An haifi Salahuddin Sani a gidan limamin juma’a na garin Kudan, wanda ke ƙofar Arewa Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan a ranar 01/01/1989, ya yi karatu a Model Primary school take Kudan a shekara ta 1995-2000. Ya yi karatu G.G.S.S Kudan a 2000-2006, ya yi karatu a makaranatar gaba da sakandire ta Maƙarfi wato Shehu Idris Collage of Health a 2014-2017. Ya yi aikin asibitin kuɗi da ke Kaduna Tudun Wada mai suna AITAM.
Yanzu kuma yana aiki a asibitin Gwamnati wanda ke garin Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna. Sannan kuma ya fara karatun addininsa ne a makarantar Hayatul Islam ƙofa, wacce take bakin kasuwa Kudan, amma kuma ya yi saukarsa ne a makarantar Irshadul Aulad wacce take ƙofar Arewa Kudan, haka kuma ya fara bege ne a Irshadul Aulad a 2003 waƙar da ya fara yi ita ce “Mubar cuta”, sannan kuma ya yi karatun fiƙihu a wajen marigayi malam Suraj Yunusa Kudan, ya yi karatun allo a wajen Alaramma malam Iliya na tsawon shekara biyu kafin ya kuma zuwa islamiyyah.
Shaharar sa
Shi ne wanda ya assasa ƙungiyar sha’irai a garin Kudan mai suna Raudatul shu’ara’ul Islam Kudan a shekara ta 2015, wanda a yanzu tana da mutane guda ashirin. Bugu da ƙari kuma, ya iya sana’ar kafinta wanda ya koya a wajen ‘ya’yansa wato Ahmad Gaddafi, ya kuma iya sana’ar nona da kiwo, sannan kuma shi ne wanda ya buɗe makarantar Taufiƙil Islam, wanda take Furoja a garin Kudan, jihar Kaduna.
Ya kuma rubuta ƙasidu da dama , ga kaɗan daga cikin kamar haka;
1. Raddi.
2.Shu’ara’u ‘yan Kudan.
3. Raudatul Shu’ara’ul Islam.
4. Ta’aziyyya (Rabi’u).
5. Ƙololuwar matsayi.
6. Ranar murna.
7. Maulidin muke yi.
- (Mun samu wannan jawabin ne daga bakin Salahuddin Sani wanda ya rubuta ya turo min da shi ta waya (Message) a ranar Asabar 25/12/2020) da misalim ƙarfe 7;30 na safe).
Domin karanta tarihin Salmanu Faris Adam danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu