Tag: Haihuwa

  • Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Mahaifar Mace wato “Uterus” a sanda ta ɗauki ciki babu wani guri a jikin halittar ɗan adam da jini ke kai-komo ba tare da ƙaƙƙautawa ba irin wannan gun…. Saboda ƙoƙarin jiki don ganin ya samarwa da abinda ke cikin iska, jini, abinci da kyakkyawan yanayi. Guri ne da ake kira “No go Area” in dai da sunan wargi ne, saboda ko ya hatsari ya faru ana iya shiga uku.

    A duk minti ɗaya na agogo wato sekons 60 sai jini adadin Milimeter 800 zuwa dubu (1liter) ya shiga mahaifa ya fita. Wato dai kwatankwacin ledar pure Water 3 zuwa 4 na jini a duk minti. Shi ko jini baki ɗaya a jikin mutum an yi ƙiyasin ba ya wuce lita 5. Ka ga kenan a minti biyar kacal duk adadin jinin da ke jikin mutum ke shiga ya fita daga cikin Mahaifa. 

    Toh wannan ne yasa ko ya mace ta haihu jini ya ɓalle minti 4 zuwa 5 kacal ta mutu ta gama. Abun ba ya buƙatar ɗaukar lokaci, domin kafin a ankara an yi ta an ƙare. Shi yasa zubar jini bayan haihuwa da ake kira post partum hemorrhage ke kashe mata a karkara da birane ba ji ba gani, domin ko kuna raye a inda manyan asibitoci suke jinkiri kaɗan na abin hawa, ko shawarwarin ya za ai, ko cinkoso a hanya na iya kawo mutuwa ɓagatatan. 

    Toh yanzu Mace masu ciki sun saka kansu cikin wata musiba ta shan wani ruwa da suke wa laƙabi da “RUWAN NAƘUDA” ko a sakaya a riƙa faɗin “RUWAN ADDU’A”. Da ake karɓarwa mata a ba su su sha da sunan naƙuda ta zo musu a gurguje su haihu nan da nan abinda muke kira “PRECIPITATE LABOR.” 

    To alal haƙiƙa ku sani wannan ba wani ruwa ba ne illa ruwan musiba, ruwan guba, ruwan ta-da zaune tsaye, wallahi, wallahi, wallahi duk macen da ke marmarin tafiya lahira a dalilin haihuwa, ko take da burin ta sha da ƙyar tare da ja wa mijinta da iyayen ta asarar manyan kuɗaɗe ba tare da shiri ba, ko take da burin daga haihuwa ɗaya kar ta kuma har abada…

    Toh ta je a ba ta wannan ruwan ta riƙa sha, tunda Allah ya ba ku hankali don ku yi tunani amma sam kun mai da ƙwaƙwalenku tamkar tsumma. Kowanne tarkace yanzu kawowa ake mata su kuma su ɗiba babu lissafi. Shi wancan ruwan wasu muggan sinadarai ake sa mishi masu aiki irin na “Okzitosin” da nan da nan ke sa mahaifa ta fara harbawa tana jijjiga domin juye abinda ke cikinta, tana fisga tana talewa ƙarshe musibar da ake shiga FASHEWAR MAHAIFA yake haddasa wa inda nan da nan Mace kan fita hayyacinta, ta nufi lahira.

    Amma masu ba da irin wannan ruwan wasu ma iyayen yaran ne ke kawo musu. Sun kashe ‘ya’yansu ba tare da sun san su ne suka kashe su ba, sai dai a ce ta haihu amma jini ya ɓalle Allah ya yi mata rasuwa. Karya ne ku kuka kashe ta, kuma akwai shari’a gaban Allah. Kun ba ta abinda ba ku da ilimi kansa, kun ƙi kuma saurarar masana ku ji jan hankalin da suke game da irin wannan muggan al’adun.

    A ƙalla na sami mata uku da suka mutu a wannan tsakanin dalilin shan wannan ruwan naƙudar. Sannan na sami mutum 2 tsakanin nan ‘ƴar shekara 17 da ƴar 21 wanda suka sami fashewar mahaifa, duk da ba su mutu ba sun sha da ƙyar to amma dai hakan na nufin ba su ba kuma ɗaukar ciki ballantana su haihu a duniya, in mahaifa ta fashe ba batu ne a ɗinke ta ba, ta riga ta yi condemn.

    Kuma abin takaici duk jariran nasu sun mutu tun a ciki, shikenan in ba mazajen ƙwarai ba ne shin wa zai zauna da macen da ba zata iya haihuwa ba a irin wannan rikitaccen zamanin namu? Sabuwar amaryar shekara ɗaya a ce ka gane ba ita ba kuma haihuwa dole sai kai shirin kuma sabon aure in kana son haihuwa. 

    Toh wannan ba shi ba ne ma ƙarshen damuwar, ba su ba kuma iya riƙe fitsari, yanzu rayuwarsu za ta dauwama ne da robar fitsari a jika, hanyar kashi ta ɓulle ta dubura ta haɗe da farji. Tsabar wauta da rashin hankali, yarinyar da ko haihuwar fari ba ta yi ba amma da zarar ta sami juna biyu shikenan anta mata aiken abubuwa iri-iri ana ta sha, wannan maganin zaƙi, wannan maganin ciwon mara da dai sauran su.

    Ya kamata idon ya buɗe ku gane me duniya take ciki, kar ki laminci ganganci da rayuwarki. Lallai mu hankalta. Babban abin damuwar har ‘yan boko ko matan da kake ganin suna da ilimi su ma sukan auka cikin irin wannan ɗebe-ɗeben, a haka na sami mace me Masters amma ta je wai an ba ta maganin fibroid a Islamic CHEMIST. An ce idan ta sha zai narke, ƙarshe ga shi fibroid bai narke ba dukkan mararta ta zazzage.

    Dole aka cire mahaifar aka zubar, sannan ba ita ba kuma haihuwa, sannan mafitsararta “Bladder” ta fashe ba za ta gyaru ba, fitsari yanzu ta cikin farjinta yake fita, haka zalik kashi ma wani na fita ta duburarta wani kuma na biyo ta cikin farjinta duk. Yanzu me ya fi wannan tashin hankali, kin je kin kashe kuɗi kin illata kanki a banza da wofi.

    Hakance dai ke faruwa a fannin breast cancer, mace na fama da ciwon nono amma taita biye-biyen masu magunguna a loko suna karɓe mata kuɗi, ba za ta je asibiti ba sai abu ya gama lalacewa nono ya fara wari, in cancer ta gama yaɗuwa inda sai de mutuwa kurum. Don haka Lallai Yan Uwa Mata ku yi hattara, lafiya ta wuce wasa wallahi in kunne ya ji……

    Karanta Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Abin Da Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa (AMNIOTIC FLUID)

    Abin Da Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa (AMNIOTIC FLUID)

    Amniotic fluid ruwa ne dake zagaye da jariri a cikin mahaifa wanda ke taimakawa yaron ya sami balance ta yadda ko faɗuwa mai juna biyu ta yi ta ruf da ciki, cikin ikon Allah shi jariri ba zai san me yake faruwa ba ma ballantana abun ya shafe shi.

    Shi wannan fluid ɗin yakan haɗu da fitsarin da babies ɗin kan yi a cikin mahaifa lokacin da suka kai sati 25weeks sukan kuma fara shan wannan ruwan tun daga sati na 10-11 weeks na ciki, ko lokacin da fatar ƙwayar halittar kumatunsu cikin mahaifa ta fara rufe bakinsu. Dan haka dama sukan sha abinsu tun a ciki.

    Daga lokacin da ciki ya kai sati 20weeks duk wannan ruwan kusan yakan rikiɗe ya zamo fitsarin babies ɗin ya fi yawa. Yayin da ainisin ruwan amniotic ɗin da ke zuwa daga ƙodar baby ɗin ke kasancewa ɗan kaɗan kurum.

    ME YASA SUKE SHA WASU HAR HAKAN YASA SU MUTU?

    Kamar yadda na faɗa ainihin ruwan amniotic fluid dama suna shan abinsu tun a ciki kafin zuwan haihuwa domin shi ne ke ƙara ma huhun su (lungs) ƙwari. Abinda suke sha ya wahal da su yayin haihuwa koma su rasa ransu muna kiransa da (MECONIUM).

    Meconium wato na nufin kashin farko da suke fara yi a ciki yayin artabun naƙuda, idan ya haɗu da ruwan fluid ɗin suka haɗiya shi ke musu illa yake shiga ƙofofin numfashinsu.

    Wanda kamata ya yi sai bayan an haihu za su yi wannan kashin koma kada su yin kwata kwata sai bayan an fara ba su nono. Bisa larura amma idan aka samu doguwar naƙuda musamman haihuwar fari ko kuma matsatsi yayin haihuwa shi ke jawo su yi kashin kuma su sha abinsu musamman yayin da suka ja numfashin farko suka fara fitowa yayin haihuwa.

    Sannan hakan ya fi shafar yaran da suka jima suka ɗau sati 37 zuwa 41 a ciki ko sati 42. Wannan shi ne abinda ke faruwa, kun ga kenan ba abu ne da yake wajibi a a hana faruwarsa ba sai dai ana iya daƙilewa idan ka ba iyalin ƙwarin guiwa zuwa awo tare da kulawa yayin goyon ciki.

    Danna nan don karanta Hatsarin Amfani Da Mayukan Hasken Fata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Za a Magance Ɓallewar Jini Bayan Haihuwa

    Yadda Za a Magance Ɓallewar Jini Bayan Haihuwa

    Malamai masana ilimin likitancin musulunci sun gano cewa cin dabino mai bauri bayan haihuwa yakan hana zubar jini.

    Da yawa mata sukan samu ɓallewar jini bayan sun haihu, wasu ma har ya kai da rasa rayuwarsu. Wannan ya ɗauko asali daga mahaifiyar Annabi Isa (Alaihis Salam), wato; Nana Maryam (Radiyallahu Anha) bayan ta haifi Annabi Isa (Alaihis Salam) kuma ta haife shi a gurin da ba wanda zai kawo mata taimako.

    Ubangiji ya umarce ta da ta kama kututturen dabinon da ke gabanta ta girgiza shi; nan take zai girma ya yi ‘ya’ya ya zubo ta kuma ɗebi ‘ya’yan ta ci. Akan so duk macen da ta haihu ta nemi ɗanyen dabino; domin zai taimaka mata wajen zubar jini da kuma samun lafiya da kwanciyar hankali.

    Sannan ana amfani da ganyen geza, bayan an niƙa shi ya yi laushi. Akan jiƙa shi sai a bai wa mace ta sha. Shi ma yakan tsayar da jinin biƙi ko na haila wanda ya ƙi tsayawa. Hatta yankewa idan mutum ya yi jini ya ƙi tsayawa da an sa garin geza zai tsaya.

    Haka ana amfani da ɓawon gyaɗa soyayya wanda aka murmushe. Za a haɗa shi a kwaɓa shi da man zaitun. Nan take in aka sa shi shi ma jinin zai tsaya. Sannan ana amfani da ganyen ruhu da balma a jiƙa.

    A sha nan take shi ma yakan tsayar da jini. Waɗannan duk abubuwa ne da ake sarrafa su domin su tsayar da jini na al’ada ne ko na biƙi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shayarwa Bayan Haihuwa danna koren rubutun nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Nau’in Jinkiri Guda Uku Da Suke Sabbaba Mace-macen Mata Masu Naƙuda a Nigeria

    Nau’in Jinkiri Guda Uku Da Suke Sabbaba Mace-macen Mata Masu Naƙuda a Nigeria

    Ko kun san adadin mata nawa ke rasa rayukan su duk shekara yayin naƙuda a nigeria da kuma dalilan faruwar hakan?

    Jinkiri na farko:

    Da ake samu shine zaka ga mutane suna ƙoƙarin neman taimako a gida, kamar neman maganin gargajiya a yi ta bawa mai naƙudar,ko a ce a saurara mu gani,da sauransu,wanda hakan ba komai yake kawo ba face matsala ga mai naƙudan yayin haifar da ita da kuma ɗan dake cikinta,rashin neman taimakon likitoci a kan lokaci ko rashin kai mai naƙuda asibiti a kan lokaci,haye-shayen rubutu ko maganin gargajiya suna ƙara cikawa mai naƙuda mara da fitsari ne kawai,har yakai ga janyo mata yoyon fisari a wasu lokutan.

    Jinkiri na biyu shine: 

    Rashin samun abun hawa kamar mota ko adaidaita sahu ko wani abu na hawa a kan lokaci,ko rashin hanya mai kyau na ababen hawan ta yadda za su sami isa da mai naƙudan asibiti a kan lokaci,wannan ya fi faruwa ne ga mutane mazauna ƙauyuka da unguwannin dake fama da munin hanyar sufuri.

    Domin karanta bayani akan Kansar Bakin Mahaifa Danna nan

    Jinkiri na uku shine:

    Jinkiri wajen tunanin wani ingantaccen asibiti ne ya kamata a kai ta, wasu lokutan mace na samun damar tsallake jinkiri na farko da na biyun amma sai ta afkawa wani sashin jinkiri na uku sakamakon rashin ƙwararrun ma’aikata ko rashin isassun kayan aiki a asibitin. 

    Yan’uwa masu daraja ku sani,rashin kai mace mai juna biyu asibiti don duba lafiyar ta da abunda ke cikinta na janyo mata matsala babba da kuma jefa rayuwar ta cikin barazana.

    Domin karanta bayani akan Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

    Rashin mayar da hankali ko rashin gaggauta kai mata masu naƙuda asibiti a yayin da suke naƙuda zalunci ne dake sabbaba yawan mace-macen matan a nigeria,wannan mummunar ta’asar dai tafi faruwa ne Arewacin ƙasar nan, Jikirin, akwai buƙatar wayar da kan wadanda basu fahimta ba da kuma hukunci ga masu ganganci.

    Daga ƙarshe muna miƙa shawarar mu ga mata da su mayar da hankali wajen kulawa da  ziyartar asibiti a kan ƙa’idar da likita ya basu,sannan suke bada haɗin kai yayin da likita ke duba su. Su kuma Mazaje su zama masu tausayawa iyalansu a irin wannan yanayi da suke cikin mafi wahalar yanayi,suke gaggauta kai iyalansu asibiti lokacin naƙuda,suke tallafa musu gun ziyartar Asibiti lokacin da suka ɗauki ciki don duba lafiyar su da abunda ke cikin su,haka nan,muna riƙon hukumomi da masu hannu da shuni suke taimakawa ƙananan asibitocinmu domin hakan shine hanyar farko na inganta lafiya.

    Domin karanta Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo Danna nan

  • Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Ɗaukar Ciki

    Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Ɗaukar Ciki

    Akwai abubuwa da yawa da za su iya haifar da rashin ɗaukar ciki ga  mace, wanda aka sani da rashin haihuwa, yana da mahimmanci a tuna cewa rashin haihuwa na iya shafar maza da mata, kuma ba koyaushe ba ne kawai saboda lafiyar haihuwa ta mace.

    Wasu Dalilai Na Rashin Haihuwa Na Mace Sun Haɗa Da:

    Cutar Ovulation: Matsalolin Ovulation na iya faruwa saboda rashin daidaituwar yanayin hormonal ko kuma al’amurran da suka shafi ovaries, polycystic ovary syndrome (PCOS) wani yanayi ne na kowa wanda ke shafar ƙwai.

    Toshewar Tube ko Lalacewa: Cututtuka irin su pelvic inflammatory disease (PID) ko endometriosis na iya haifar da toshewa ko tabon bututun fallopian,wanda ke hana ƙwai isa mahaifa. 

    Karanta amsar wannan tambayar Nakan Ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] a nan 

    Al’amarin Uterine: Rashin al’ada a cikin mahaifa, kamar fibroids ko polyps na mahaifa na iya shafar dasa embrayo da girma. 

    Shekaru: 

    Yayin da mata suka tsufa, yawan haihuwa ya ragu, kuma adadin ƙwayayen da za su iya samu ya ragu, hakan ya sa ya zama ƙalubale wajen samun ciki musamman bayan shekara 35. 

    Cutar Endocrine:

    Matsalolin thyroid ko wasu matsalolin hormonal na iya yin tasiri ga haihuwar mace. 

    Ayyukan da suka gabata: misali surgeries:

    Tiyatar da ta gabata a yankin pelvic na iya haifar da mannewa ko lalata gabobin haihuwa, yana shafar haihuwa. 

    Domin karanta bayani akan Samiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash} Danna nan

    Rashin lafiya ta autoimmune: 

    Wasu yanayi na autoimmune na iya kai hari ga gaɓoɓin haihuwa da kuma tasiri ga haihuwa. 

    Cutar Halittar Halitta wato genetic: 

    Halin da ba kasafai ake samu ba yana iya haifar da rashin haihuwa a wasu lokuta.

     Lifestyle factors:

    Abubuwan da suka haɗa da shan taba, yawan shan barasa, shan muggan ƙwayoyi, da ƙiba duk suna iya shafar haihuwa. 

    Damuwa:

    Damuwa na yau da kullum na iya kawo cikas ga daidaiton hormonal, yana shafar yanayin al’ada da haihuwa. 

    Yana da mahimmanci ga ma’aurata masu fama da rashin haihuwa su je su ga likita domin neman shawarai, ƙimar ƙima na iya taimakawa wajen gano ainihin dalilin da kuma jagorantar jiyya masu dacewa, wanda zai iya haɗawa da canje-canje salon rayuwa, magunguna, aikin tiyata, ko taimakon fasahar haihuwa kamar in vitro haɗi (IVF) ko intrauterine insemination (IUI), ka tuna cewa al’amuran haihuwa na iya zama haɗaɗɗun kuma suna iya haɗawa da abokan tarayya biyu, don haka ana ba da shawara sosai ga namiji da mace. Fatan Allah ya ba mu lafiya baki ɗayanmu.

    Domin karanta Alamomin Cancer Danna nan

  • Mutane Da Yawa Sukan Yi Tambaya Akan Aa Yaya Za a Samu Hanya Mafi Sauki Ta Yin Tazarar Haihuwa Ba Tare Da Shan Ƙwayoyi Ba

    Mutane Da Yawa Sukan Yi Tambaya Akan Aa Yaya Za a Samu Hanya Mafi Sauki Ta Yin Tazarar Haihuwa Ba Tare Da Shan Ƙwayoyi Ba

    Hayar itace lalle lalle mace sai tasan ovulation period nata domin itace lokocin ake kyeutata zato ciki yake shiga.

    Menene Ovulation?

    Ovulation: shine wani lokaci da mace ke fafe kwan haihuwarta wanda da zaran ta fafe ta kusancu miji to shikenan sai ciki da ikon Allah. 

    lokacin ovulation lalle idan kina da kula zaki gane,yakamata mu dinga kula domin akwai wani irin painless contraction da zakiji,mun san fallopian tubes dinmu guda biyu hagu daya a dama,so duk wata daga gefe daya ne kwan zai fito.

    Ga Alamomin Da Ake Ji Lokocin Ovulation Period:

    • Farko shine painless contraction zakiji wani irin ciwo a hagu ko dama.
    • Zaki dinga jin menstral pains slightly amma ba menses kikeyiba
    • Areola: wato black point na nononki zai kara baki kuma nipple wato kan nononki zai mike yayi erect kuma akwai zafi kadan kadan musamman idan ana tabawa 
    • Vaginal fluid:majina mai tsananin danko wanda take zama kamar spring zai dinga fito miki a gabanki
    • Matsananciyar sha’awar namiji duk yadda mace take gudun miji irin wannan rana mace baza ta iya gudu ba domin ita da kanta take begen mijinta wato sha’awarta ta karu sosai. 

    A wadannan lokutan sai a karauce wa jima’i ko ayi amfani da kwaroron roba,idan ba kya gane ta alamu ga bayani dalla dalla  yadda zaki irga lokocin ovulation naki:

    (1)     Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 22, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana takwas (8), a kwana na  takwasdin nan shine ovulation period nata,domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 7,8 da 9.

    (2)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 23, to za tafara irga daga ranan  da taga jinin hailanta zuwa kwana tara (9), kwana na  tara (9) ita ranar ovulation period nata,domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 8,9 da 10.

    (3)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 24, to za tafara irga daga ranan  da taga jinin hailanta zuwa kwana Goma (10),kwana na Goma (10),domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 9,10 da 11.

    Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan

    (4)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 24, to za tafara irga daga ranan  da taga jinin hailanta zuwa kwana (11),kwana na (11) itace ranar ovulation nata, domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 10,11 da 12.

    (5)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 26, to za tafara irga daga ranan  da taga jinin hailanta zuwa kwana (12), kwana na  (12)  shine ranar ovulation nata, domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 11,12 da 13.

    (6)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 27, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (13), a kwana na 13 idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga, domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 12, 13 da 14.

    (7)   Idan mace jinin hailanta yana zuwa a kwana 28, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (14), a kwana na (14) idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga,domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 13,14 da 15.

    (8)   Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 29, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (15), a kwana na (15) idan takwanta da mijinta ana kyautata zato ciki zai shiga,domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 14,15 da 16.

    Karanta cikekken bayani akan Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Magancesa

    (9)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 30, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (16), a kwana na (16) idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 15,16 da 17.

    (10)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 31, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (17), a kwana na (17) idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 16,17 da 18.

    Domin karanta Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

    (11)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 32, to za tafara irga daga ranan  da taga jinin hailanta zuwa kwana (18), a kwana na (18) idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 17,18 da 19.

    (12)    Idan mace jinin hailan ta yana  zuwa a kwana 33, to za tafara irga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (19), a kwana na (19) idan takwanta da mijinta ana kyeutata zato ciki zai shiga domin kariya ga samun ciki sai a kauracewa jima’i ko ayi amfani da condom a rana ta 18,19 da 20.

    Domi karanta Minene Fibroid? {Ƙarnin Mahaifa } Da Kuma Abubuwan Da Suke Kawosa Danna nan