Yaushe Tura Za Ta Kai Bango?

0
21

Jama’a wai kwa du kuna iya ji na
Na ga kamar fa ba ku saurare na
Ya na gane ku ne a zaune a rana
An ya ma kwa za ku so waƙe na.

Da dai na mayar wuƙar ƙuguna
Na ajiye dukka al-ƙalumana
Domin ni fa ko? Akwai hange na
Shi nassa gidan ga ba waƙe na.

Yanzu hakan ga za ku zauna ni kam?
Wasu gommai suna zuba muku poison
Ko sai sun fara dangana ku da prison
Ƙarni CENTURY decade kuma season.

Ba ni da arzuƙin zama a gidana
Ba ni abin da zani bai ‘ƴa’ƴana
Balle ma na kai gidan surukaina
Haka kullum nake barin matana.

Yanzu ƙasar ga babu canji kenan
Ba mai tausayin da zai ce uffin
Sai wahala ake ta sha ni wai kam
Ko sararin ga mun fi kowa more than.

Sai an ambata ku ce watarana
In komai ya kai mahudar rana
Akuya in ta dangana bangona
Cizo za ta dunga yi ɗan Chana.

An zo an kashe iyayen wancan
An ɗau wane sai kace Al-kakin
Wane kwa an kashe hi can ba haƙƙin
Matar wane ko gabansa ka haiken!!

An sace ɗiyar mutum fa da rana
Ni kuma an kashe ɗiyata gidana
Haka an sace wance du a idona
Dan Allah ku kai kuɗin fansana.

Na kai shekara rabon a gidana
Da Tukunya ta doshi kan murhuna
Kuma wallahi babu ko son raina
Tsabar an ci ne da haƙƙoƙina.

Na je Hospital a ban haƙƙina
Ba komai cikinsa duk sai yana
Ba daktas da sunka kai saba’una
Kuma adadin garinmu ya fi a auna.

Ba mai faruwa a bayan wannan
Akuyar ta shige ta bayan bangon
Ta ma tsallake ginin har zauren
Ta manta ashe fa an zo bangon.

To ko dai mu tashi ko kwa mu zauna
Ko kwa mu dunga shan bugun fir’auna
Ba baƙon da za ya zo shi gidana
Ya yi aikin da ban iya ba ku auna!!

Sai gyara ake a wassu ƙasashen
Amma mun yi shu kamar ba ma nan
Kuma mun fi su ma karmar mu yi wannan
Dan kwa da mai kama ake yin ƙotan.

Abban Marke.

Edita: Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceDuka A Murɗe
Labarin na GabaMe Za Ka Yi Idan Ka Ga Ɗan Uwanka Zai Mutu?