Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya 2025

0
15

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya gudana cikin nasara a ranar 31/12/2025 a ɗakin taro na Manpower Development Institute da ke garin Dutse jihar Jigawa, inda ya haɗa marubuta, manazarta, malamai, ‘yan jaridu, ɗalibai, da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na Nijeriya da maƙwabtanta.

Taron ya ƙara jaddada muhimmancin rubutun Hausa a ƙarni na 21, musamman a fuskokin tsaro, tattalin arziki, al’adu, da ci gaban al’umma.

Muhimman Abubuwan Da Aka Tattauna A Wajen Taron:

1. Ƙalubalen Tsaro da Al’adar Karatu: An jaddada cewa duk da ƙalubalen rashin tsaro, akwai babbar matsala ta raguwar al’adar karatu musamman a tsakanin matasa, wadda ke buƙatar tsayuwar daka. An ba da shawarar a fara gyara tunani tun daga makarantu, ta hanyar kafa kulob-kulob na karatu da al’adu, tare da gayyatar marubuta su riƙa yi wa ɗalibai bita kan muhimmancin rubutu da karanta littattafai.

Sai kuma yadda za a yi amfani da fasahar AI domin gina rubutu mai inganci da kuma sauƙaƙawa marubuta da amfanin hakan ta fuskar tsaro da tattalin arziƙi.

2. Zaurukan Tattaunawa (Panels):

“Rubutun Zube na Hausa a Onlayin: Ina aka dosa?” inda masana suka tattauna muhimmanci da ƙalubalen rubuce-rubucen onlayin, musamman matsalar rubutun batsa.

“Marubuta Mata a Jiya da Yau: Ina aka dosa?”

“Rubutun Gajerun Labaran Hausa: Ina aka fito? Ina ake? Ina aka dosa?”

“Tattaunawar waƙoƙin Hausa.”

“Rubutun Hausa a wajen ƙasar Hausa”

Waɗannan zauruka sun samar da ilimi mai zurfi da gogewa wadda ke da wahalar samuwa a wuri guda.

3. Halarta da Wakilci: Taron ya samu halartar marubuta sama da 250 daga faɗin Nijeriya, tare da wakilcin gwamnatocin Arewa musamman Kano, Katsina da Jigawa. Haka kuma, an samu baƙi daga ƙasashen Togo, Kamaru, Senagal da kuma ƙasar Nijar.

An bayar da kyaututtuka ga manyan baƙi na musamman da kuma marubutan da suka samu nasara a gasar da aka shirya don taron.

Ga wasu daga cikin hotunan taron

Kammalawa

Taron ya tabbatar da cewa rubutun Hausa ginshiƙi ne na gina tunani, tsaro, da tattalin arziki, kuma dole ne a ƙara ƙaimi wajen farfaɗo da al’adar karatu da rubutu, musamman a tsakanin matasa. An amince da ɗaukar darussa daga ƙalubalen da aka fuskanta domin ƙara inganta taruka na gaba.

Danna nan don karanta Taron Makon Hausa FCE Bichi 23 Oktoba 2025

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaƙa Mai Taken Rabbi Kare Min Mijina
Labarin na GabaWaƙar Neman Mafita Da Riba Babba