Babi Na Biyu:
A cikin wannan babin an bi salsalar ko kuma an kawo taƙaitaccen tarihin samuwar ƙagaggun labaran Hausa ne. An dubi yadda aka fara samar da labaran Hausa na gargajiya kafin su koma a rubuce, da kuma yadda suka samu cuɗanya da baƙin al’adu.
Ya’allah baƙin nan na kusa ne a cikin ƙasar Hausa ko kuma na nesa kamar Larabawa da kuma Turawa domin ganin yadda ƙagaggun Labaran Hausa suka samu canji da fasalce-fasalce daga garjiya zuwa zamani.
Ma’anar Ƙagaggun Labaran Hausa
Masana da dama sun kawo ma`anar ƙagaggen labari da cewa warwarar bayani ne bi-da-bi a kan aukuwar wasu abubuwa da yadda suke gudana, saboda haka ma’anar labari ta haɗa da jerin bayani, da ambaton dukkan muhimman al’amurra da iya siffanta su a lafazi mai kyau (Zarruƙ, 1990).
Ke nan a iya cewa ƙagaggen labari ya ƙunshi waɗansu labarai masu ɗan tsawo, ana kuma yin su ne a lokacin hira kamar, labarai na jarumai ko `yan fashi ko na almara, irin su labaran hikima ko wasa ƙwaƙwalwa da kuma tatsuniyoyi irin na su gizo da ƙoƙi da hikayoyi na iskokai ko kuma aljannu.
Haka kuma Magaji (1982:47) ya ce labarin zube (ƙagaggen labari) ya ƙunshi labarai masu ɗan tsawo kamar tatsuniya (Ga ta nan), da almara, da hikayoyi, da ƙissoshi da sauransu. Haka kuma akwai guntattakin maganganu na hikima kamar kirari, da karin magana, da kacici-kacici, da zaurance, da salon magana da dai sauransu.
A taƙaice za a iya cewa labarai sun kasu gida biyu; na haƙiƙa ko kuma masu ƙamshin gaskiya, wanda aka fi sani da ƙissa ko tarihi ko tarihihi da kuma na ƙirƙira ko kuma ƙagaggen labari, wanda bai da asali ko tushe.
Saboda haka ana iya bayyana ƙagaggen labari da wata hikima, ko basira ko tunani irin na ɗan Adam da ya ƙaga kan wani abu wanda bai ji ba, kuma bai gani ba, ya furta shi da fatar baki domin watsa wata manufa don koyarwa ko kuma hannunka-mai-sanda da jagora don nishaɗi.
Akwai ire-iren waɗannan ƙagaggun labaran da yawan gaske a cikin adabin Hausa da suka haɗa da tatsunniya da almara da hikaya da zaurance da salon magana da kirari da take da zambo da sauransu da dama.
Haka kuma ana iya kallon ƙagaggun labarai na baka da zance na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa a kara zube, kuma mai ɗan tsawo, mai kuma ban sha’awa da koyar da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban.
Samuwar Ƙagaggun Labaran Hausa
Tun kafin haɗuwar Bahaushe da baƙi, yana da hanyoyi da dama da yake amfani da su domin ilimantar da kuma tarbiyantar da ‘ya’yansa ta yadda za su tashi cike da dabaru da kuma ilmin zamantakewa. Waɗannan hanyoyin kuwa su ne ire-iren ƙagaggun labaran da ya tanadar, sun kuwa haɗa da maganganunsa na azanci da sauransu.
Tambayar da aka yi ita ce yaya aka yi waɗannan abubuwa suka samu? Daga waɗannan maganganun azanci ne aka samar da ƙagaggun labarai, waɗanda tushensu shi ne adabin bakan al’umma.
Kuma kamar yadda masana suka nuna wannan ba sabon abu ba ne, domin kuwa ko a zamanin ci gaban Girkawa, ire-iren waɗannan sassan adabin aka fi ba muhimmanci wajen tarbiyantar da jama’a, domin labarai da maganganun azanci da suka yi tashe a wancan lokacin da baki ake aiwatar da su, daga wannan birni zuwa wancan (Malumfashi, 2004:6), sun kuma taimaka wajen ilmantar da al’ummar.
A nahiyar Asiya kuma irin waɗannan al`adu na fasahohin baka sun ginu, ta yadda a fadojin masu mulki da masu arziƙi, an samar da manyan masana labarai da maganganun azanci don su zama tamkar makaranta ta koya wa ‘ya’yan masu mulki da sauran masu arziƙi tarbiyya, su kuma nishaɗantar da al`ummar nahiyar. Labaran Sansikirti a Indiya da maƙwabtanta duk irin wannan fasalin suka ɗauka, kuma da yawa daga ire-iren waɗannan labaran sun kasance asalinsu ɗaya ne, wato tatsuniyoyi da almarorin jama’ar wannan yanki ne, (Malumfashi, 2004:6)
Saboda haka, muna iya cewa a ƙasar Hausa ma irin wannan adabi ya yi tashe a lokacin maguzanci ko jahiliyya. Wato gargajiya ita ce jahiliyyar Bahaushe, lokacin da al’ummar Hausawa ba su waye ba ko kuma lokacin ba su haɗu da wasu baƙi ba, wannan zango ne tsakanin ƙarni na 10 zuwa na 11.
A wannan lokacin ana neman matakai waɗanda za a fara rayuwa ta kan su, lokaci ne na neman wurin zama da abinci da gina shugabanci da yadda za a tsara shi, da kuma tsarin sana`o`i daga wurin mutane. Don haka, ilahirin wannan lokaci ya ƙunshi fafutukar gina al`adu na gargajiya. Wannan shi ne zangon da ya samar da adabin baka da sassansa da lokacin da ake ganin ana da adabin ka na tsantsar Hausawa.
A wannan lokacin ne aka samar da kirare-kirare na bauta da kirarin noma da na farauta da kuma waƙe-waƙen mata da labarun gargajiya da labarun tatsunniya da na jaruntaka da kuma na ban dariya (Muhammad, 2005:6).
Saboda haka ko da irin wannan adabi na baka ya ginu, ya tashi ne kurum ya gan shi cikin al`ummar Hausawa, ta yadda Hausawan ke koyar da ‘ya’yansu dabarun zaman duniya ta yin amfani da sassan adabin baka na zube (ƙagaggun labarai) da suka haɗa da tatsuniyoyi da labarai da makamantan su. Bari mu dubi wasu daga cikin waɗannan sassan ƙagaggen labarin Hausa, mu ga yadda suke a taƙaice.
Tatsuniya
Tatsuniya tana daga cikin manyan rassa na adabin bakan Bahaushe, kuma ƙagaggen labari ne da Bahaushe kan ba ‘ya’yansa domin tarbiyya ta yadda za su tashi cikakku kuma kamilan mutane.
Masana da dama sun daɗe suna kallon tatsuniya ta fuskoki daban-daban, Umar (1978: 25) yana cewa “tatsuniya wani ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya, musamman don tarbiyya bisa ga tsarin gargajiya”. Amma shi kuma (Gusau, 2006:112) cewa yake “tatsunniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musamman tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare”.
Duk da irin yadda tunani ya bambanta tsakanin masana game da ma’anar tatsuniya, sai dai masana da dama (Yahya, 1972 da Umar, 1978 da Alhassan da wasu, 1982 da Ɗangambo, 1984) duk sun yarda da cewa tsofaffi ne kan shirya tatsuniya, kuma ƙagaggen labari ne da akan shirya domin ilimantarwa ga yara.
Daga nazarin da aka yi an fahimci cewa tun can farkon al`amari Hausawa suna da labaransu na tatsuniyoyi waɗanda su ne suka ƙirƙiro su da kansu don nishaɗi da koyarwa. Sun mallaki wannan hanya ta bayyana matsayinsu, musamman ga yara, tun jimawa, ba sai da suka cuɗanya da wata al`umma ta koya musu ba.
Hasali ma dai ba za a iya bugun gaba a ce ga lokacin da aka fara yin ta ba. Tatsuniya gadon gado ce, ta ginu a sakamakon tasirin al`adar rayuwa ta Hausawa, har ta zama ruwan dare game duniya (Yahya da wasu 1992). Haka kuma, labari ne ƙagagge ake harhaɗawa a tayar da gangar jikin tatsuniya, har a kaɗa ta, ta bayar da wani amo da ake son sadarwa ga masu saurare.
Saboda haka muhimmancin tatsuniya ya fi gaban a ambata, domin kuwa tatsuniya makaranta ce ta malam Bahaushe, ta nan yakan ilimantar da `ya`yansa dabarun zaman duniya tun kafin Bahaushe ya sadu da baƙi. Al`adun Hausawa ne suka haifar da tatsuniya kuma wajibi ne a yi la`akari da cewa tatsuniya ta samu tun kafin Bahaushe ya iya karatu da rubutu balle ya kafa makaranta.
Tatsuniya ta wanzu cikin al’ummar Hausawa wadda tunaninta da hikimominta da fannonin ilminta duk da baki ne akan baza su, daga wannan mutum zuwa wancan da kuma wannan zamani zuwa wancan. Koyo da koyarwa, ɗabi’ar ɗan Adam ce, saboda haka ya zama tilas ga Bahaushe ya ƙirƙiro wata hanya ta aikawa da hikimominsa da al’adunsa daga zamani zuwa zamani.Ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ita ce tatsuniya. Ta amfani da tatsuniya Bahaushe kan kaifafa tunanin ‘ya’yansa.
Labari
Labari shi ne wani zance da yake abkuwa tsakanin mutane ko tsakanin mutum da mutum wanda ya wuce tsayawa a gaisa kurum. Kusan duk wani abu da ya danganci samar da wani abu game da wani abu mai tsawo ko gajere ana iya kiranshi labari.
Shi dai labari zai iya kasance wa tsararre mai ma`ana sannan kuma yana da farko da kuma ƙarshe wanda kuma zai iya cusa tarbiyya ko kuma a koyi wani darasi daga cikin shi. Kazalika, labari na iya kasancewa a rubuce ko a magance.
Labari na zuwa ta hanyoyi daban-daban, kamar Yanayin abinda labarin yake ɗauke da shi ta fuskar jigo ko siffa, wato dai a taƙaice abinda yake koyarwa. Kamar labarai na jaruntaka, da tarbiyya, da girmamawa, da zaman duniya da sauransu da dama.
Ƙissa
ƙissa kalma ce da aka samo daga harshen Larabci wadda ta shige tsundum a cikin adabin Hausa. Ita da wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni biyu ne a cikin harshen Larabci. A ma’ana ta lugga ƙissa na nufin bibiya ko ƙididdigewa, wato mutum ya bi diddigin wani abu har zuwa ƙarshensa.
A ma’ana ta fannin ilimi kuwa, ƙissa na nufin ba da labarai dangane da mutanen da suka shuɗe, ko kuma ba da labari a kan waɗansu abubuwa da suka auku a da, ko kuma wani labari da ke kara zube da ya ƙunshi shiryarwa zuwa ga addini ko gaskiya ko neman tsira kan wani abu.
A ra`ayin masana (Gusau,1995:68) an fi danaganta ma’ana da manufar ƙissa a kan labarun da suka danganci addini kawai. Wato bayanai a kan rayuwar annabawa da sahabbai da waliyyai da sauransu. Duk da haka akwai wasu labarai na ƙayatarwa da jawo hankali da za a iya kiran su da ƙissa, kamar irin ƙissoshin da suka shafi soyayya. Don haka akan ce ƙissa wata hanya ce ta cusa wata manufa cikin zukatan masu saurare.
Duk da irin wannan hasashe game da ƙissa an fahimci cewa ta shafi abin da ya biyo labaran Annabawa kamar yadda ya zo cikin Alƙur’ani mai girma, inda ake da surori da suke bayyana labaran annabawa da aka zayyana a cikin Alƙur`ani.
Sai dai ita ƙissar da Bahaushe ke bayani ta shafi wadda aka gina bisa tunanin Bahaushe, wato ga yadda labarin yake a zahiri amma a ƙara masa wani abu ko dai don daɗin labarin ko kuma domin a ƙara ƙayatar da mai sauraro. Misali ƙissar Annabi Yusuf ko ta Annabi Sulaiman ko kuma ta Annabi Nuhu za a same su da ɗan bambanci da wadda Alƙur’ani ya zo da ita.
- Ƙissar Cinye Dare: Wadda ta ƙunshi labarai da zuntuttukan da mutane suke yi don cinye ko ƙarasa dare.
- Ƙissar Addini: Wannan ta ƙunshi labarai ne da ake tsarawa a kan wani abu da ya auku na addini a lokacin annabawa da sahabbai da waliyyai da shehunnai da sauransu.
A Hausance ke nan, ƙissa labari ne na gaskiya da aka bayar a kan rayuwar Annabawa da sahabbai ko waliyyai ko shehunnan malamai, ko wasu bayin Allah da sauransu waɗanda suka shafi addinin Musulunci, musamman waɗanda Alƙur’’ani da hadisai suka kawo bayanansu.
Masana (Gusau, 1995: 69) sun raba ƙissa zuwa gida huɗu;
- ƙissar Annabawa wadda ta bayyana rayuwarsu ta haƙiƙa da irin gwagwarmayar da suka sha wajen isar da saƙon Ubangiji.
- ƙissar sahabbai da waliyyai da shehunnai wadda ke ƙunshe da rayuwarsu.
- ƙissar sauran bayin Allah wadda ke nuna rayuwar wasu bayin Allah nagartattu waɗanda suka miƙa wuyansu ɗungurungum zuwa ga addini Allah
- ƙissar kangararrun mutane waɗanda suka bijire wa addinin Allah.
Tarihihi
Asalin wannan kalma ta tarihihi an samo ta ne daga kalmar tarihi ta hanyar liƙa wa kalmar ɗafe-ƙeya na ‘hi’, sai ta koma ‘tarihihi’. Sai dai abin lura a nan shi ne tarihi dai yana nufin wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma.
To amma shi tarihihi za a iya cewa wani labari ne na wasu abubuwa da suka taɓa wakana na haƙiƙa a cikin al’umma, sai dai irin wannan labarin yana cakuɗe da wasu abubuwa da ba a tabbatar da faruwarsu ba. Don haka idan aka ce tarihihi, a taƙaice ana nufin gurɓataccen tarihi, wanda aka cakuɗe shi tsakanin gaskiya da ƙarya.
Tarihihi labari ne na da ake riƙe da shi a kai, kuma kasancewar kai ba mariƙi ba ne, ballantana har ya yi ajiya, sai wajen ruwaito abubuwan da suka faru a rayuwa ake gwama su da waɗanda ba su faru ba. Wato dai yawancin tarihihi ya ƙunshi labarai ne na kunne-ya-girmi-kaka, waɗanda ba a iya tabbatar da abkuwarsu.
Akwai tarihihi kala-kala a ƙasar Hausa, sai dai waɗanda suka yi tashe sun haɗa da na tarihihin zuwan Bayajidda ƙasar Hausa, da na sarkin Katsina Korau, da WaliƊanmarna, da WaliƊanmasani, ko naƊanwaire da sauran su.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Domin karanta Al’adun Hausawa Na Jiya Da Na Yau danna nan
Edita@rumasau-kallamu