Masana kiwon lafiyar ƙoda sun bayar da shawarar shan tsabtataccen ruwa aƙalla lita 2 zuwa 3 a kowace rana to lita 2 zuwa 3 shi ne mafi ƙarancin ruwan da mutum ya kamata ya sha a rana,saboda haka,shan ruwa fiye da lita 2 zuwa 3 ƙarin alfanu ne ga lafiyar ƙoda musamman a lokacin zafi.
Shan isasshen ruwa na taimaka wa aikin ƙoda wajen wanke ko tace jini da ruwan jiki daga guba da sauran muggan sinadarai da jiki ke samarwa domin fitar da su zuwa cikin fitsari.
Bugu da ƙari,yawan fitar gumi na nuni da yawan ruwan da ke fita daga jiki,kuma yawan gumin da ya fita na nuni da ƙarancin fistarin da za a samu.
Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan
Saboda haka,ƙaranta shan ruwa na da haɗarin gaske domin yana haifar da dunƙulewar sinadaran da ke cikin fitsari har daga ƙarshe ya haifar da tsakuwar ƙoda.ciwon tsakuwar ƙoda na iya tilasta yin tiyatar ƙoda domin cire tsakuwar.
Ruwa Rayuwa Ne!
[…] Domin karanta Amfanin Ruwa Da Lafiya Danna nan […]