Tag: Tsire

  • Yadda Ake Tsiren Nama

    Yadda Ake Tsiren Nama

    A yau za mu koyi yadda ake tsiren nama; Tsiren nama abinci ne mai matuƙar daɗi musamman ma idan aka haɗa shi yadda ya kamata, kuma aka lura da dukkanin tsabtar abubuwan amfanin zuwa kayan haɗawar.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Tsokar nama
    • Jajjagen attaruhu da albasa
    • Magi
    • Curry
    • Spices
    • Fennel seed
    • Albasa
    • Tattasai
    • Koren tattasai
    • Tumatir
    • Garin yaji
    • Tafarnuwa domin buƙata
    • Mai
    • Tsinken yin tsare
    • Bama

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sami nama me kyau gurin tsoka inda babu jijiya, sai a yayyanka shi madaidaita.
    2.  A wanke shi tas a caccaka masa wuƙa saboda Idan an yi haɗi ya ratsa cikin, a tsane ruwan. Sannan a saka fennenl seed.
    3. A jajjaga tafarnuwa Idan ana buƘata, curry, spices, garin citta, Maggi, bama, jajjagen taruhu da albasa kaɗan, da garin yaji shi ma kaɗan.
    4. Sai a jujjuya sosai har ko’ina ya ji, sai a saka a fridge na tsawon awa 1 da rabi. Sai a jiƙa tsinken yin tsire a ruwa na mintuna 30 sannan a cire.
    5.  A yayyanka albasa yankan manya, tattasai ma haka, tumatir da koren tattasai duk a yi musu yankan manya.
    6.  Sai a ɗauko tsinken a soka albasa, sannan nama, sannan Koren tattasai sannan nama sannan albasa sai tumatir, sai jan tattasai haka za a yi ta yi har a gama.
    7. Sai a kunna abin gashi, Idan ya yi zafi sai a ɗauko tsiran, a jera sannan a yaryaɗa mai a kai sai a bar shi ya gasu, a dunga juyawa akai-akai saboda kar ya ƙone.
    8.  Ana yi ana yaryaɗa mai har a gama. Za a ji yana ƙamshi.
    9. Idan aka tabbatar ya gasu, sai a cire a saka a kwano ko faranti.
    10. A ci da ɗuminsa ya fi daɗi. Za a iya saka wa a tsakiyar bread a ci. Shi ma akwai daɗi.

    Domin sanin Yadda Ake Onion Rings danna nan.

  • Yadda Ake Kebab Sabon Salo A Sauƙaƙe.

    Yadda Ake Kebab Sabon Salo A Sauƙaƙe.

    Barkan mu da  kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake kebab sabon salo a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shehu. 

    Abubuwan haɗawa
    1. Jan nama kilo
    2. Albasa 1
    3. Maggi 4
    4. Yajin barkono  cokali
    5. BBQ sauce chokali
    6. Ƙli-ƙuli (gari)
    7. Kayan ƙamshi
    8. Man gyaɗa ¾ cup
    9. Koren tattasai 2
    Yadda ake haɗawa
    1. Da farko za ki wanke namanki, ki masa yanka mai fadi ki ajiye a gefe.
    2. Sai ki haɗa yajin da man gyaɗa da garin ƙuli-ƙulinki da BBQ sauce ki sa maggi da kayan ƙamshi sai ki kwaɓa.
    3. Sai ki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya.
    4. Sai ki kawo baking tray ki sa naman, sai a saka a oven bayan minti 15 sai a duba a juya shi, sannan a ƙara yaryaɗa haɗaɗɗen mai. Kar ki sa wutar ta yi yawa.
    5. Idan ya yi, sai ki sauke, ki yanka daidai misali, ki yanka albasa da koren tattasanki sannan a mayar oven na minti 2-3 sai a sauka domin albasa da tattasai su rusuna.
    Domin koyan Yadda ake danderun nama sabon salo danna wannan koren rubutun.