An haifi Malam Aliyu a zamanin Sarki Abdullahi a garin Kadawa cikin ƙaramar Hukumar Warawa da ke Jihar Kano. Hamshaƙin malamin Alƙur’ani, ma’abocin zaumunci da kyauta.
Malam Aliyu ya yi tafiye-tafiye na neman Alƙur’ani har sai da ya dangana da ƙasar Maiduguri, baya ga lokacin da ya ɗauka yana gwagwarmayar neman karatu tsakanin Gaidam da Gayan da ke garin Haɗeja.
An ce a lokacin da Turawa suka fara zuwa Kano, Malam Aliyu na rubuta AIƙur’aninsa na biyu. A lokacin kuwa da Gwani Hamad ya bayyana a birnin Kano. Malam Aliyu Ɗankadawa na daga cikin Gwanayen AIƙur’ani da suka sanya allo a gabansa don ɗosana daga hasken da Ubangiji Ya ba shi na ilmin tajwidi da ƙira’o’i.
Saboda irin shaharar da Malam Aliyu ya yi wajen sada zumunci kuwa, ya kasance duk da girma ya kama shi; ya kan yi shiri wani lokaci ya yi tafiya mai nisa da ƙafa cikin wasu garuruwa don kai ziyara ga tsofaffin alarammomi abokan karatu tun lokacin ƙuruciya.
Game da karamcinsa kuwa, ya lazimta wa ‘ya’yansa zuwa gidajen aminansa da ke kusa; domin gaishe su a kowace safiya da yi musu wasu ayyuka kafin ma su gaishe shi ya amsa. Alaramma Malam Aliyu ba ya shigar da wani abu na sadaka gidansa har sai ya rabar da shi ga almajransa. Almajiri ba ya samun fada a warin malam sai in kaɗai ya rungumi Alƙur’ani ka’ in da na’in.
Game da baiwar Alƙur’ani da rubuta shi kuwa; Alaramma Malam Aliyu Ɗankadawa ya kasance hatta a lokacin tafiya ba ka rasa shi da kayan rubutun AIƙur’ani. Da ya samu wata dama ko yaya ta ke to, sai ya cigaba da rubuta Alƙur’ani abinsa. Da haka ya ribaci rayuwarsa ta hanyar amfanı da lokaci komai ƙan-ƙantarsa.
Kaɗan daga cikin almajiransa sun haɗa da:-
- Malam Yalwa
- Malam Musa Gurgu Takai
- Malam Abubakar
- Malam Garba Kurna
- Malam Rabi’u Gezawa
- Malam Isa Ringim
Ubangiji Maɗaukaki Ya yi wa Malam Aliyu Ɗankadawa tsawon rai don ya rasu a shekarar 1998 yana ɗan shekaru 130; ya bar ‘ya’yaye waɗan da suka haɗa da:-
- Malam Ya’u
- Malam Ɗayyabu
- Malam Tasi’u da
- Malam Haruna
Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Sheikh Malam Mahammad Ɗan Almajiri danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.