Muna kira don ba da gudunmawar muƙalu

Shigo a dama da kai, ba wa WikiHausa gudunmawa wajen inganta harshen Hausa a WikiHausa, muna gina gagarumin ƙamusu don amfanin masu magana da harshen Hausa a duniya baki ɗaya kuma muna buƙatar taimakon ku! Muna gayyatar masana ilimin harshe da malamai da marubuta da masu amfani da harshen Hausa a yau da kullum don su kawo gudunmawa ta yanda za mu alkinta kuma mu ɗabbaƙa harshen Hausa a yanar gizo.

Me yasa za ka ba da gudunmawa? Gudunmawarka za ta taimaka wajen adanawa da inganta harshen Hausa don amfanin masu tasowa. Samun Sanayya: Masu ba da gudunmawa akan ƙamusu da maƙalu za a san su a cikin manhajar, hakan kuma zai ba su damar baje kolin gwanintar su. Haɓaka Sana’a: Marubuta da malamai da masana harshen za su bunƙasa harshen Hausa ta hanyar ba da gudunmawa ga duniya baki ɗaya. Tasirin Al’umma: Idan ka sanar da ilimin da ka ke da shi jama’a za su koya kuma su yaba kyawun harshen.

Ta yaya za a dama da kai: Maƙala: Sanar da ilimin da kake da shi akan maudu’an da suka danganci al’adun Hausawa da tarihi da harshen da sauran su, ta wannan shafin namu na yanar gizo www.wikiHausa.com.ng Bunƙasa ƙamusu: Danna nan domin taimakawa da kalmomi wajen bunƙasa ƙamusun mu ta hanyar ba da sababbin kalmomi ko inganta ma’anonin da muke da su da a ƙamusun mu.

Aikin Fassara:Za ku iya zama masu fassara rubuce-rubuce zuwa harshen Hausa a wikiHausa ta hanyar yi mana magana kai tsaye ta nan. 09019086105 Shigo yau ka ba da gudunmawa a WikiHausa–inda kowace kalma take da tasiri!

Siyi kuma ka siyar da littattafan Hausa a shafin siyar da littattafai ta yanar gizo na WikiHausa. Shafin littattafan WikiHausa kai tsaye ne! Muna samar da hanyar kasuwanci ga marubuta, da masu buga littafi da kuma makaranta, don saye ko siyar da littattafan Hausa. Idan kana neman inda za ka buga ayyukanka ko kuma kana neman rubuce-rubucen Hausa na ban mamaki, WikiHausa manhajar ka ce.

Me ya sa za ka siyar da littattafanka a WikiHausa? *Zai samu isa ga mutanen duniya: Nuna littattafanka ga masu amfani da harshen Hausa na duniya. *Ƙarin Riba: Marubuci zai samu kaso mafi yawa daga farashin littafinsa. *Sassauƙar hanya: Dora littafinka ka fara siyarwa cikin hanya mai sauƙi.

Me ya sa za ka siya daga WikiHausa? Tallafawa Marubuta: Duk littafin da aka siya yana tallafawa marubutan Hausa wajen alkinta harshen. Zaɓi: Bincika nau’o’in ƙagaggun labarai da tarihi da waƙoƙi zuwa ga littattafai na ilimi. Sauke littafinka da zarar ka siya ka fara karantawa a kowacce irin na’ura.

Fara siya ko siyar da littafin ka a yau! Ziyarci shafin siyar da littafan WikiHausa don ɗora littafinka na farko.