An haifi Abdullahi Mustapha a 1985 a unguwar tsauni Kudan. Ya yi karatu Islamiyya a Madarasatul Hayatul Islam bakin kasuwa Kudan daga 1990/1997. Ya yi Firamare daga 1990/1996. Ya yi karatun gaba da Firamare daga 1997/2014.
Ya sake komawa makaranta, wanda ya yi karatu a National Teachers Institude Kaduna (NTI), amma a ɓangaran karatun nesa (Distanca learning Studies) a reshen su da ke Hunƙuyi, wanda a nan ne ya samu shaidar malanta (NCE).
Bayan haka, ya yi gwagwarmaya a gidan mai (Petroleum station) gidan man na mahaifinsa, tun a shekara ta 1995-1998 inda daga nan Allah ya amshi rayuwar mahaifinsa marigayi Alh. Zakari Haladu Kudan, Allah ya ji ƙansa da rahama.
Bayan wasu shekaru ya fara tunanin ya fara aiki a studio wato shagon ɗaukan hoto, sannan ya nemi izinin babban mai ɗaukar hoto na wannan lokaci wato marigayi Hassan haske Allah ya ji ƙansa da rahama, inda a wurinsa ya samu ƙwarewa na tsawon shekaru biyar (wanda shi wancan bawan Allah yana ɗaya daga cikin mutanan da suke zuwa Kudan ɗaukar hoto a duk ranar Juma’a) kuma sun rabu da shi lafiya cikin girmamawa da ladabi.
Bayan haka, wani lokaci Alhaji Sabi’u Ibrahim kansila a lokacin yana da studio, shi ma ya ɗauke shi aiki a shagonsa, a matsayin shugaban shagon ƙarƙashin kulawar Aliyu Wada (mai Talata) na tsawon wani lokaci. A wannan studio, ya yi aiki tare da ma’aikata uku, wato Usman Isah (Ameer hoto) da Jamilu Zakari da Sani Umar.
Dukkanin su ya koya musu aiki ta yanda kowannen su ya samu ƙwarewa, biyu daga cikinsu ma sun samu damar mallakar studio nasu, wato Usman Isah (Ameer hoto) da kuma Jamilu Zakari. A yanzu haka yana da babban studio, wanda mallakarsa ne, wanda yake printing/photocopy da su. Yana yin noma da kasuwanci, yana da aure da ‘ya’ya, Allah ya ƙarama rayuwa albarka amin summa amin.
Ya yi karatu a Nigerian communication commission (NCC) Zaria a reshensu da ke GSS Kudan, a inda a nan ne ya samu takardar diploma a computer, a networking/computer engineering daga 2013/2014.
(Mun samu wannan jawabin ne daga bakin sa, wanda ya rubuta ya turo min da WhatsApp a ranar 12/02/2021 da misalin ƙarfe 7:33 na safe).
Danna nan karanta tarihin Hajiya Halima Jumare Kudan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu