Tag: Soyayyen Dankalin Hausa na musamman

  • Yadda Ake Soyayyen Dankalin Hausa Da Miyar Ƙwai

    Yadda Ake Soyayyen Dankalin Hausa Da Miyar Ƙwai

     

    Dankali na da matuƙar amfani a jikin ɗan Adam kuma ya kasance an haɗa shi da ƙwai, zai yi daɗi wajen ci, ga matuƙar amfani a jikin mutum.

    Soyayyan dankalin Hausa:

    Abubuwan da ake buƙata

    Dankalin Hausa

    Gishiri & maggi

    Citta & kanunfari

    Mai

    Yadda ake haɗawa

    A fere dankali a yanka shi dogaye ko round a wanke shi a tsame shi, a barbaɗa gishiri, a ɗora mai a kan wuta yai zafi, a yanka masa albasa, idan ta yi ja, sai a zuba dankalin, idan ya soyu, za a ga ya yi ja, in kuma farar suya ce, za a sa cokali mai yatsu a caka idan yayi baza a ji garas-garas ba, to ya soyu, sai a tsame shi a haka har a gama.

    Miyar Ƙwai

    Abubuwan da ake buƙata:

    Ƙwai(egg)
    Tomato
    Attaruhu
    Onion
    Maggi & salt
    Kanunfari & citta
    Mai

    Yadda ake haɗawa

    A yanka albasa, attaruhu, da tumatir amma ɗan kaɗan,
    A zuba mai a wuta, idan ya yi zafi, sai saka yankakkun kayan miyar nan a ciki, a soya su, sai a sa dakakkiyar citta da kanunfari a zuba,
    Sannan a fasa ƙwai a kaɗa a ƙwara a kan soyayyen kayan miyar nan, sai a juya, idan ta yi sai a sauke