Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

0
37
  1. Allahu sarki ka ban sani,

Da zai yi amfanuwa ga ni,

Cikin dare har ma da wuni,         

Tsare ni aikin take sani,

Ina ta roƙon ka mai niya.

2. Ƙaro salati ga Ahmadu,

Sidi masoyinmu sarmadu,

Fiye da ‘ya’ya da walidu,   

Shumagaba namu Rashidu,

Wannan da ya zo da shiriya.

 

3. Ya ɗan uwa zance zan maka,

Bisa ga haƙƙin maƙwabtaka,

Da malamai sun faɗa maka,        

To ga ni zan jaddada maka,

Don mu kiyaye shi bai ɗaya.

 

4. Akwai maƙwabci na gun zama,

Gidanka ga nasa hakka ma,

Duk wanda ke layin da zama,

Baya gaba dama hauni ma,

Su ne maƙwabtanka ka jiya.

 

5. Akwai maƙwabci na kasuwa,

Wurin sana’a ke haɗuwa,

Ko kuwa ofis ke gamuwa, 

Zama na mota domin zuwa,

Wani gari yayin tafiya.

 

6. Haƙƙin maƙwabci ko kafiri,

Ne ba shi za ai ba jinkiri,

In ko musulmi ne na gari,  

Haƙƙi na addini tun wuri,

Ga na maƙwabta za a biya.

 

7. In ko musulmi ne ɗan uwa,

Na jika to ukku haƙƙuwa,

Na musulumci na ‘yan uwa,

Na uku haƙƙin maƙwabtuwa,

Za a cika babu tawaya.

 

8. Haƙƙin maƙwabci fa babba ne,

Ba da shi yankin imani ne,

Kada mu tauye ko ƙanƙane,       

Wannan umarnin Manzonmu ne,

Zuwa gare mu baki ɗaya.

 

9. Ka so masa duk abin ƙwarai,

Kamar da ka so wa kanka kai,

Abin tsiya kar ka so garai,

Kamar da ka ƙi gare ka kai,

Cikin dare ko ko safiya.

 

10. In ya buƙatu ka taimaka,

Don ɗan uwa yake gu naka,

Kai za ya farko sanar maka,       

Kafin kiran ‘yan uwan jika,

Da ke a can nisan tafiya.

 

11. In ya yi cuta dubo shi yi,

Ka nuna damo da tausayi,

Gare shi ko da sartse ya yi,

In ma da ɗan hasafi ka yi,

Shi ne tafarki na shiriya.

 

12. Kar kai gini mai tsawon bisa,

Jikin katangar gida nasa,

Iskar ƙwarai ka tare masa,

Sai ka biɗi izini nasa,

Kada ka soma in ya ƙiya.

13. Sharar da ka yi ka tattara,

Kada ka watsa ta gangara,

Gaban gidansa ba hattara,

Ko da kuwa shi zai haƙura,

Cutar maƙwabci haramiya.

14. Ka soya nama na raguna,

Ko kuwa kaji da zabuna,

Amma maƙwabcinka ka hana,

Rabonsa ƙanshi ga hantuna,

Cuta kake yi ƙazamiya.

 

15. Kada ka kwana a ƙosashe,

Shi ko maƙwabcinka busashe,

Ya kwana yunwa za ta kashe,

Dukkan tukwanensa ƙeƙashe,

Kai kuwa kaji a jar miya!   

 

16. Annabi ya ce “Bai so ni ba,

Da ni ku san bai imani ba,

Wanda ya kwan ƙoshe bai ji ba,

Yunwa maƙwabci kwano gaba,

Ya yi zugum babu lomiya.”

 

17. Aro na kayan buƙatuwa,

In ya biɗa sai ka basuwa,

Manjagara tsani don hawa,

Wuƙa in ya roƙi daddawa,

A sam masa gishirin miya.

 

18. Dukkan abin yin farin ciki,

Idan ya samar kamar biki,

Ka zam taya shi har kaɓaki,

Ka yi masa in baƙin ciki,

Ne ku yi tare ba wariya.

 

19. Haƙƙin maƙwabcinka ne idan,

Ya mutu to kan gaba ka zan,

Wajen suturce jana’izan,

Har fa a binne shi saliman,

Zaman makoki kar ka ƙiya.

 

20. Idan da hali ka tallafa,

Wa su iyalan ɗa’am dafa,

Ka ba su ko tsabar su dafa,

Tanyon marayun ka duƙufa,

Ba za ka taɓe ba duniya.

 

21. Cutar maƙwabci mu hanƙure,

Kullum mu yafe in yai kure,

Dukkan haƙi nasa mu tsare,

Laifinmu Allah zai kankare,

Ran lahira mu yi dariya.

 

22. Kada mu zam cutar sa muke,

Ko da ko shi cutar mu yake,

Aljanna ba shi wanda yake,

Cutar maƙwabci ko a fake,

Faɗarsa Manzo abin biya.

 

23. Allahu kab ba mu juriya,

Bisa zamn tare lafiya,

Ba ce-ku-ce ba hayaniya,

Mu zam game kai ba fariya,

Amin mu zam shafa fatiya.

 

24. Mai tsara waƙar ga Nasiru,

Ahmad ko ko sha’iru,

Wannan da ke koyon shi’iru,

Ba mahiri ne ko baharu,

Bisa ga waƙe ba kun jiya.

 

25. Ran Juma’a ne na kammala,

Waƙar maƙwabci don mu kula,

Ga jalla sarki nai hamdala,

Ya khaliƙina salli ala,

Ɗaha da ya zo da gaskiya.

 

Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceƘaddamar Da Manhajar Karin Magana Challenge
Labarin na GabaYadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take
Nasiru G. Ahmad
Haifaffen jihar Kano ne a unguwar 'Yan awaki. Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan harshe da adabin Hausa. Yana cikin ƙungiyoyi da dama na marubuta a ciki da wajen jihar Kano. Malami ne kuma mawallafin littattfai da waƙoƙi.