Yadda Ake Haɗa Fondant

0
950

A yau za mu koyi yadda ake fondant.

Abubuwan Da Ake Buƙata:

  • Icing sugar
  • 1 tbsp Corn syrup
  • 1 tbsp Glucose
  • 2 tbsp Gelatine
  • 1 tbsp Glycerine
  • ruwa 4 zuwa 5 tbsp
  • 1 tbsp Cmc
  • Corn flour
  • 1 tbsp Flavour
  • gishiri
  • 1 tbsp Butter

Yadda Ake Haɗawa

  1. A sami kwano ɗan ƙarami, sai a zuba gelatine kamar cokali biyu, a sa ruwa kamar cokali 4 haka a juya.
  2. Sai a juya shi, amma zai iya ɗan burtsatsai bai yi smooth ba.
  3. A zuba ruwa a tukunya, a ɗora a kan wuta, amma ruwan ba mai yawa ba, yadda idan an sa kwanon da aka zuba gelatine ɗin ba zai sha kansa ba.
  4. Sai a sa glucose a juya sosai, sanna sai a sauke, sai a zuba flavour, corn syrup, glycerine a juya sanna a ɗan sa gishiri da butter.
  5. Sai a ringa juyawa ana ƙarawa, ana juyawa kamar ana kwaɓin dough, a haka za a ga yana ƙwari har sai an ga ya daina kama hannu.
  6. Sanna idan ana yi a tabbatar ana yin shi a kan leda ko irin waje me kyau da tsafta kuma idan ana murzawa kada a yi da yatsu, tafin hannu za a yi amfani da leda mai yatsu.
  7. Idan yana kamawa za a iya barbaɗa corn flour a ƙasan wajen ko icing sugar.
  8. Za a ga idan ya yi sosai, zai daina kama hannu, zai zama dough sosai, sai a sami Leda a sa a ciki, yadda iska ba za ta shiga ba, ya daskare.
  9. Sai a yi kwalliyar da ake so idan wani kala ake so, za a iya sawa a murza shi.

Domin sanin Yadda Ake Pizza danna koren ruutun nan.

labarin da ya wuceInganta Rayuwar Ma’aurata Ta Hanyar Karin Magana
Labarin na GabaYadda Ake Yogofruit
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.