An haifi mai girma Isa Muhammad Ashir a garin Kudan a ranar 23rd ga watan October, 1962, a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna. Ya yi karatu a Model Primary School Kudan daga 1968-1974, ya yi karatu a makarantar Kufena wacce take a Wusasa Zaria a 1976-1980.
Ya yi karatu a Polytecnic Katsina a 1982-1985, wanda ya samu shaidar Diploma a ɓangaren harkan kasuwanci (Business administrative), ya kuma halarci makarantar Polytechnic Kaduna, wanda ya yi karatun gaba da Diploma wato HND a 1987-1989.
Haka kuma a 1990 ne ya halacci wajen horas da manyan ɗalibai, wato NYSC Corps a Barno (BD/KD/89/4217). Sannan kuma a 1999 ne, ya yi Post-graduate a ɓangaren cinikayya (marketing management). Bugu da ƙari kuma ya yi Master’s degree a public policy and administration a 2000-2001 a jami’ar Bayero Kano (B.U.K).
Har ila yau, ya tsunduma harkar siyasa a 1996 a Jam’iyyar Zero party (ZP), wanda ya tsaya takarar shugaban ƙaramar hukuma (Chairman), amma bai samu nasara ba, ya kuma sake tsayawa a jam’iyyar Social democratic party (SDP) a 1997, sannan kuma ya zama member a KSHA ƙarƙashin jam’iyyar DPW a 1999-2000. A inda aka zaɓe shi a matsayin ɗan-majalisar jihar Kaduna (House of Assembly) mai wakiltar Kudan-Maƙarfi zuwa 2000-2003.
Haka kuma, an sake zaɓansa a matsayin ɗan-majalisar jihar Kaduna daga 2003-2007. Sannan kuma an sake zaɓansa a 2007-2011 a matsayin ɗan-majalisa na tarayya mai wakiltar Kudan-Maƙarfi a jam’iyyar People Democratic Party (PDP). Haka kuma, ya sake zama ɗan-majalisa na Tarayya a karo na biyu daga 2011-2015.
Haka kuma a 2014 ne ya koma jam’iyyar All progress congress (A.P.C), wanda ya yi takarar Gwamna na zaɓen cikin gida, amma bai samu nasara ba, a 2019 ne kuma ya sake tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyar PDP bayan ya koma cikin Jam’iyyar, wanda kuma bayan an yi zaɓen gama-gari nan ma bai samu nasara ba. Haka kuma ya yi aure yana da mata guda ɗaya da kuma ‘ya’ya guda bakwai.
Bugu da ƙari kuma, ya sake tsayawa takarar Gwamna a kakan zaɓe ta 2023, a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, wanda a nan ma bai samu nasara ba, tun da mutane suna ganin cewa an yi maguɗin zaɓe sosai.
Sannan kuma, ya samu damar samun sarautar Sarkin bai Zazzau, wanda masarautar Zazzau ta naɗa shi, duba da irin tulin ayyuka na ci gaba, wanda ya samar da su a lokacin da yake kan mulkin. Haka kuma an samu ‘yan majalisun jiha da na Tarayya a ƙaramar hukumar Kudan-Maƙarfi, amma kuma ba a samu wani wanda ya kai shi aiki ba, saboda a lokacin da ya riƙe waɗannan mukamai ya samar da ayyuka kamar haka;
1.Ya gina babban Asibiti a garin Kudan kusa da masallacin Idi na garin Kudan.
2. Ya gina makarantar horas da ‘yan sanda a garin Kudan hanyar Sundu ko hanyar Barmo.
3. Ya gina Masallacin Juma’a a garin Kudan, wanda yake ƙofar gidan hakimi.
4. Ya gina makarantar koyan sana’a, wanda take kan hanyar zuwa Doka daga Kudan.
5. Ya gina makarantar Firamare a ƙofar Arewa a garin Kudan.
6.Ya gina ɗakin koyan sarrafa na’ura mai kwakwalwa a garin Kudan da Hunƙuyi (E-library).
7. Ya gina wajen zaman ‘yan Sanda (Headquater) a garin Kudan kan hanyar zuwa Doka daga Kudan.
8. Ya gina wajen koyon wasan ƙwallon ƙafa a garin Kudan wanda yake kan hanyar zuwa Garu.
9. Ya gina ɗakin taro a garin Kudan wanda yake kan hanyar zuwa Garu.
10. A samar da fitilloli masu samar da haske ta hanyar amfani da hasken rana (electry-Solar) a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.
11. Ya samar da famfo wanda yake amfani da hasken rana (Water-solar) a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.
12. Ya tura mutane ashirin zuwa ƙasar wajen domin yin karatun digiri na farko.
13. Ya samar da tituna a cikin garurruwan da suke a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.
14. Ya sabunta da faɗaɗa ginin Dam, wanda yake Kudan kan hanyar zuwa Doka ko Sundu daga Kudan.
Guraren da ya yi aiki
1. Ya yi aiki a ma’aikatar kuɗi (Ministry of finance) a 1980-1982.
2. Ya yi aiki a ma’aikatar samar da kuɗin cikin gida (Internal Revenue) a 1985-1992.
3. Ya yi aiki a ma’aikatar kasuwanci da wajen shakatawa (ministry of commercial Industry and Tourism) a 1992-1993.
Danna nan don karanta tarihin Adamu Yero Hunƙuyi
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu