Musanye Mafi Alheri

0
18

Ba za a ce an hana yin amfani da kayan shafe-shafe da sutura na zamani ba gaba ɗaya, sai dai, lallai ne a lura da ladubban Musulunci cikin kowane irin kayan ƙawa da ake so. 

Bayan haka, kuma matuƙar dai mace kyawun jikinta take tattali, to babu shakka za ta iya samun kayan abinci da na marmari waɗanda ake samun su a gonaki da kasuwanninmu a koda yaushe (cikin yardar Allah).

Sabobda haka, idan mace ta kula da cin abinci mai gina jiki, kamar nama da kifi da madara da kayan marmari irinsu ayaba da lemon zaƙi da tuffa da kankana da dai sauransu, da kuma kayan ganye, kamar su: lamsir da yaɗiya da zogale da dinkin, duk waɗannan cima ce wadda idan ana cin su akai-a-kai bisa tsari za su sanya jikinta ya yi kyau, kuma fatarta tabyi laushi da haske. 

Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

Haka kuma sauran kayan kwalliya waɗanda tuni shari’a ta kwaɗaitar da mata a kansu, kamar lalle da kayan zinariya da tadin alharini da sauransu. 

Bugu da ƙari, motsa jiki akai-akai idan mace za ta iya kullum ta keɓe guri ɗaya, inda ba mai ganin ta, sai waɓda ya halatta (kamar mijinta) ta yi tsalle-tsalle da sassarfa kamar na minti ashirin har ta yi gumi, sannan ta je ta yi wanka, wannan ma zai sanya ta ta zama mai ƙuruciya. 

Wani muhimmin lamari shi ne, tsoron Allah da yawan ambaton sa da bauta masa cikin nutsuwa, yana sanya haske da annuri a zuciya da fuskar muminai.

Domin karanta bayani akan Dunƙulallun Matsalli A Musulunci Danna nan 

Kuma duk irin kwalliyar da mace za ta yi, lallai ne ta lura da ladubban Musulunci na kwalliyar mata, kaɗan daga wannan ladubba su ne kamar haka: 

(1) Sutura ko kayan kwalliya su zama na halal ne, kuma masu tsarki. 

(ii) Su kasance masu suturce jikin mace ba masu bayyana kowane sashe na tsiraicin ta ba. 

(iii) Ya zamana tana yin wannan ado ne don bayyana godiya ga Allah wanda ya hore mata ni’imarsa. 

(iv) Ya kasance tana ɓoye adonta ga barin maza waɗanda bai halatta su ga adon nata ba. 

(v) (Idan matar aure ce) ta mayar da hankali wajen kwangwajewa don ɗaukar hankalin mai gidanta. 

(vi) Kada su zama kaya waɗanda suka keɓanta da maza. 

(vii) Kada su zama sanandin canza wani abu daga halittar da Allah ya yi mata. 

(viii) kar su zama kayan ado ne na din-din-din, wato ba za a iya cire su ko goge su daga jikin mace ba. 

(ix) Kada su hana sadar da ruwa ya zuwa fatar mace. 

(x)Kar ya zama akwai ɓarnar dukiya a ciki. 

(xii) Kada su sanya mace girman kai da nuna isa.

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceDunƙulallun Matsaloli A Musulunci
Labarin na GabaWaƙar Ya’yan Alhazai