Waƙa A kan Dangina

0
861

Salam alai dangina, Ku amsa domin ƙauna, Allah daɗo tsiran na, ga Shugaba Manzona, Mai son sa ba ya gaba.

 • Tsira, aminci ƙara,
 • Ga sahiban nan jera,
 • Mai son su ba ya ƙyara,
 • Sai so da ƙauna jera,
 • Daɗo aminci Rabba.
 • ———————————
 • A yau akwai wani zance,
 • Ku bi ni, kar da na mance,
 • Batu na murna kunce,
 • Na bayyano ba ƙifce,
 • A zaurukan nan babba.
 • ——————————–
 • Lasan na yo tattaki,
 • Cikin aminci ɗoki,
 • Domin halartar fa biki,
 • Na tsara baitin baki,
 • Na jera murna babba.
 • ———————————
 • Abokanai sun zo wa,
 • Ta ko’ina ba ƙiwa,
 • Domin su nuno sowa,
 • Cikar mutunta da yawa,
 • Su shaidi ƙauna babba.
 • —————————–
 • Da safe in yai wanka,
 • Ran Juma’a ba shakka,
 • Da yamma yai tattaka,
 • Gare ki sai sam-barka,
 • Domin ku zazzaga hira.
 • —————————–
 • ƙarshen ta cuta mutuwa,
 • haka ƙarshen gani soyewa,
 • kuma ƙarshen fa so aurewa,
 • A dabdale bidirewa,
 • A so a kore gaba.
 • —————————–
 • Nura abokin kaina,
 • Aurenka nai wa murna,
 • Na tsara baitin ƙauna,
 • Domin gabatarwana,
 • Aure zumunci babba.
 • —————————-
 • Fa Nura kare haƙƙi,
 • Ka bi su kar ka yi raki,
 • Tuwo, tufafi ɗauki,
 • Ka ba ta har fa a baki,
 • Da rangwaɗar nan duba.
 • ———————————
 • Auren ga sunnar Manzo,
 • Ku raya domin ƙwazo,
 • haka Ku yi shi har ku yi tozo,
 • Dan Ku amsa kiran Manzo,
 • Don Ku zazzago so babba.
 • ————————–
 • Amarya zan yo kanki,
 • Ki tsara kanki da kanki,
 • Biyayya ba yin birki,
 • Mijinki shi ne angwanki,
 • Gare ki tamkar Baba.
 • —————————
 • Ki lallaɓa shi a komai,
 • Danginsa so su da sosai,
 • Ki tausaya mai ji nai,
 • Ki toshe kunnen son rai,
 • Allah ya kawo riba.
 • —————————-
 • Nayaya na tsara,
 • Baiti fa sha uku jera,
 • Hanyar zuwa nat tsara.
 • NWAN uwa mai gyara.

domin samun karanta waƙoƙi danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceSaƙo Ga Masoyiyata
Labarin na GabaYadda Ake Kwalakca