Tarihin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

0
55

Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. An haife shi a shekara ta 1964 a garin Danbagina da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Ya girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano.

Ya fara karatun allo,(Alƙur’ani) a makarantar marigayi Malam Rabi’u a Unguwar Zangon Bare-bari a shekarar 1968 da karatun littattafai na Islamiyya, a makarantar marigayi Sheikh Tijjani na ‘Yanmota, (1971). Bai sami damar yin karatun boko yana ƙarami ba, sai da ya girma sannan ya shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci Adult Evening Classes, Kano a shekara ta 1984 zuwa 1986.

Ya yi makarantar sakandare ta dare (G.S.S. Warure Evening Session), Kano a shekara ta 1987 zuwa 1990. Ya shiga Jami’ar Bayero inda ya sami takardar shaidar Diflomar ƙwarewa a kan yaɗa labarai, wato (Professional Diploma in Mass Communication) a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005.

Ya rubuta littattafai da aka buga su kamar haka: In Da So Da Kauna 1-2 da Masoyan Zamani 1-2 da Hattara Dai Masoya 1-2 da Wani Hani Ga Allah 1-2 da Duniya Sai Sannu da Kaico! Mata Da Shaye-Shayen Kayan Maye:Ina Mafita? da Malam Zalimu (wasan kwaikwayo) da Ina Mafita (wasan kwaikwayo) da Dakika Talatin (wasan kwaikwayo) da Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan (tarihi), wanda suka rubuta tare da Sani Yusuf Ayagi da From Oral Literature to Video:The Case of Hausa. (Takardun da suka gabatar a jami’a Hamburg, Jamus, shi da Farfesa Abdalla Uba Adamu).

An kuma fassara wasu daga cikin littattafansa guda uku daga harshen Hausa zuwa Turanci: The Soul of My Heart (Fassarar In Da So Da Kauna) da Nemesis (Fassarar Masoyan Zamani) da kuma Kaico! (Fassarar Kaico!) Young Women Substance Abuse and The Way Out (Fassarar Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye:Ina Mafita?)

Ya gabatar da muƙalu da dama a tarurrukan ƙara wa juna sani a cikin Nijeriya da ƙasashen waje. Wasu daga cikin takardun nasa an buga su a cikin kundaye (littattafai). Yana yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujallun Hausa.

Tare da shi aka kafa wasu ƙungiyoyi, kamar Kungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen jihar Kano, (ANA) a shekara ta 1992, kuma ya riƙe shugabancinta na tsawon shekara uku da ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, (Kano State Film makers Association) wanda a halin yanzu shi ne shugaban riƙo na Ƙungiyar da Ƙungiyar Marubuta ta Raina Kama (Raina Kama Writers Association)wanda kuma shi ne shugabanta.

Shi ne Mai Gabatar da shirin Alƙalami Ya Fi Takobi, a gidan rediyo Freedom, Kano da kuma shirin Duniyar Masoya a gidan rediyo Shukura FM da ke Damagaram, ƙasar Nijar. Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba shi damar zuwa ƙasashe fiye da goma sha biyar na Afrika, sannan kuma a ƙasashen Turai ya sami zuwa London da France da Italy da Holland da kuma Germany.

Ya zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009 ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir Karaye, a Abuja, Nijeriya. Ya sami takardun yabo da dama daga jami’o’i da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummawa iri-iri da yake bayarwa waɗanda suka shafi harshen Hausa da adabi da aladu ta fannin rubuce-rubuce da shirin finafinai da aikin jarida da harkokin ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati.

A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 ya sami takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha ɗaya da aka yaba da su a jihar Kano wajen bayar da gudummawa game da ci gaban aľ’umma. Sannan a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da yake yi a cikin ayyukansa.

A shekarar 2017 ya sami zuwa matsayin tantancewa ta ƙarshe (nomination) a gasar finafinai ta Zuma Film Festival da ke Abuja a matsayin jarumin jarumai na Afrika. A shekarar 2018 ya sami nasarar lashe kambun jarumin jarumai har sau uku a cikin gasar AMMA Award da Kaduna International Film Festival da Arewa Entertainment, sannan ya amshi kambun mai shirya finafinai da ya zarce kowane (Best Producer) a ‘KILAF Film Festival’ duk a cikin fim ɗin Juyin Sarauta.

A shekarar 2019, ya sake zama jarumin jarumai (Best Actor in Leading Role) sannan ya amshi kyautar alƙalan gasa (Golden Jury Award) a gasar Kaduna International Film Festival.

Yana cikin ƙungiyoyi kamar haka:

  • Motion Picture Practitioner’s Association of Nigeria, MOPPAN
  • Association for PromotingNigerian Languages and Culture, (APNILAC)
  • West African Research Association (WARA)
  • Indegenous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN)

Mutum ne mai Sha’awar tafiye-tafiye da rubuce-rubuce da bincike. Yana da mata ɗaya da ‘ya’ya biyar. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ne Shugaba kuma Daraktan Gudanarwa na kamfanin Gidan Dabino International Nigeria Limited.

Littattafan Marubuci

  • In da so da Kauna, 1, 2 (1991)
    Hattara Dai Masoya, 1, 2 (1992)
  • Masoyan Zamani, 1, 2 (1993)
  • The Soul Of My Heart, (Fassarar In Da So, (1993)
  • Wani Hanin ga Allah…,1,2 (1994)
  • Nemesis, (Fassarar Masoyan Zamani, 1995)
  • Kaico!, (Hausa,1996)
  • Duniya Sai Sannul, (1997)
  • Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Mukhtar Adnan (Ado Ahmad da Sani Yusuf Ayagi, 2004)
  • Malam Zalimu ‘Wasan Kwaikwayo’, (Hausa, 2009)
  • From Oral Literature ti Video: The Casa Of Hausa, (Ed: Joseph Mechthild Reh, 2011)
  • Mata da Shaye-Shayen Kayan Maye: Ina Mafita?(2012)
  • Daƙiƙa Talatin,(2015)
  • Young Women Substance Abuse and The Way Out (2019)(Fassarar Mata da Shaye-Sayen Kayan Maye:Ina Mafita?)
  • Malam Zailani, Ci Gaban Malam Zalimu, Wasan Kwaikwayo'(2021)
  • Dausayin Fasaha, Rubutattun Waƙoƙi, (2023)
  • From Oral Literature to Video:The Case of Hausa,(Ed:Joseph Mdntyre and Mechthild Reh,2011)

Littattafai Masu Fitowa

  • Ina Mafita?
  • Kaico!(Fassara zuwa Ingilishi)
  • Malam Zalimu (Fassara zuwa Ingilishi)
  • Rabuwa
  • Gani Da Ido…

Don karanta Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu M. Gusau danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFitowar Haƙora Ga Yara, Faɗuwarsu, Da Sake Fitowarsu
Labarin na GabaMalaman Ƙasar Zariya