Tag: Malamai

  • Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    September 12, 2024

    ƁANGARE NA II: HANYOYIN SADA ZUMUNTA

    Musamman a wannan ƙasar Najeriya hanyoyin sada zumunta sun fara ɓulla ne daga shekara ta dubu biyu (2000) lokacin da aka fara amfani da wayar hannu mai amfani da layin waya.

    Da farko wayoyin da ake amfani da su, wayoyi ne da ba sa ɗauke da manhajar hanyoyin sada zumunta, da yawan mutane a lokacin ba hanyoyin sada zumunta ne a gaban su ba, kawai abinda su ka fi yi shi ne buga waya da amsa kira.

    Za a iya ce wa mafiya wayancin waɗannan hanyoyi ba a samar da su ba, balle ma a saka su a matsayin manhaja a wayar hannu. Misali, manhajar sada zumunta na 2go wasu ɗalibai na jami`ar Witwatersrand Johannesburge, suka ƙirƙire shi a 2007.

    Brian Acton da Jan Koum su ne suka ƙirƙiri manhajar Whatsapp a shekara ta 2009, Facebook kuma Nick Clegg, Sheryl Sandberg, Sean Parker, Mark Zuckerberg suka ƙirƙira a 2004 a Massachuset ƙasar Amurka. Twitter kuma a shekarar 2006 aka ƙirƙire shi, amma sai 2012 aka ƙaddamar da shi wanda Jack Dorsey, Noah Glass, Biz Stone da Evan Williams su ka ƙirƙira.

    Twitter (2006), Tiktok( 2016), Telegram (2012). Kafinsu akwai wasu hanyoyin na wasiƙu da sada zumunci kamar su hotmail, yahoomail (1997) da gmail (2004) da sauransu amma ba a samun su a manhajar wayar hannu. Waɗancan su ne aka fi sani a nan, amma akwai dubbansu suna nan ana ta amfani da su yau a faɗin duniya.

    A nan kasar, musamman a yankin mu na Arewa, da yawa daga cikin masu amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta ba su san waɗannan manhajoji ba sai kusan shekarar 2010 yau shekara goma sha –biyar ke nan. Sannan da yawa da ga cikin mutane ba su san babban dalilin samar da waɗannan manhajojin ba, balle su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

    Matasa na cikin `yan gaba dai gaba dai wurin amfani da waɗannan manhajojin. Ƙaramin misalin da zan bayar shi ne a cikin mutane miliyan hamsin (50M) da suka yi amfani da 2go a nahiyar Afrika miliyan 13 suna Najeriya kuma sama da kashi casa`in (90%) matasa ne.

    Wannan hasashe haka yake har yau a ko ina, matasa su ne kan gaba wurin amfani da waɗannan hanyoyi musamman a ƙasashe masu tasowa. Wannan ya na faruwa ne sakamakon rashin aikin yi da zaman banza da matasa suke fama da shi a ƙasashe masu tasowa wanda ci bayan tattalin arziki ke sabbaba shi.

    A yau ana ganin samari marasa aikin yi suna yin duk abinda za su yi dan su sami kuɗin da za su sayi data dan su sami damar amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta. Misali, Facebook idan mutum ba shi da data, idan kuma ba lite yake amfani da shi ba, toh a akwai abinda ake cewa “free mode” kwai za ka ga rubutu, amma hotuna ko bidiyo ba za su bayyana ba, sannan ba zai baka damar bin hanyar da za ka sami labari ba ko wani bayani ba wato “link”.

    Sau da yawa wannan yana hana mutane fahimtar asalin abinda aka yaɗa ko aka wallafa, sannan ya kan sa mutum ya yi sharhi na goyon baya ko akasin haka, ko ma ya yaɗa abinda ba shi ne ba.

    Abu mai mahimanci na gaba shi ne, mutane suna shiga abin da ba su da ilimi a kai. Wannan shi ne dalilin yin wannan rubutun. Sau da yawa babban malami zai yi bayani na ilimi mai zurfi a kan wani abu mai mahimmanci da ya shafi addini, a yaɗa shi ta hanyoyin sada zumunta, kwatsam sai ka ga wani matashi, ko wani ɗan tasha bai san dama ko hagu ba a kan abinda ya shafi ilimin addini, kawai sai ya ce wannan babban malamin nan “ƙarya” ya keyi, ko zai ci gyaran malamin.

    Ba don komai ba, kawai wannan hanya ta ba shi dama ya ga ko ya ji abinda wannan babban malamin ya faɗa. Wani babban abin takaicin shi ne shi, wannan matashi ko ɗan tashan ba zai iya kawo wata hujja na ilimi ba, sai soki-burutsu, jahilci da hayaniya.

    Misali ɗaya daga cikin misalai masu yawa shi ne mas`alar mutum ya ce ya saki matarsa da wasa ko da kuwa a shirin wasan kwaikwayo ne. Manyan malamai kamar Dr. Bashir Aliyu Umar, oon da Prof. Umar Sani Fagge sun yi fatawa a kan ce wa duk wanda ya aikata haka matarsa ta saku.

    Suka kafa hujja da hadisin Manzon Allah SAW ingantacce. Amma aka samu wasu waɗanda ba su wani abu na ilimin addini, kai wasu ma `yan tasha ne, suka rinƙa surutai na jahilci da rashin ladabi ga malamai da malanta da ƙoƙarin ƙaryata hadisin Manzon Allah SAW da molon ka.

    Ba abinda ya ba su wannan damar sai waɗannan hanyoyi na sada zumunta wanda suke ganin ilimi kamar abin banza da arhan malanta. Idan aka duba a baya za mu ga mas`aloli na addini, malamai da tsarekunsu su suke tattauna cikin girmamawa ta hanyar rubuce – rubucen ilimi.

    Amma yanzu saboda waɗannan hanyoyin na zamani sai a ci mutuncin malami, a zage shi, a faɗi munanan maganganu game da shi, ba tare da an kawo wata hujja ko wata magana ta ilimi ba saboda ba abin da za a iya faɗa da rashin ilimi.

    Sannan abu na biyu, wannan ya ba da dama kowa ya ga cewa zai iya zama malami saboda yawan yaɗuwar ilimin kayauta kuma cikin sauƙi. Kowa zai iya zama malami dare ɗaya. Wanda kuma ba haka ba ne, kuma ba ma zai yiwu ba.

    Abu na uku, waɗannan hanyoyin sun bai wa wasu `yan dagajin mutane damar yin sojan gona, su mai da kansu malamai, su tsoma baki a cikin abinda ya shafi ilimi, da ma faɗin duk abinda suka ga dama. Jahilai kuma suna nan birjik followers, masu sharing da masu like.

    Daga ƙarshe, waɗannan hanyoyin sun ba da gudumawa wurin yaɗuwar ilimi da wayar wa mutane kai game da addini, sannan a gefe ɗaya kuma sun ba da damar raina malamai da ilimi, rashin ganin girman ilimi da mahimmancinsa. Malamai sun zama ba komai ba, sannan malanta ta zama arha.

    Duk wanda baya ganin wanɗanda suke riƙe da tushen addininsa, (ilimi) da girma ta yaya zai ga girman addininsa? Gimama malamai yana daga cikin abinda zai sa mutum ya san daraja da girman addininsa.

    Whatsapp: 08039290267

    Karanta Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Malam Imam Ahmad da sauran malaman sunan sun rawaito daga Abi Darda` (RA) ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: “Lallai Malamai magada Annabawa ne, Su Annabawa ba su bar dinari ko dirhami ba, sai dai sun bar ilimi. Wanda ya yi riƙo da shi lallai ya yi riƙo da rabo babba”

    A cikin wannan rubutun duk inda aka faɗi malami ko malamai ana nufin malamin addinin musulunci wanda aka yarda da iliminsa da kuma tsoron Allahan sa. Irin waɗannan malaman su ne magada Annabawa, saboda suna yaɗa shiriya ga mutane (Wanda aiki ne annabawa). Ko kuma don su (malamai) suna ɗauke da wani abu (ilimi) wanda yake daga wurin Allah wanda aka samu ta hanyar Annabawa. Duk ɓangare biyun sun cancanci girmamawa.

    Malanta wata hanya ce da ta ƙunshi kyautata niyya, tsoron Allah, gwagwarmaya, haƙuri, jajircewa, ladabi da girmama wanda ake neman ilimi wurinsa, dan neman sanin abinda ya shafi addini, wanda ya ke ɗaukan lokaci mai tsawo. Duk mai neman ilimi yana ba da lokacinsa ne gaba ɗaya, ya lizimci malami, ya jajirce, tare da yi wa malami ladabi, da haƙuri ga duk abinda zai iya bijirowa ta ɓangaren malamin ko ta ɓangaren karatun ko yau da gobe.

    Duk wanda ya bi wannan hanyar, bayan wani lokaci ana sa ran ya sami wani abu na ilimi, har ma ya amsa sunan malami. Sanin kowa ne shi ilimi ba a daina nemansa kuma ba a iya ƙure samunsa. Sai dai mutum ya yi iya yinsa kawai. Sannan ba kawai don mutum ya sami ilimi shi ke nan ba, sai an cigaba da bincike, karatu da nazarce nazarce.

    A ƙarni na Sha-shida (16) a Arewacin ƙasar nan, Jami`ar Gobarau da kuma `yandoto ta Katsina sun zamo wurare da suka tara masana a kowani fanni na ilimi wanda manyan malamai daga duk faɗin nahiyar Afrika da ma wasu wuraren suke zuwa dan neman ilimi da ilimantarwa.

    Bayan jihadin Babban Malami, Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, cikin jama`ar Shehun malamin, manyan malamai irin su ƙaninsa, Abdullahi Ibn Muhammad Ibn Fodiyo (Abdullahin Gwandu), Malam Mustapha (Ɗan Tafa), Waziri Ɗan Laima da kuma irinsu ɗan Shehu Usman bin Fodiyo wato Muhammad Bello da ƙanwarsa Nana Asma`u da ɗanta Abdulkadir Ɗan Tafa da sauran manyan malamai sun yi ta ba da gudunmawa wurin karantar da mutane, rubuce rubucen littatafi da ƙasidu na ilimin addini, lugga da sauransu.

    Duk lokacin da aka sami tarin malamai a wuri, ko a lokaci ɗaya, sau da yawa akan sami wata mas`ala ta addini wadda za a iya samun saɓani a tsakanin malamai. Wannan yana faruwa ne sakamakon yawan bincike a kan mas`aloli na addidni daban daban da malamai su ke yi. Sabani ba wani abu ba ne da zai sa a ta-da jijiyar wuya ko a ɗau makami, tun da su masu ilimi ne, toh a ilmance ake komai ta hanyar rubuce rubucen ƙasidu, littattafai da wasiku da fitar da fatawa.

    MISALAI GUDA UKU KAƊAI DAGA MAGABATA.

    Misali na farko shi ne: Lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo yankin Arewa, Sarakunan mu na musulunci sun ƙi miƙa wuya, kamar yadda turawan suka nema. Da yawa sun zaɓi su yaƙi waɗannan turawan.

    Sarkin Muslumi Attahiru I da sanyin safiyar ranar 15 Maris 1903 bayan an gwabza tsakanin jama`arsa da turawa na kimanin sa`o`i biyu, sai ya fahimci yaƙi da turawan nan babu nasara, saboda a ƙalla an kashe mutane kusan 100 cikin mutanen sa, a ɓangaren turawa ko mutum guda ba a kashe ba, saboda bindigogi na zamani da suke amfani da su a wancan lokacin.

    Ganin haka, ya yanke shawarar yin hijira zuwa gabas, bayan ya yi shawara da wasu daga cikin muƙarrabansa. A ranar 27 Yuli, 1903 aka yi yaƙin ƙarshe a wani gari da ake kira Burmi ranar Juma`a Sarkin Musulmi Attahiru I da kusan mutane 600 suka yi shahada a cikin masallacin juma`a. Wannan jajircewa da Sarkin musulmi da yayi, ɗaya daga cikin sojojin taurawan Ingila William Wallace ya tabbatar da haka.

    Ba tarihin Sarkin Musulmi Attahiru I zan bayar ba, amma ana cikin wannan taƙaddama bayan fitar Sarkin musumi daga birnin Sakkwato ranar 21 Maris, 1903 aka zaɓi Muhammad Ibn Ali Ibn Bello (Attahiru II) a matsayin sarkin Musulmi. A wannan lokacin Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya nemi fatawa a wurin Alkalin Gwandu Ahmad Bin Sa`id kan maslaha ga musulmi; A miƙa wuya wa turawa, ko a ci gaba da yaƙarsu ko a yi hijira? Wanda wasu suna ganin ba bu wata maslaha da ta wuce a miƙa wuya wa turawa kawai.

    Wannan fatawa ta a miƙa wuya ta samu karɓuwa sosai musamman dalilin takardar da Wazirin Sokoto Muhammadu Buhari ya yi “Risalatil Wazir Ila Ahlil Ilmi Wat Tadabbur” ta yadda suka yi amfani da ilimin usul wurin bayanin hukuncin abinda ya kamata shugabannin musulmi su yi na miƙa wuya da yarda da turawan mulkin mallaka. Akwai waɗanda suka saɓa musu a ra`ayi suma da hujjojinsu, amma cikin rubuce rubuce na ilimi kowa ya fito da hujjarsa, ba hayaniya ko zage –zage da cin mutunci.

    Misali na biyu: Shi ne Lokacin da aka sami taƙaddama kan saka karatun Qur`ani a gidan rediyo a 1955 zuwa 1960 wanda Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawar ya halatta a sa karatun Qur`ani a gidan rediyo, shi kuma Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da fatawa sɓanin haka.

    Dukkansu (Sheikh Ibrahim Nyass da Sarkin Zazzau Malam Jafaru Dan Isyaku) kowa ya yi amfani da ilimi mai zurfi na Usulul Fiqh da hujjoji masu ƙarfi wurin bayanin hukuncin wannan mas`ala. Sheikh Ibrahim Nyass ya ba da fatawarsa ne sakamakon tambaya da wasu daga cikin malaman Kano suka yi masa. Sarkin Zazzau Malam Jafaru Ɗan Isyaku ya ba da nasa fatawar ne sakamakon tambayar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi I ya tura masa duk da cewa shi ma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sasusi I babban malami ne.

    Abin sha`awa a nan shi ne Shiekh Ibrahim Nyass har wani littafi ya yi wanda aka buga shi a shekaran 1956 a ƙasar Masar mai suna “Alhujja albaligha fi kawn Idha`at alQur`an fir radiyo Sa`igha”. Wannan mas`alar ita ma haka aka ƙarƙareta ta hanyar ilimi ba hayaniya da harigido.

    Misali na uku, a ƙarni na 19, an sami taƙaddama a kan Sadalu da Qabalu a sallah, wannan taƙaddama ta samo asali ne saboda bayyana da yaɗuwar tajdidin ɗarikar Tijjaniya da Sheikh Ibrahim Nyass ya kawo wanda kafin zuwan wannan tajdidi, ɗarikar Ƙadiriyya ita ce aka fi sani kuma ta fi daɗewa a ƙasar Hausa tun bayan jihadi.

    Malaman ɗarikar Kadiriyya sun tafi a kan sadalu cikin sallah. Sheikh Ibrahim Nyass da wasu malamai a Kano suka zo suka warware wancan fahimta ta sadalu da hujjoji. Wannan ya sa `yan Kadiriyya suke ganin `yan Tijjaniya sun zo da wani sabon abu har aka riƙa kiran `yan Tijjaniya masu bin wannan fatawar da “`Yan Ƙabalu”

    Shehunan malamai irin su Malam Muhammadu Salga (r. 1938), Malam Tijjani Usman Zagon Barebari (r.1970), Malam Shehu Maihula (r1988) da sauransu sun yi rubuce rubuce dan tabbatar da ingancin yin ƙabalu a sallah. A ɗayan ɓangaren na Qadiriyya wanda Malam Nasiru Kabara ya ke jagoranta sun yi na su rubuce rubuce kan ingancin yin sadalu a sallah.

    A nan ma wani abin sha`awa, shi ne duk rubuce rubuce na ilimi aka rinƙa yi, har yau waɗannan rubuce-rubuce suna nan. An sami irin wannan taƙaddama ta faru a sokoto har Malam Abubakar Atiku Gwandu (r. 1913) ya rubuta wani littafi mai Irshad al-ikhwan ila bayan hukm as-salat bis-sadlu wa al-kablu.

    A kwai misalai masu yawa kan taƙaddama ko saɓani da ake samu tsakanin malamai tun tuni, amma abin zai birge ka idan ka kalli hanyar da ake bi wurin bayyana ra`ayi da hujjoji da fito da komai fili, hanya ce ta rubuce rubuce na ilimi, ba soki burutsu da hauragiya da shirme ba. Kuma malamai su suke kayansu ba kowani kare da doki ba. Hargowa da hayaniya da shiga fagen ilimi daga ko wani kare da doki ya samu asali ne dalilin yaɗuwar hanyoyin sada zumunta.

    Wanda shi ne za mu tattauna a rubutu na gaba.

    Rabiu Musa Adam

    Whatsapp: 08039290267

    September 12, 2025

    Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Edita@rumasau-kallamu