Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

0
18

Kamar yadda tarihin rayuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya tabbatar; shi mutum ne mai kula da ciyarwa da shayarwa da tufasarwa da samar da muhallai na zaman iyalinsa da makusantansu; da sauran waɗanda suke majiɓinta a gare shi.

Sannan yakan yi wa iyalinsa tarbiyya gwargwadon yadda addinin Musulunci da al’adu kyawawa na Hausawa suka tanada.

Mutum ne kuma wanda yake fafutukar haɗa kan dukkan zuriyyarsa da yi musu addu’a su zauna salim alim; ba ƙyama ko faɗa ba wata hauragiya ko ƙiyayyar juna. Haƙiƙa, wannan wata hanya ce ta wanzar da zuriyya bisa haƙuri don ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Musa Ɗanƙwairo kamar yadda ya tashi, ya gani a gidansu, ya himmatu ta fuskar yin noma da duka ayyuka na gona; don samar da abinci da abubuwan masarufi waɗanda suka zamanto abokan zama.

Sau da yawa; Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ba ya buƙatar duk wani abu da zai hana shi yin noma a kowace faɗuwar damina. Ta haka Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya nuna ba ya son jama’arsa ta tagayyara. Saurari wata damuwa ta makaɗa Musa

Ɗanƙwairo a sa’ilin da Damina Bakolori ya tauye shi a yin noma a wata damina:

Jagora(Daudu): Allah shi ka kawo komi,
: Yaƙin Dam Bakolori ya ci mu,
‘Y/Amshi: Sai in faɗa ma Mamman,

: Ban da gida yanzu ban da gona, Jagora(Daudu): Yanzu cikin damina ni kai ta shirin,
‘Y/Amshi: Gyaran wurin da za ni bacci, Jagora(Daudu): Yanzu gidan Makaɗa ya zamo gurbi na ƙwarai,

: Wanda ad da zurhi,
‘Y/Amshi: Sarkawa su sukai da taru,

Jagora(Daudu): Sarkin Daura ko da damina,
: Sai kai ta shirin tariyab baƙi,
‘Y/Amshi: In wasu sun kore mu mu taso,

: Muhammadu in wasu sun kore mu mu taso,
Jagora(Daudu): Ba ni zama inda babu gona,
‘Y/Amshi: Ba ni zama inda ba abinci,

: Babban jigo na Yari,
: Uban Shamaki tura haushi.
(Ɗanƙwairo, Waƙar Babban Jigo, ta Sarkin Daura, Alhaji Muhammad Bashar (1966-2007)

Bayan harkokin noma, makaɗa Musa Ɗanƙwairo kuma ya yi kiwon shanu da tumaki; da awaki da Kaji da sauran dabbobi da tsuntsaye. Ya ƙaura ya bar wa iyalinsa yin waɗannan sana’o’i.

Domin karanta cikakken bayani akan Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo) Usman Ɗankwanagga a 1991 danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun; A Aiwatar Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTarihin Shehun Malami Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki (1897-1959)
Labarin na GabaTarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868-1998)
Prof. Sa’idu Muhammad Gusau
FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU, An haife shi a Gusau jihar Sakkwato, (Maris 24, 1952). Ya yi karatun firamare na Islamiyya daga 1965-1969, ya je kwalejin sarkin Musulmi Abubakar daga Junairu 1970 zuwa Yuni 1973. Ya yi Diploma, Digiri Na farko (B.A), na biyu (M.A) da Digiri na uku (Ph.D) duk a jami'ar Bayero, Kano.