Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi, kamar haka;
- Ƙurajen gaba
- Ƙaiƙayin gaba
- Fitar da farin ruwa mai kauri
- Jin zafi idan za a sadu
- Jin zafi idan za a yi fitsari
- Ɗaukewar sha’awa
- Kunburin mara ko ciwon mara
- Ƙanƙancewar azzakari ga namiji
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi. Duk da yake fitar da farin ruwa a gaba yana daga cikin babbar alamar ciwon sanyi, amma shi kansa farin ruwa ba kowanne yake da matsala ba. Akwai mara matsala. Shi kansa farin ruwan da yake fita ya kai kala huɗu, ga su kamar haka;
- Akwai mai fita fari tas, kamar koko mai kauri mara yauƙi ko kamar madara;
- Akwai mai fita kamar gasara ko kuma in ce kamar kitse, wata ma sai ta sa hannu a ciki tana zaro shi;
- Kuma akwai mai fitowa kamar zare a rinƙa zaro shi kamar zare, da ya taɓa jiki sai ya bushe;
- Sannan akwai mai fita kamar majina mai haske mai ƙyalli mai yauƙi.
Duk a cikinsu guda uku na ciwo ne wanda ba a sonsu a jikin mace. Wanda ake so shi ne mai fitar kamar majina, mai yauƙi, wannan shi ne ruwan ni’ima. Idan mace ta rasa shi a jikinta to akwai matsala.
Samuwar ɗaya daga cikin ukun nan a jikin mace yakan hana wannan zuwa, daga nan sai ka ga mace ta shiga cikin damuwa.
Domin karanta cikakken bayani akan
Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi danna nan
Domin karanta cikakken bayani akan
Maganin Damuwa danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu