Tag: Ka San Kanka

  • Kammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka

    Kammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka

    Warwara

    Duk da na bayyana muhimmancin mutum ya gano kansa, zan iya cewa ba dole sai ka yi hakan ba. Gano kai wani aiki ne babba mai matuƙar wahala, da in ba ka yi sa’a ba zullumin da za ka shiga a ƙoƙarin gano kanka zai iya lahanta maka ma rayuwa, ya hana ka jin daɗinta.

    Kamar yadda na fara ba da labari a farko, na daɗe ina son gane ni wane ne, kafin na gano kai na har ciwon damuwa sai da na yi, na ma fara karɓar magani a asibiti na ga abun ba mai ƙarewa ba ne na watsar, amma ban karaya ba, na ci gaba da tambayar kai na da kuma ƙoƙarin nemo amsoshin tambayoyin.

    Ba zan ce iya ƙoƙarin gano kai na ne ya sa ni a damuwa ba, abubuwa ne da yawa suka haɗu, amma dole ko dai rashin sanin ni wane ne ya taimaka, ko kuma son gano ni wane ne ya ƙara ingiza abun. In kana ganin ba lallai ka iya jure wahalar da take cikin aikin gano kanka ba, ba kuma za ka iya rayuwa cikin haɗarin rashin sanin kanka ba, to ina ganin abu ɗaya za ka yi.

    Ka bi wanda yafi ka sanin kanka sau da ƙafa. Duk abin da kake son sani ya turo an sanar da kai, duk abin da kake son aikatawa ya turo an koya maka. Na san za ka fahimci inda na dosa, ina nufin ka zama mutumin kirki mai biyayya wa Allah da manzonsa (tsira da aminci su tabbata gare shi) domin in dai ka tsaya kan hanyar da suka ɗauraka a kai, dole za ka amfanu kuma za ka amfanar, za a ƙaru da zuwanka duniya, kuma duk abubuwan da na lissafa a baya za su dinga zuwa maka a ɗabi’ance (naturally) ba tare da wani hoɓɓasa ba, kamar dai abin da ake cewa “autopilot”.

    Idan ka yi wannan ka hutasar da kanka yawan tunani. Duk da cewa ita ma fa wannan hanyar ba sauƙi ne da ita ba, domin kana buƙatar ilimi da kuma aiki da ilimin, ilimi na gaske ba na wasa ba, aiki na gaske ba na wasa ba. Sai ka san ibada da mu’amala da haƙƙoƙin mutane a kanka da haƙƙoƙinka a kansu, da dabarun zaman lafiya da mutane, da yadda rayuwarka a cikinsu za ta amfane su kamar yadda ta magabata ta ke amfanarmu.

    A iya ilimina (wanda ɗan kaɗan ne) ban san wani mutum da ya yi wata bajinta ba a duniya da bai zo wata gaɓa da ya san kansa ba. Kowa in za ka saurare shi, ko za ka karanta littafi ko rubutunsa ko tarihinsa za ka fahimci cewa daga cikin sa’ar da ya yi a rayuwa akwai gane shi wane ne da ya yi da wuri.

    Don haka ko wanda ya zaɓi yin rayuwarsa kan tsari mai kyau zai zo gaɓar da zai san kansa, ko kuma ya dinga rayuwa kamar ta wanda ya riga da ya san kansa ko mai daren daɗewa. Akwai wani hadisi da sahabbai suke tambayar Annabin Allah mai tsira da aminci kan cewa tunda Allah ya riga da ya ƙaddara ƴan wuta da ƴan aljanna, ai ba buƙatar kowa ya yi komai, sai ya jira ƙaddararsa, sai ya ba su amsa da cewa “ku yi aiki, kowa za a sauƙaƙe masa abin da aka halicce shi don shi”.

    Wannan yana nuna mana cewa ba a taɓa kafa hujja da ƙaddara, ko a zauna ana jiran rayuwa ta faru, manufar halittar shi ne ka rayu, ba ka zauna jiran rayuwar tana wucewa ba (waɗanda suka mutu a wurin kare addini Allah yace kar mu ɗauka a mace suke, a raye suke, wataƙila saboda sun mutu a kan manufa da bin tafarki, Allah ne mafi sani).

    Don haka in ba za ka iya sanin kanka ba, to ka bi Allah ka huta, in za ka iya sanin kanka kuma ka samu riba biyu kenan, ka san kanka, kuma kana bin Allah a yadda kake don haka komai zai dinga zuwa maka a sauƙaƙe. Manufar rubuta wannan ɗan ƙaramin littafin shi ne karkato da hankalinmu kan yin rayuwa da manufa da tsari, ba kara zube ba.

    In muna kara zube yanzu muka fara ganin cin kowanne irin kashi, ba za mu taɓa kwarjini ba, balle mu cimma wani abu, mu da ƙorafe-ƙorafe da ganin laifin juna mun ɗaura kenan har illa masha Allahu. In ka samu wannan littafin kada ka karanta shi ka ajiye shi, ka yi ƙoƙarin yin aiki da wasu abubuwan da ka ga za su iya dacewa da taka rayuwar.

    Sani ba aiki ba ya canja komai, bambancinsa da rashin sani kaɗan ne. Allah na ke
    roƙo ya ba mu dacewa duniya da lahira ya kuma azurta mu da kyakkyawan ƙarshe.
    Kada a manta da yaɗa wannan saƙon dan amfanar ƴan’uwa gaba ɗaya, musamman matasa ƴan’uwana da ke ta faɗi tashin ganin sun gano kan rayuwa.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Yadda Manufar Rayuwarka Take

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ya Ake Sanin Kai?

    Ya Ake Sanin Kai?

    Kamar yadda na sha faɗa a rubuce-rubuce na, mutum haɗin gambiza ne na ƙwayar halittarsa, tarbiyyar da ya samu daga gida, iliminsa, abokanansa, wurin da ya tashi da gogewarsa a rayuwa.

    Su waɗannan abubuwan su suke sa wa mutum ƙauna ko ƙin wani abu, su suke taimakawa mutum wajen yanke shawara, su suke taimakon mutum kan zaɓinsa da ayyukansa, su suke haskawa mutum abubuwan da zai iya yi cikin sauƙi da waɗanda sai ya wahala.

    Wanda yake son ya san kansa yana da kyau ya fara daga ƙwayar halittarsa, domin ita take zuwa da duk wasu halayensa da ya gada a wurin iyayensa da kakanninsa. Don haka ni ma zan fara da shi, ina mai cirowa daga litattafan masana a wannan fanin.

    ❖ Ka San Yanayinka Na Halitta

    Shi yanayin mutum shi ne halayen da aka haife shi da su, waɗanda ya gada daga iyaye da kakanninsa. Kafin ya shiga duniya ya koyi wasu dabarun. Tim Lahaye (marubucin littafin why you act the way you do) ya kasafta mutane zuwa gida huɗu (4).

    Bibbiyu, biyun farko su ne mutane masu surutu da hayaniya (extroverts) sauran biyun kuma su ne shiru-shiru waɗanda ba su cika shiga mutane ba (introverts). Zan kawo dukkanin kashi huɗun haɗi da rauni da ƙarfin kowanne, ina mai cirowa daga wannan littafin.

    SANGUINE

    A ɓangaren masu surutu akwai waɗanda ake kira “Sanguine”, waɗannan su ne irin mutane masu yoyon magana ɗin nan, ba sa iya riƙe bakinsu, duk inda suka shiga dole sai an san suna wurin, akwai su da haba-haba da mutane, ga su kuma ba wuyar sabo, ga saurin ƙulla abota. Ba su san jimami ba, kuma komai suna iya mayar da shi raha, sun yarda da tatsuniyar dawwama cikin farin ciki a rayuwa.

    Ƙarfinsu: suna da saurin sabo, sun iya ba da labari, ba sa gajiya da surutu, suna rayuwa a yanzu (tuna baya ba ya damunsu balle fargabar gaba), suna da nuna tausayawa da alhini kan abu marar daɗi na wani, suna nuna shauƙi kan komai, ga su da raha da kuma shiga cikin ayyukan sa kai dumu-dumu, saurin ƙulla abota, da fara magana in kun haɗu.

    Rauninsu: ba sa iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, in ka ba su aiki da wuya ka ga sakamako yadda ya kamata, yanayinsu yana saurin canjawa daga walwala zuwa tausayawa, in ka shiga wani hali sai sun fi ka nuna jimami don haka ma ana iya zargin ko na ƙarya ne in ba a fahimce su da kyau ba, ba su da tsari, sun fi sauran nau’in mutanen girman kai, kuma cikin sauƙi suke samun kansu cikin yaudara, ƙarya da cutar mutane don su ɓoye rauninsu, sannan suna da ƙarawa komai gishiri (kambaba abubuwa).

    CHOLERIC

    Nau’i na biyu cikin masu surutu su ne “Choleric”, shi choleric bai kai Sanguine surutu ba, shi ma yana da saurin sabo da jama’a, shi ma’aikaci ne, yana da zummar cimmawa ko azama, yana zama jagora, yanke abin da zai yi ba ya masa wahala, haka ma yanke wa waninsa, yana wadatuwa da kansa, yana da buruka kuma yana tsara yadda zai cimma su.

    Ƙarfinsa: ƙarfin gwiwa, wadatuwa da kai, hangen nesa, duk abin da ya sa a gaba ana ganin ci gaba (progress), yanke shawara ba ya ba shi wahala, jagora ne, akwai shi da naci, ba ya jira, in ma ba ku yi ba zai yi da kansa.

    Rauninsa: ba ya nuna ƙawa zuci/motsin rai (emotion) dan haka bai cika nuna tausayi ba, yana ganin komai zai iya yi da kansa ko ba taimako, yana danne na ƙasa da shi da musu kama-karya, ya iya ƙeta, bai cika yafiya ba, yana da saurin fusata dan haka ma yake yawan faɗa da mutane, kuma ya iya cin fuska da baƙar magana, tunzura mutum ma yakan iya sa shi nishaɗi.

    MELONCHOLY

    Nau’i na gaba wanda shi ne na farko cikin mutane shiru-shiru shi ne meloncholy, waɗannan su ne irin mutane ma su basira ɗin nan, wanda kowa yake mamakin baiwarsu, akwai su da lissafi, sadaukar da kai, da son ganin komai ya cika ɗari bisa ɗari 100%. Ba su da saurin ƙulla abota amma in suka ƙulla abota da kai ba za su ci amanarka ba, yanayinsu yana saurin canzawa dan haka sun fi duk sauran saurin shiga damuwa.

    Duk da ba su da surutu amma in suka samu wuri za ka rantse ba su ba ne (ko da kuwa a gaban kyamara ne ko wurin wani taro). Akwai su da tattali da rowa, in an ɓata musu
    rai suna da fushi amma ba kamar choleric ba, su a zuci za su cigaba da tafarfasa dan haka suna iya ɗaukar fansa ma.

    Ƙarfinsu: ‘ƴan baiwa ne, akwai su da basira, suna da lissafi, suna son ƙyaleƙyale, suna iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, suna da zurfin tunani da tsari, ba su cika son hayaniya ba, kaɗaici yana ba su damar zurfafa tunani, ba su cika yin raha ba saboda komai gaske ne a wurinsu(da muhimmanci suke ɗaukarsa), suna da baiwar ƙirƙira da bincike, duk aikin da suka sa a gaba sai sun ga ƙarshensa, sun fi sadaukar da kansu kan abin da mutane za su amfana ko da su suna cutuwa.

    Rauninsu: saboda zurfin tunaninsu cikas suke fara hangowa game da komai da za su yi, caccanzawar yanayinsu ya sa suna saurin shiga da kuma daɗewa a damuwa, saboda suna son yin komai ɗari bisa ɗari (100%) ya sa ba a cika burge su ba, su da kansu ma suna barin ayyukan da suka ga ba za su cika yadda suke so ba, ba sa shiga mutane, suna kallon rayuwa a yadda ya kamata a rayu ba a yadda take a zahiri ba, basirarsu ta sa suna da saurin zargi da munanan tunani kan abubuwa, suna da saurin kushe abu
    tare da caccakar abin da bai kai mizani ba a ma’auninsu.

    PLEGMATIC

    Kaso na ƙarshe su ne plegmatic, su waɗannan shiru-shirunsu har ya fi na meloncholy domin ba wani shauƙi da za su samu kan su a ciki da zai sa su zama ma su surutu. Da wuya ka ga sun yi fushi ko an ɓata musu rai, suna da mugun sauƙin kai don haka sun fi sauran daɗin zama, suna da kakaci amma ba su cika dariya ba ko da sun yi kakacin, ba sa wuce iya abin da aka sa su, ba su cika son ɗaukar nauyin komai ba, sun fi jiran rayuwa ta zo ta same su.

    Ƙarfinsu: nutsuwa da rashin hayaniya, suna da sauƙin kai da daɗin sha’ani, za ka iya dogara da su, sun iya sasanta mutane, suna da tsari, akwai su da kakaci, suna kallon rayuwa a zahiri, ba sa yin abu ba tare da tunani da kuma kyakkyawan tsari ba, ba sa fara aiki da kansu amma in dai an sa su sai sun kammala shi, suna da son tsafta, ba su cika shiga sha’anin mulki ba, amma duk lokacin da aka zaƙulo su aka ba su mulki, suna yin mulki da ƙwarewa ta ban mamaki.

    Rauninsu: ba sa iya zaburar da kansu, suna da ganda, suna da son kansu, akwai su da rowa da tsoro, suna da yawan damuwa da zullumi kan abubuwa (gujewa ɗaukar nauyi yana farautarsu), ba sa iya saurin yanke mai za su yi balle su yanke wa wani, kullum cikin ƙoƙarin kare kansu suke daga cutuwa ko asara dan haka da wuya su ɗauki kasada, suna da turjiya da tawaye, za ka iya musu bayanin mai kake son su maka, su yi kamar sun yarda amma da sun juya baya su yi a yadda suke so.

    Tim Lahaye bai tsaya a iya kasa mutane gida huɗu ba, ya ƙara bayani da cewa kowanne mutum haɗin gambiza ne na kashi biyu cikin huɗun, kowa ya haɗa ɓangare biyu amma ɓangare ɗaya yana iya fin rinjaye, akan samu ma su haɗa uku amma su suka fi ƙaranci, dan haka yace mutane za su iya kasuwa gida goma sha biyu (12).

    A taƙaice dai kai tsaye mutum ba zai iya gane wanne yafi rinjaye a tattare da shi ba, amma daga bayanan da suka gabata zai fuskanci inda ya fi karkata in ya zauna ya nazarci rayuwarsa. Abu na gaba da zan ƙara shi ne, su waɗannan ɗabi’u na halitta koyaushe suna tare da mutum har ƙarshen rayuwarsa domin gadonsu ya yi, amma
    iliminsa, tarbiyyarsa, imaninsa da aƙidunsa su suke mayar da shi mutum.

    Dan haka yana daga cikin amfanin gane ƙarfi da rauni na halitta mutum zai san ina zai karkata a rayuwa, sannan zai san waɗanne halayya ne zai zama a ankare da su dan kar su dinga ɓata masa hulɗa da jama’a. Misali, sanguine dole ya yi aiki a kan rashin iya sauraren mutane, ya koyi kama bakinsa ya ji suma me za su ce, choleric dole ya koyi dena yin ƙarfaƙarfa da danne na ƙasa da shi, saboda wannan zai sa su daina ganinsa da
    ƙima.

    Meloncholy dole ya koyawa kansa kyakkyawan tunani kan abubuwa, in ba haka ba basirar ta sa ba za ta masa amfani ba, phlegmatic sai ya koyi zaburar da kansa ko zama wurin da za a dinga yawan zaburar da shi in ba haka ba zai tsinana komai ba a rayuwarsa. Wannan raba mutane da Tim Lahaye ya yi ba lallai ya zama cif-da cif ɗari
    bisa ɗari (100%) ba amma a cikin duk rabe-raben da ake yi ana ganin cewa wannan na san ya fi tattara kowa da kowa.

    Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi ya ce “ Allah ya halicci Annabi Adamu daga wata damƙa da ya yi daga ƙasa (a wurare mabambanta), don haka ‘ƴan’adam an halicce su a gwargwadon haɗe-haɗen ƙasar. Sai ya zamto a cikin mutane akwai ja, akwai fari, akwai baƙi akwai kuma tsaka-tsakin dukkaninsu, akwai mai kyan hali, akwai mai munin hali, akwai mai sauƙin lamari, akwai mai wahalar sha’ani” (Abu dawud da Tirmizi, kuma sun ce hadisi ne kyakkayawa).

    Akwai wani jan hankali, ko da ka ga halin wani da ka sani kada ka yi gangancin faɗa masa ko da kuwa abokinka ne, domin in ya ga raunin irin wannan mutumin ba zai yafe maka, kuma da wahala ka iya gamsar da shi cewa ba iya bayanin ba kenan, dan haka gara ka bar shi ya gano da kansa in yana da buƙata, sai a kula.

    ❖ Ta Ya Zan Gano Kaina Daga Wannan Rabe-raben?

    Kusan komai da muke yi ya dogara ne da irin tunanin da muke yi, shi kuma tunani ba komai ba ne face tambaya da amsa, tambaya ce kake yi wa kanka a zuci kuma kake amsa ta da kanka a matsayin tunani, don haka yana da kyau ka dinga yi wa kanka tambayoyi ma su kyau.

    Da farko abin da za ka fara tambayar kanka shi ne, ina cikin ma su surutu ko ba na ciki? Idan ka san kana da yawan zuba a ko ina to kana cikin ma su surutu kenan dan haka za ka zama kana tsakanin Sanguine da Chloric. Daga nan sai ka sake tambayar kanka wanne irin surutu ne da ni? Ina hana sauran mutane magana saboda surutuna ko kuwa ina ɗan sararawa su ma su yi? Ina da tausayi in ana ba da labari ko wani ya shiga wani hali ko kuwa ba ruwa na? ina da son girma da nuna iko ko kuwa?

    Idan amsarka ta zama e a tambayoyi biyun farko, ta zama a a, a tambaya ta uku akwai yiwuwar ka zama sanguine, saɓanin haka kuma choleric. Idan dukka e ne ko dukka a a kuma wataƙila kai gamayyar biyun ne. Idan kuwa ɓangaren shiru-shiru kake za ka iya farawa da tambayar kanka ko kana son komai ya zama ɗari-bisa-ɗari? Ka iya lissafi? Kana da zurfin ciki da kawaici? Kana nuna halin ko in kula a kan komai?

    Tambayoyi biyun farko ɗabi’un Melancholy ne, biyun ƙarshe na Phlegmatic, idan e ne amsarka a kashin farko a a a kashi na biyu ka zama Melancholy kenan, saɓanin haka kuwa Phlegmatic. A lura, kamar yadda na faɗa a baya, za ka iya samu amsoshinka duk su zama e ko duk a a, wannan alama ce da ke nuna duk ka haɗa bangarori biyun.

    Ta yiwu kuma ka ga wasu halayenka sun faɗo a gidan ma su surutu, wasu kuma a gidan marasa surutu, in haka ta faru sai ka sake duba sauran abubuwan da suka gabata a bayanin rauni da ƙarfi dan ka ga inda kafi karkata. Bayan ka gano gidan da ka faɗa a wannan kashe-kashen sai kuma ka amsa waɗannan tambayoyin da za su zo a babi na gaba.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Karanta Amfanin Sanin Kai

    Edita@rumasau-kallamu

  • Amfanin Sanin Kai

    Amfanin Sanin Kai

    Kafin na yi nisa cikin wannan littafin, yana da kyau na fara kawo kaɗan daga cikin amfanin sanin kai ga kowanne mutum da yake da mafarkin rayuwa mai kyau.

    ❖ Sai Ka San Kanka Za Ka Ci Gaba

    Babu wanda ya zo duniya da sani, kowa a gidan duniya ya san duk abin da ya sani. Haka nan babu wani da yake samun ci gaba sai ya ci gaba da neman sani, duk wanda ya tsaya da neman sani daga nan rayuwarsa take ƙarewa.

    Za ka yi mamaki idan na ce da kai ‘ƴan gargajiyar da muke gani a yanzu masu ilimi ne a zamaninsu, sun ƙi yarda su karɓi ilimin sabon zamanin da suke ciki ne ya sa ake musu kallon ‘ƴan gargajiya. Haka duk wanda ya ƙi ci gaba da neman ilimi zai zama a zamanin gaba.

    Mene ne alaƙar ci gaba da sanin kai? Sai ka san kai wane ne da matakan da ka taka na ilimi kafin ka san inda za ka ɗaura. Wanda ya san bai iya turanci ba misali, ba zai yi karambanin karanta littafin turanci mai wahala ba, in kuwa zai karanta da wuya ya tsinci wani abu. Inda iliminka ya tsaya daga nan za ka ɗaura in ka san kanka, in ba ka san kanka ba kuwa za ka iya kamawa daga ko ina sai abu ya yi nisa ka ga ashe akwai wani giɓi a baya da ka baro.

    Sanin kai wane ne zai haska maka wuraren da kake da rauni, da wuraren da
    Allah ya maka baiwa, hakan zai taimake ka ka mayar da hankali wajen inganta baiwarka sama da ƙorafi a kan gazawarka. Wanda ya mayar da hankali kan inda baiwarsa take shi ne rayuwarsa take ci gaba ba wanda yake ta faɗi-tashi da rauninsa ba.

    Hakan kuwa ba lallai ya zo da mamaki ba saboda ƙa’idar ita ce: duk abin da aka mayar da hankali kansa shi ne yake ƙara girma da haɓaka.

    ❖ Za Ka Dena Haɗa Kanka Da Wasu

    Muna rayuwa a wani zamani da bayanai suka yawaita, abubuwan da muke karantawa, kallo da saurare ba ƙaramin tasiri suke mana ba a rayuwa, don haka muke shafe shekaru ma su tsawo a rayuwarmu muna kamanta kanmu da wasu, muna ganin cewa mu ma ya kamata mu yi rayuwa irin yadda suke yi, har ma mukan shiga damuwa a dalilin hakan.

    Wanda ya san kansa ba zai tsaya damuwa da kwatanta rayuwarsa da ta kowa ba, ya san me yake so, ya san ina zai je, ya san kuma hanyar da zai kama domin isa wurin, to yaushe zai tsaya tunanin wane ba haka yake rayuwa ba? Sanin kaina ya taimaka min sosai wurin rayuwa irin wacce ta dace da ni, zan ga mutane suna yin abubuwa, amma saboda abubuwan ba su shalle ni ba, ba na fatan na zama su, ina so ni dai kawai na fi yadda na ke a jiya.

    ❖ Za Ka So Kanka

    Son kai yana daga cikin abubuwa mafiya wahala a wannan zamanin, mutum ya ji yana ƙaunar kansa a yadda yake ba tare da jin haushin gazawarsa ba. Yana daga cikin dalilin da ya sa malaman tarbiyya suke ba wa iyaye shawarar su dinga nuna wa yaransu ƙauna, yaba musu in sun yi abin kirki, yaba musu a cikin mutane in sun yi bajinta, ba su ƙwarin gwiwa, rashin gwale su ko disga su, neman shawararsu da ba su dama su yi wasu
    abubuwan da kansu (Dr. Aisha Hamdan: Nurturing Eeman in children).

    Wanda ba ya son kansa ba zai taɓa tsinana komai ba, zai cika kansa da tunanin gazawarsa da rauninsa dan haka sai wannan ya zama masa matsala. Wanda ya san kansa ya san wuraren da Allah ya fifita shi a kan sauran mutane dan haka zai gode masa kuma zai cigaba da aiki tuƙuru a wannan fannin. Haka nan kuma zai san wuraren da yake da rauni, don haka zai dinga taka-tsantsan a wannan ɓangaren.

    ❖ Za Ka San Abokanka

    Zaɓar aboki wani ɓangare ne mai wahala a rayuwa musamman ga mutane shiru-shiru irina, ba mu da saurin ƙulla abota. Amma duk da haka duk lokacin da muka san kanmu muna samun sauƙi wurin zaɓen aboki. Aboki wani jigo ne na rayuwa, ana tasirantuwa da shi matuƙa, dan haka ake so mutum ya yi taka-tsantsan wurin zaɓar abokai.

    Misali, a sanin da na yi wa kaina tunani ya fi aikina yawa, zan daɗe ina tunanin abu har sai na gano ba zai yiwu ba sai na watsar tun kafin na fara, da na ƙulla abota da Mallam
    Bahaushe wanda shi kuma yana aikin yana tunanin a lokaci guda, sai ya zama na tasirantu da shi na koyi haɗa dukka biyun ni ma daga gare shi.

    Wataƙila da ba mu ƙulla abota ba da wannan littafin ma yana nan zaune cikin tunanina har yanzu. Sanin kanka da sanin manufarka zai sauƙaƙa maka wannan ɓangaren na
    rayuwarka, za ka yi abota da wacce ta ku ta zo ɗaya, za ka yi haɗaka da wanda za ku ƙarfafi raunin juna, za kuma ka ci gaba da mutunci da sauran mutane, domin ƙa’idar dama ita ce “ba a ce sai kowa ya zama abokinka ba, amma za ka iya yin mutunci da kowa”.

    ❖ Za Ka Koyi Yi Wa Mutane Uzuri

    Wanda ya san kansa yana saurin sanin cewa mutane kowa da yanayin halittarsa, yadda yake ba haka kowa yake ba, kuma yana lura ya gane ya mutane suke, hakan yana taimakonsa wajen yi musu uzuri.

    Kafin na samu haske kan ni wanene wannan yana daga cikin ɓangaren da ya fi wahalar da ni, sai in kasa gane me yasa mutane suke abu iri kaza, ko meyasa suke son su ga ina yin abu iri kaza, ko meyasa su ba sa lura da kaza da kaza.

    Wannan Ilimin yana daga cikin abubuwan da suka ɗaga darajar Ma’aiki mai tsira da aminci kan sauran shuwagabannin duniya. In kana bibiyar tarihinsa za ka ga yana bambance sahabbansa ko wurin sanya su aiki yana mai la’akari da yadda suke. In ana buƙatar zafi ba ya neman sayyadina Abubakar, sayyadina Umar yake nema, haka nan in ana buƙatar wata maslaha ko wani abu na sauƙin kai, ba ya neman sayyadina Umar sai dai ya nemi sayyadina Abubakar. A rubuce-rubucena na “Iya ruwa…” na kawo
    makamancin wannan misalin.

    ❖ Za Ka Ɗauki Alhakin Rayuwarka

    Sanin kai yana ragewa mutum yawan ƙorafi da ɗaurawa wasu lefin matsalarsa. Wanda ya san kansa zai gwammaci ya mayar da hankali kan abin da zai amfani rayuwarsa sama da ba wa kansa hanzari ba gaira ba dalili. Kai ne ya kamata ka zama a kujerar mai tuƙi a motar rayuwarka ba a kujerar mai zaman banza ba (Sean Covey: 7 habits of highly effective teens).

    ❖ Rayuwarka Za Ta Yi Sauƙi

    In ka san kanka komai zai zo maka da sauƙi. Misalin wanda ya san kansa kamar misalin me yin bulaguro ne, ya san inda za shi, ya san a ina zai samu mota, ya san wacce hanya za a bi. Idan ka san kanka komai za ka san irin na ka, tun daga kan abinci, tufafi, abun hawa, wasa, kai hatta kallo da zuwa wuraren nishaɗi, za ka je ko aikata abin da bai ci karo da kai waye ba ne, balle ka samu ƙunci.

    Za ka rage damuwa da kallon da mutane za su maka don kai ka san abin da ba su sani
    ba game da kanka (kamar yadda na yi tsokaci a baya, akwai lokacin da dole sai ka saje da su don maslaha).

    Kana buƙatar wani cikin waɗannan abubuwan a rayuwarka? In amsarka e ce to mu je zuwa, in kuwa ta zamto a a, ina mai ba ka haƙuri wannan littafin ba na ka ba ne.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Ka Ɗauka Ka Sani

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ka Ɗauka Ka Sani

    Ka Ɗauka Ka Sani

    Gabatarwa

    Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai.
    Abin da za ka karanta mai yiwuwa ya iya canja maka rayuwa, yana da kyau ka samu wurin da babu kowa ka nutsu, ka kashe tv, ka kashe data, domin karanta wannan ɗan littafin a cikin cikakkiyar nutsuwa.

    Ba haka kawai na faɗa ba, ni ganau ne ba jiyau ba, na sha fama da abubuwa da dama a rayuwa, ga shi dai babu abin da na nema na rasa a gida, amma kullum ina ganin rayuwata tana shan bamban da ta sauran jama’a.

    Na daɗe ina yi wa kai na tambayoyi game da rayuwa, wasu daga cikin irin tambayoyin sun haɗa da:

    • Me yasa wasu mutanen surutu da shiga mutane ba ya musu wahala wasu kuwa yake musu?
    • Me yasa wasu sun gwammance su zama kullum suna su kaɗai wasu kuma ko da kuɗi ba za su iya ba?
    • Me yasa wasu duk abin da in dai a aji za a koyar ba abin da zai hana su ganewa wasu kuma sai an nuna musu shi ɓaro-ɓaro sun gani ko ma sun taɓa?
    • Me yasa wasu suke da saurin sabo da ƙulla abota wasu kuma sai an ja daga?
    • Me yasa wasu sun fahimci rayuwa da wuri wasu kuma har sun fara gangarawa amma ba su san inda suka dosa ba?
    • Me yasa wasu suke da naci, duk abin da suka sa a gaba sai sunga abin da ya turewa buzu naɗi, wasu kuma daga sun fara kamar ana mintsininsu suke bari?
    • Me yake sa mutum ya ji ga shi dai yana rayuwa kuma yana cimma abubuwa amma ba ya ganin ma’anar rayuwar ta sa, wani da bai kai shi ba kuma yana masa ganin ya kai wani mataki har yana sha’awarsa?

    Ba iya tambayoyin ba kenan, wannan kaɗan daga cikinsu ne, in kai iri na ne mai yawan zama yana ƙoƙarin gano wani abu ba mamaki ka taɓa yi wa kanka wasu daga cikin tambayoyin nan. Ko ka samu amsa ko ba ka samu ba, ni dai abin da nake fahimta shi ne, akwai lokacin da mutum yake matuƙar buƙatar ya san kansa, sanin kansa ne zai ba shi damar iya amsawa kansa mafi yawancin tambayoyinsa.

    Wasu tambayoyin ko da ka tambayi makusantanka, ko wasu da kake ganin sun fi ka, za ka ga ba za su ba ka amsa a yadda kai kake kallon abun ba, domin yawancin jama’a suna magana ne suna masu la’akari da yadda su suke.

    Wannan dalilin kaɗai zai iya hana abin da za su faɗa ya iya gamsar da kai. Amma idan kai ma ka san kanka fa? Za ka san a yadda za ka musu tambayar, kuma za ka fahimci a yadda suka kalli abun sannan ka alaƙanta amsarsu kai ma da yanayinka.

    Ni ba masanin kimiyya ko halayyar ɗan Adam ba ne, ni mai sha’awar rubuce-rubuce ne kawai, a wannan ɗan littafin na yi ƙoƙarin tattara abubuwan da na ci karo da su a halin binciken da na yi ta yi game da sanin kai na.

    Tambayoyi da dama na samu amsarsu, waɗanda ban samu ba kuma ina ci gaba da nemansu. Jin daɗin da nake yi a yanzu da na fahimci kaina ya wuce misali, haka kawai don mutane suna yin abu ba zai sa ni na yi ba, in ba ni da buƙatarsa (wannan ba ya kore siyasa ta rayuwa, in ka tsinci kanka a wurin da kowa yake da jela kai ma ka samu tsumma ka ɗaura, in ba haka ba za a dinga kallonka a matsayin barazana har a iya maka illa ta inda ba ka yi tsammani ba).

    Abubuwan da na ke sa ran za ku ƙaru da su a wannan ɗan littafin ga su kamar haka:

    • Meyasa ba ka san kanka ba
    • Muhimmancin sanin kai
    • Dabarun sanin kai
    • Amsa wasu tambayoyi da za su bayyana maka kanka
    • Muhimmancin samar da manufar rayuwa
    • In ba za ka iya sanin kanka ba to ka yi…

    Abin da na ke buƙata daga kai mai karatu shi ne wannan littafin na rubuta shi ne a matsayin wata ƴar ƙaramar tunatarwa ga kaina da sauran mutane da nufin ya yaɗu a tsakankaninmu mu ma su jin yaren Hausa. Don haka in ka samu kuma ka karanta kada ka bar shi a zaune haka nan, ka turawa abokananka ko da guda 3 ne domin su ma su amfana.

    Idan ka karanta wannan littafin ba ka ƙaru da komai ba, na bar “link” na whatsapp ɗina a kowanne shafi na littafin, za ka iya min magana don bayyana min kura-kuren da ke cikin littafin, da kuma bubuwan da suka sa littafin ya gaza wurin amfanar da kai.

    Idan ka ƙaru sosai kuma kana sha’awar cigaba da samun rubuce-rubuce na, ka ziyarci shafinmu na fesbuk da yake saman kowanne shafi domin mu ci gaba da ƙaruwa da juna.
    Allah nake roƙo ya amfanar da duk wanda wannan littafin zai isa gare shi, sannan ya ba mu ikon yin aiki da abubuwan da suke ciki ni da ku gaba ɗaya.

    Ka Ɗauka Ka Sani

    Sau da dama in na fito daga gida zan ga mutane a zazzaune suna hirar duniya ko a ƙarƙashin bishiya ko a kan wani dakali ko benci. Cikin irin hirarrakin nan da suke zai yi wuya ka ji babu labarin wani a ciki.

    Misali idan hirar ƙwallo suke za ka ga sun san komai game da gwaninsu, sun san haihuwarsa, garinsu, iyayensa, yaushe ya fara buga tamola, ƙungiyoyin wasannin da ya bugawa wasa, kofi nawa ya taɓa ɗauka, yanzu a wacce ƙungiya yake, nawa ne albashinsa da sauransu.

    Haka nan in hirar siyasa suke yi, komai na wannan ɗan siyasar sun sani, in hirar malamai ce ma haka, kowanne hali suke ciki suna sane. Haka nan idan ‘ƴan wasan kwaikwayo ne ko ma su sarauta. Abun ba ya tsaya a iya shahararrun mutane ba ne kaɗai, har waɗanda ake unguwa ɗaya da su, waɗanda suka kai, da waɗanda ba su kai ba za ka ga duk an san komai nasu.

    Wani abun ban mamaki shi ne da za ka kalli wannan mutumin shi a karan kansa, ta hanyar nazarin halayyarsa za ka fahimci ya san kowa ban da mutumin da ya fi cancanta ya sani, wato kansa.

    Ba haka kawai mutane suke nuna halin ko in kula da sanin kansu ba, saboda daɗewar da suka yi da kansu ne ya sa suka ɗauka sun san kansu, don haka suka mayar da hankalinsu kan sanin sauran mutanen duniya.

    Wannan kuwa ba abun mamaki ba ne, domin bincike kan bincike na masana ya tabbatar da cewa mutum halitta ce da dole sai ta yi imani da wani abu, in ba ta samu abun da za ta yi imani da shi ba sai ta ƙirƙiro abubuwa, ko ta dinga zato da tsammani kan wani abu, sannan ta mayar da zaton nan gaskiya a zuciyarta (Andrew Newberg: why we believe what we believe).

    Wataƙila wannan dalilin ya sa mutane da yawa suke ganin sun fahimci kansu, idan kana/kina cikin mutanen da suke ta ƙoƙarin ganin sun fahimci kansu amma sun rasa mafita saboda ƙarancin bayanai ko taimakon da zai haskaka musu su waye, to wannan littafin na ka/ki ne.

    Idan kana cikin mutanen da sun riga da sun ɗauka sun san kansu, amma hakan bai taimake ka wajen tsinana wani abu a rayuwa ba, yana da kyau ka ɗan duba wasu shafuka kaɗan cikin littafin nan. Idan ka fahimci kanka, kuma ka gamsu haka kake amma kuma ka kasa yin komai da rayuwarka duk da haka, akwai shawarwarin da zan kawo a gaba da za su taimaka maka. Sai a biyo ni domin shan karatu.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Sababbin Karin Maganar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu