Yadda Aka Yi Bautar Kurmin Jakara A Kano

0
45

BAUTAR JAKARA

Ga abinda ya zo a littafin Tarihin Kano game da Bautar Kurmin Baƙin ruwa ko a ce kurmin Jakara.

Ma’abotan wannan ƙasa (Kano) waɗanda Bagauda ya same su a cikinta suna mulkin garinsu, ba su bin kowa sai Tsumburbura da duhuwa tasa JAKARA. Ana ambatonta (duhuwar) da KURMIN BAƘIN RUWA, domin shi ruwa ne baƙi, duhuwa ta kewaye shi, ana kiyaye dukan musiba da ita da gunkinsu.

Mafarinta kuwa daga Gurgumasa har zuwa Dausara. Kiraranta da zartakenta ba su motsi sai idan musiba ta gabato wannan gari ta yi kuruwa sau uku, hayaƙi ya riƙa fitowa daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin tsakiyar ruwa. Sai su nemi baƙin kare su yanka a ƙarƙashin Tsumburbura, kuma su yanka baƙin bunsuru a cikin duhuwar.

Idan hayaƙi da kururuwan sun daɗu, to babu makawa sai musibar ta sadu da su. Idan kuwa ba su daɗu ba, babu masiba. Sunan duhuwan nan kuwa MADAMA. Kuma sunan Tsumburbura RANDAYA’.

Ƙarin Bayani game da KURMIN JAKARA

Ita Jakara ana kiranta da suna KURMIN-BAƘIN-RUWA saboda ruwan tafkin baƙi ne, kuma kewaye take da bishiyoyi masu yawa. A cikin bishiyoyin ne akwai guda ɗaya da aljani yake kanta, wadda suke yin tsafinsu a kanta, kuma wadda take yin hayaƙi idan musiba ta tunkaro Kano.

Ita wannan bishiyar a tsakiyar ruwan take. Wannan daji mai yawan bishiyu sunansa MATSAMA, Bishiyar tsafin kuma ita ce RANDAYA. Ɗaukacin wajen shi ne Jakara har zuwa inda Kasuwar Kurmi take a yanzu.

Daga Littafin KANO TA DABO TUMBIN GIWA na Alhaji Ahmad Bahago

Danna nan don karanta Asalin Kafuwar Jihar Katsina

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaƙa Mai Taken Ladubban Tsuguno
Labarin na GabaWaƙa Mai Taken Abokin Tafiya
Sadiq Tukur Gwarzo
Sadiq Tukur Gwarzo marubuci ne mai binciken tarihi da son taskance ilimi da taimakon al'umma.