Tag: Illar Magungunan

  • Magungunan Na Aiki Ta Hanyar Daƙile Azarbabin Sinadarin Isar Da Sakon Zafi A Jijiya Zuwa Ga Ƙwaƙwalwa.

    Magungunan Na Aiki Ta Hanyar Daƙile Azarbabin Sinadarin Isar Da Sakon Zafi A Jijiya Zuwa Ga Ƙwaƙwalwa.

    Saidai waɗannan magungunan basa buƙatar ake musu shan gaba gadi, ko kullum-kullum kamar abinci, domin suna da tarin illolin da suke haifarwa jiki, ko likita inya san me yake bazai baka su na sama da kwana uku ba, yayi yawa kwana 5.

    Idan kuwa xaka wuce haka kana Sha toh tabbas sai ya hadama da wani maganin da zai rage tasirinsu, kuma zaita kokarin gano tushen matsalar domin maganceta, don bazai so ka jima akai ba.

    Daga cikin matsalolin da magungunan kan haifar duk da suna dauke zogi sun hada da:  haddasa zubar jiki ta cikin ciki, lalata koda musamman idan mutum nada ciwon koda kuma aka bashi su, yawan kwarnafi, ciwon ciki, haddasa ciwon ulcer, gudawa, tayar da ulcer, ciwon hanta, kawo tsaiko wajen control din ciwon suga, ta azzara hawan jini musamman me wuyar sauka inya hau, ciwon zuciya, toshewar magudanan jini, tayar da asthma…dadai sauran matsaloli.

    Karanta cikekken bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure)

    Wannan maganin na zuwa a nau’in ƙwayoyi, mai na shafawa, maganin ruwa, da kuma allura.

    Babban Saƙona Gareku Jami’an Lafiya Shine:
    • Ku sani bawani magani a cikin rukunin dake gaba da wani. ma’ana karka taɓa tunanin ibuprofen yafi diclofenac ko feldin, karka taɓa tunanin celebrex yafi cataflam ko naproxen… Baki dayansu efficacy dinsu guda, ba wanda yafi wani, koda patient yace ga wanda yafi masa karka taɓa falling for that, duk efficacy tasirinsu guda.
    • Da nsaids na sha, dana shafawa, dana allura, duk aikinsu guda ne, babu banbanci, hanyar shigarsu jika ne kurum ta bambanta su.
    • Duk da ajika tasirinsu guda toh amma illar su wato side effects ba iri daya ba ce baki daya, ta bambanta wanda wannan shine abin dubawa kafin ka ba mutum NSAIDS bawai don wani yafi wani karfi ba, a’a wannene bazai baiwa patient dinka matsala ba shine abin dubawa, musamman inyana da ulcer.
    • Maganin nan nada matukar illa ga kayan ciki, amfani dashi akai akai nasa uwar hanji ta huje acid ya zuba a kayan ciki yaddasa matsalar chemical peritonitis ko septic daka iya kisa nan da nan in ba’a abude mutum anyi tiyata an wanke kayan cikin ba.
    • Ko yaushe in zaku rubuta ku fara daga mafi ƙanƙantar a dadi, wato low dose. misali kar wuce guda kaba mutum 100mg kurum don son ya daina jin zogi alhalin akwai 25mg ko 50mg. Ka fara daga kadan in abin bai sauka ba saika qara dose din.
    • Ba kowanne ciwo ake rubuta su ba, ciwon da mutum yake ciki yau da gobe anso mutum ya jure basai yasha magani ba. Kurum sai ciwo me tsananin gaske ake son shansa, wanda mutum bazai iya jure masa ba.
    • Ko yaushe a tabbatar sai bayan da aka ci abinci sannan aka sha, kar a shasa sanda ciki yake empty za’a ji ba dadi, musamman inda ulcer. Inko zaka ba mutum toh qara masa da anti acid ko PPI irinsu omeprazole, rabeprazole ba laifi yin hakan.
    • Karka taba combine NSAIDS biyu ga mara lafiya, Ina ganin haka nasan bakasan me kake ba. Na gayama efficacy dinsu guda. Karka taɓa hadawa mutum dclofenac da feldin, ko naproxen da piroxicam, ko indocin da celebrex… Kuskure ne ba taimako bane.
    • Ga wanda yake da matsalar zuciya ko hawan jini, ko heart attack, ko stroke, ko ciwon sugar …NAPROXEN shine Nsaids din da yafi dacewa dasu saboda yana da cardiovascular safety profile.

    Domin karanta bayani akan Hawan Jini (Hypertension) Danna nan

  • Amfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements )

    Amfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements )

    Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kadai bace take samar da morewar zaman aure, saduwa itace akan gaba.

    Wannan yana nufin cewa koda mace tana da ladabi da biyayya,iya magana, iya girki, iya ƙwarƙwasa,iya ƙwalliya,tsabta da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure,to dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta. Haka nan kuma koda namiji yana da ƙoƙarin samar ma matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa. Bisa wannan dalilin ne maza suke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.

    Abinda Ake Nufi da Gamsar da Juna Wajen Saduwar Aure (Sexul Satisfaction )

    Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin musulunci (Islamic clerics), da na halayyar dan-adam (psychologists) sunkai sun komo game da ma’anar gamsarda juna a wurin saduwar aure. Amma duk bayanansu sun tattara ne akan cewa ma’anarsa itace a samu natsuwar da zata gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan bukatar hakan ta taso.

    Da Wannan Ne Wasu Da Yawa Daga Cikin Mazajenmu Suke Ɗaukar Cewa Mutum Ba Zai Iya Gamsar Da Iyalinsa Ba:
    • Idan yana da al’aura mai kauri,ko tsawo, ko kuma duka biyun.
    • Idan yana dadewa wajen saduwa

    Hakan ne ya baiwa wasu kamfannoi masu sarrafa magungunan bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samarda magunguna iri-iri wadanda aka ce suna baiwa namiji karfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. Abin yayi yawa sosai, ta yadda masu wadannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.

    Rabe-Raben Magungunan Bature Na Kara Karfin Namiji 
    • Ƙwayoyi (drugs): wadannan sune magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun hada da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu. 
    • Mayuka (creams): wadannan sune magungunan da ake shafawa. Suma suna da yawa, kamar Maxman Delay Sex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.
    • Allura (injection): wadannan sune magungunan da ake yin allura dasu. Suma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.
    • Tiyata (surgery): wannan shine aikin yanka mazakuta da ake yi a dakin tiyata domin a kara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). Anfi yinta a kasashen turawa, kuma tana da tsada sosai.
    • Jike-jiken magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi yafi yawa a cikin al’umarmu. Suma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilimin kimiyya basu cika yarda da tsabtar wadannan magungunan ba, haka kuma basu yarda da sahihancin ka’idar amfani da su ba (dosage).

    Masu amfani da wadannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan baya rasa nasaba da abubuwan da ake hada su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, horny goat weed, fenugreek, maca da sauransu. Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya karuwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa dadewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in baiyi amfani dasu ba. Assha! Kaga kenan matsala ta auku.

    Sirrin Gamsar Da Mace Wajen Saduwar Aure 

    Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar damu yadda za’a gamsar da mata wurin saduwa:

    نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ 

    “matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda kuke bukata, kuma kuyi wasanni dasu (a lokacinda zaku sadu dasu)”, Baqarah: 223. 

    Kenan idan mutum yayi wasaanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita. Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa dadewa ana saduwa shine ƙwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya bane, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17. Idan ta kai minti 20, to, tayi yawa domin zata iya sanya ni’imar matar ta dauke, daga nan sai ta fara jin zafi, kila ma ayi mata rauni. Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na fada bane, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba. Domin karanta bayani akan Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i shiga nan

    Menene Abun Yi?
    • Matsalar ƙanƙanacewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to ya kamata ya tuntubi likita domin a dora shi akan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, wadanda idan illarsu ta taso bai san yadda zai magance ta ba.
    • Idan bai  zama dole ba, kada ka saba ma madam da dadewa ana saduwa, domin idan ka daina dadewa daga baya, to, akwai matsala fa.
    • Ka karfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda qur’ani yayi umurni.

    Domin karanta Kadan Daga Cikin Matsalolin da Mata Kan Fuskanta A Lokacin Zuwan Al’ada Danna nan