suka samu ɗaukaka suka shiga harkokin rayuwa da kasuwanci da harkokin ilimi har suka yi babban masallaci a Lagos, duk wannan su na daga cikin ɓurɓushin waɗanda suka taho daga Brazil da kuma samun wani abu na ci gaba a wannan lokaci. 

Don karanta tarihin Afrika danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceLokacin Da Ya Dace Mace Ta Yi Amfani Da Dabarun Tazarar Haihuwa
Labarin na GabaHaihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)
Dr. Ibrahim Ado Kurawa
An haifi malam, a ranar 10 ga Agusta, 1963, a Kano. Malam ya yi karatu a fannoni daban-daban, tun daga kimiyyar halittu har zuwa karatun Larabci da ilimin addinin Musulunci. Kuma ya wallafa littattafai da takardu masu yawa kan tarihi, siyasa, da al'adu, wanda hakan ya ba shi damar samun kima a duniya, har ma ya zama ɗaya daga cikin masu zama a Rockefeller Villa Serbelloni a Italiya.