Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Huɗu

0
158

Dole tana ji tana gani ya kafa mata doka idan dai har zai ci abinci to parlor ɗin kasa zai ci. Babu yanda ba ta yi da shi ba yaran su dinga hawowa sama amma yace ba za su hau ba tunda ita saman take so a bar mata, haka ta haƙura ta saka masa ido saboda abun yana nema ya zama matsala a tsakaninsu.

Duk wani taimako da aiki da malamai za su yi mata tana kan yi sai dai abun ya ƙi yi, idan ya yi kamar zai kama sai kuma ya sake botsare mata. Idan dai tana son ganin walwalarsa to ta yi wa yaran nan yanda suke so kuma ba tare da ta yi masa wani ƙorafi ba. Burinta ɗaya yanzu a aurar da Afaf domin haka ne kawai take ganin za ta sami natsuwa a gidan nan.

Don a halin da ake ciki komai zai yi da Afaf yake shawara, wasu lokutan ko ta ba shi list ɗin cefanen gidan sai ya tambayi Afaf abinda take buƙata ita da kannenta ya siyo musu. Idan kuma ya kawo kayan sai ya tsaya a ƙasa Afaf ɗin ta ware nasu kayan sannan ya hau mata sama da sauran. Haka dai take haƙuri, musamman da yake ya iya lallaɓa ta ya tsara ta kawai dai ya nuna mata yaran nan nasa ba za su taɓu ba.

Haka rayuwarsu ta cigaba.

Duk yanda yake jin zai samu Khadeeja ta saurare shi ya gagara, ga shi kuma sai a yanzu Allah ya jarrabe shi da ƙaunarta. Kusan kullum sai ya yi mata waya, idan ta ga dama ta ɗauka idan kuma ba ta ga dama ba ta ƙi ɗauka. Ya mayarwa kansa duk Juma’a da yamma sai ya je gidan duba Hammad, sai dai hakan bai ba shi damar ganinta ba.

Domin idan ya je ko da ya yi mata waya haka za ta saka a buɗe masa parlor ɗin baƙi ta turo masa Hammad, har ya gama hirarsa da Hammad ya tafi ba za ta fito ba. Don haka wasu lokutan sai kawai ya rutsa ta a office inda dole ta zauna su gaisa har su ɗan yi hira. Abu ɗaya ne yake hana shi zaƙewa a kan maganarta saboda har yanzu yana jin kunyar Baffanta, bai san da wane bakin zai je yace masa ya sake ba shi auren Khadeeja ba.

Shi yasa ya dage yake ƙoƙarin ganin ya gamsar da Khadeejan ta je wa Baffan da maganar da kanta. Kwanci tashi har shekara ta zagayo. Tun da ya gama haɗa takardun yake cike da farin ciki, haka ya kwana cike da zaƙuwa sabodan yanda yake son gari ya waye ya je ya sami Khadeeja ya yi mata albishir.

Yana fita office ɗinta ya fara tsayawa, ya yi sa’a kuwa ta riga ta zo. Kamar yanda ya saba a cikin office ɗin ya same ta tana zaune tana editing script ɗin da za ta yi amfani da shi wajen gabatar da show ɗinta. Yana shiga ya tura ƙofar sannan ya yi wa kansa mazauni a kujerar gabanta cike da walwala. Bayan sun gaisa yace ‘Kina jin daɗinki fa, kin ga yanda kike sheƙi kuwa.

Ta yi dariya tace ‘Don Allah ka bari, haba. Ko waya ma ba ka yi min ba kace min za ka zo to da ka zo na riga na shiga studio fa? Shi ma dariyar ya yi yace ‘Sai na jira ki mana. Ai idan kina son na daina zuwa wajen nan to ki yarda mu mayar da auren mu mu huta, in ba haka ba dole kullum na zo nan na yi attendance don duk masu shirin yi min shigar sauri su ganni su san ina nan ba fashi.’

Ta sunkuyar da kai don ba ta san me zata ce masa ba, amma dai yawan zuwan nashi office ɗin ya fara gundurarta. Ba wai don ba ta so a gan shi ba ne kuma ba wai tana jin ya isa ya hana ta kula wanda take son kulawa ba; kawai dai tana so ya ɗan ba ta space tunda ita dai ta gama magana a kan lallai ba za ta koma gidansa ba kuma har yanzu hakane a ranta.

Muryarsa ce ta katse mata tunanin da ya kirawo sunanta, ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido sannan ta kawar da kai. Yace ‘Ki sauwaƙe mana wahala ki yarda mu mayar da aurenmu, duk wani abu da ya ɓata miki rai a baya na yi miki alƙawarin ba za ki sake gamuwa da shi ba a zamanmu.’

Ta jijjiga kai ‘Na fahimce ka Mustapha, amma dai ka yi haƙuri. Ba wai kai ne ba zan aura ba, auren ne gaba ɗaya ba zan yi ba. Don Allah ka daina wannan maganar, ka mayar da hankali wajen kula da iyalinka. Ka ga yanzu ni babu aurenka a kaina, idan ta ji kana zuwa wajena zaku iya samun matsala. Ka zo kai ba ka sami natsuwa da ta gidan ba kuma ni ba aurenka zan sake yi ba.’

Ya jijjiga kai don ba ya son wannan maganar, shi yana ji a jikinsa Khadeeja matarsa ce shi kaɗai don haka duk tsawon lokacin da za ta ɗauka tana yi masa yanda zai jure. Ya zaro envelope daga aljihunsa ya ɗora a kan tebur ɗin ya tura mata gabanta yana murmushi yana cewa ‘Wannan na zo kawo miki daman. Ta ɗauko tana dubawa tana cewa ‘Me na samu?’

Ta zaro takardun daga envelop ta fara dubawa; kujerar Hajji Mustapha ya ba ta. Tana dubawa tana murmushi saboda yanda tunanin za ta je Hajji ya faranta mata zuciya. Ta ninke takardu ta fara mayarwa cikin envelop ɗin a daidai lokacin da murmushinta ya ragu. Ta tura masa gabansa tace ‘Na ji daɗi Abban Hammad, na gode Allah ya ƙara arziki da rufin asiri.

Amma ka yi haƙuri ba zan iya karɓa ba, ba wai don na raina ba ko wani abu. Na gaya maka ba zan sake aurenka ba so ka ga babu wani dalili da zai sa na karɓar maka kujerar Hajji. Kuma ko na karɓa ma Baffa ba zai taɓa barina na je ba sai dai a ɗaura mana aure kafin na tafi; kuma wannan ba zai yiwu ba. Please ka yi haƙuri! Amma na gode sosai.’

Kafin ta gama bayanin fuskarsa ta canza gaba ɗaya, ba tare da ya ɗauki takardun ba yace ‘To ki karɓa mana Khadeeja ki bari a ɗaura mana auren, please ki daina guduna haka. Ta sunkuyar da kanta cikin damuwa tace ‘Ba gudunka nake ba, amma dai ba zan iya ƙara aure ba.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci. Jimawa kaɗan yace ‘To yanzu ya kike so a yi? Ni da sunanki na biya wannan kujera. Ka yi hakuri ba zan iya karɓa ba. Suka sake yin shiru na ɗan lokaci. Kafin su yi magana aka ƙwanƙwasa ƙofar, ta amsa ta ba da izini aka shiga. Wata mace ce abokiyar aikinta ta ɗan leƙo tace ‘Anti Khadeeja yallaɓai yace ke ake jira a studio za a fara.’

‘Yanzu zan shigo.’ Ta faɗa tana shirin miƙewa. Ta dubu Mustapha tace ‘Bari na je kada ka sa a kore ni aiki. Ya yi dariya shi ma ya miƙe, sai dai tana kula da shi bai ɗauki takardun ba. Ta miƙa hannu ta ɗauka sannan ta zagayo ta tsaya a gabanshi, ta miƙa masa takardun tana murmushi tana cewa ‘Ka yi haƙuri ka tafi da wannan, wallahi ba zan iya karɓa ba.

Idan na karɓa ba zan iya da rigimar Baffa ba tunda na san ba zan aure ka ba. Ka yi haƙuri please. Ya miƙa hannu ya karɓi takardun yana tsare ta da ido kamar mai binciken wani abun a idonta, har sai da ta kawar da nata idon. Ta wuce ya biyo ta a baya suka fito daga office ɗin, suka jero har zuwa reception sannan ta yi masa sallama ya fice ita kuma ta miƙe ta nufi studio ɗin.

Tana fatan Allah ya sa dai kada ta kwafsa saboda yanda Mustapha ya jagula mata lissafi; me za ta yi da kujerar makansa? Wato ma shi har yanzu tunani yake saboda kujerar Makka yasa ta ƙi komawa gidansa? Bai ma san wacece ita ba kenan, zaman da suka yi tare bai sa ya fahimce ta ba.

Ba ta buƙatar kujerarsa kuma ta san tabbas idan ba aurensa ta kuma yi ba ko kashi ta kai gida tace shi ya ba ta sai sun yi rigima da Baffa, kuma ba ta shirya ƙarya ba saboda Mustapha wanda take so ya rabu da ita ya daina damun rayuwarta.

Tana tashi daga waje aiki ta wuce gidan Yaya Mama, ta yi sa’a yaran duk sun tafi islamiyya don haka ta sami Yaya Mama ita kaɗai. Bayan sun gaisa Yaya Mama tace ‘Bari na samo miki ruwa ko lemo. Ta dafe cinyarta tace ‘Bar shi kawai sai da na tsaya na ci abinci sannan na ƙaraso.’

Ba tare da ɓata lokaci ba ta fara ba ta labarin kujerar Makkan da Mustapha ya kawo mata ɗazu. Sai da ta gama ba ta labarin suka sheƙe da dariya a lokaci guda sannan tace ‘Wai ni zai saya da kujerar Makka ɗan rainin hankali. Yaya Mama tace ‘Ai kuwa ɗan rainin hankali lamba ɗaya, wato tunda kin ce ya sake ki saboda kujerar Makka bari ya biya ki sai ki yarda ya mayar da aurenku.’

‘Ashe kin gane. Suka cigaba da hira suna tuna abubuwan da Mustaphan ya yi a baya. Sai da Magriba ta fara kawo jiki sannan Khadeeja ta fara shirin tafiya. Bari na wuce kada magriba ta yi min a nan. ’Yaya Mama ta dafa hannunta tace ‘Khadeeja, idan fa za ki koma gidan Mustapha kin san babu wanda zai hana ki ko? Don ni ina ganin ma gara ki koma can ɗin tunda kin ga ko babu komai ga Hammad.

Kuma na ga har yanzu ba ki da wani manemin; duk da ma duk wanda za ki aura mijn wata ne don haka kin ga dole ki zauna da kishiya. Ni ina ga gara gidan Mustaphan tunda dai ya yi nadama har yana ƙoƙarin ya faranta miki. Nan take ta ɓata rai, ta zare hannunta ta ɗan matsa daga kusa da ita sannan tace ‘Ba zan taɓa komawa gidan Mustapha ba, aure kuma ba ya gabana balle na fara damuwa da rashin manemi.

Idan Allah ya saka ina da rabon aure a gaba to duk wanda Allah ya sa shi ne mijina zan aura amma fa in sha Allahu ba zan sake auren Mustapha ba. Mutumin da ya ɗauke ni ne kawai a matsayin solution to his problem. Ko yanzun ma da yake ta ƙoƙarin na koma gani ya yi ƙiriƙiri matar tasa ta kasa kula masa da gidan da yara kamar yanda na yi.

Shi yasa ya lallaɓo ya mayar da ni cikin wahalar da Allah ya raba ni da ita. Ba zan koma na, can su ƙarata. Ta miƙe ta ɗauki jakarta, don haka ita ma Yaya Maman ta miƙe. Ta san idan ta fiya takurawa da maganar yanzu za su yi faɗa don haka sai ta ƙyale ta suka yi sallama ta kama hanya.

Wunin ranar gaba ɗaya bai yi masa daɗi ba. Ko da dai bai sa ran Khadeeja za ta karɓi kujerar ba tare da an kai ruwa rana ba amma kuma bai sa ran za ta ƙi karɓa haka gaba ɗaya ba ba tare da wata ƙofa ta sulhu ba. Haka ya wuni a office ɗin babu walwala. Sai da yamma ta yi sannan ya kwashi kayansa ya koma gida.

Yana shiga ɗakinsa ya ajiye takardun hannunsa a kan mudubi; takardar kujerar da ya ba wa Khadeeja ce a sama tare da wasu takardun na office. Tunda ya je sallar magriba masallaci ya dawo ya yi zamansa a ƙasa shi da yara. Da farko ta ɗan zauna a wajensu ana hira gaba ɗaya, daga baya kuma sai ta tashi ta haye sama ta bar su.

Ɗakinsa ta shiga don ta samu ta huta domin nan ne kawai idan ta rufo ƙofar Rukayya ba za ta so ta buga ta tashe ta ba. Har ta wuce mudubin sai kuma ta koma da baya, ta sa hannu ta ɗauki envelope ɗin da ta ja hankalinta. A buɗe take don haka sai kawai ta zaro takardun ta fara karantawa.

Nan da nan kanta ya kulle; tabbas wannan sunan Khadeeja ne. To me hakan yake nufi?Suna tare kenan yanzu ta zama bazawararsa ko me? Tunda idan ba wata alaƙa ce tsakaninsu ba me zai saka har ya biya mata kujerar Makka? Kenan ma ita Mustapha zai rainawa hankali, ya saki matar sannan ya koma yana bin ta? Gaskiya ba za ta yarda ba.

Ta ɗaga kanta ta hango wayarsa tana chaji a kan bedside durowa; nan da nan ta ajiye takardun ta ƙarasa ta ɗauki wayar. Ta riga ta san PIN ɗin don haka kai tsaye ta buɗe ta fara duba whatsapp; sai dai har ta gama dubawa ba ta ga sunan Khadeeja ba. Tana duba calls ta ga sunan ‘Sweetheart’ shi ne sunan da ya yi saving lambarta tun yana zuwa zance kuma bai taɓa canzawa ba.

Bayan rabuwarsu Najan ta goge ta saka maman Hammad amma ba ta san yanda aka yi ya mayar ba. Ta mayar da wayar ta ajiye cike da damuwa da takaici. Ta tashi ta dawo ɗaya gefen gadon ta zauna ta zuba tagumi; tabbas za su yi rigima da Mustapha don ba zai yiwu ba ya dinga zagayawa wajen tsohuwar matarsa suna raina mata hankali.

Sai wajen ƙarfe tara na dare ya hawo saman, lokacin ya je sallar isha’i ya dawo kuma sun gama cin abinci da yara. Zuwa lokacin ita ma ta gama duk abinda take yi ta kwantar da yara tana kwance a kan gadon ɗakinsa sanye da rigar bacci ta miƙe kafa tana kallo a waya ya shiga ɗaki. Bayan ta amsa sallamarsa ta mayar da hankali kan wayar hannunta.

Kai tsaye ya wuce ciki ya canza kayansa sannan ya zauna a kan carpet ɗin da ke gaban gadon ya miƙe ƙafa ya janyo computer ɗinsa ya kunna ya kama aiki. Yawanci idan dai har yana da aiki to ya kan kai dare sosai a zaune yana aikin, ita kuma ba za ta iya jira ba. Don haka ta miƙe ta zauna ta ajiye wayar da take hannunta ta yi gyaran murya sannan tace ‘Uhm, na ga wata takarda, wai Maman Hammad ka biyawa Makka?’

Bai yi mamakin jin tambayar daga gareta ba duk da bai sa rai da ita ba, amma dai ya san ya manta ya ajiye takardun a kan mudubinsa. Ba tare da ya bar aikinsa ba yace ‘Eh ita na biyawa, akwai matsala ne. Cike da neman rigima tace ‘To kuma a yanzu meye tsakaninka da ita tunda na ga dai babu aure. Ko kuma kun mayar da auren ne ni ce ban sani ba.’

Har yanzu hankalinsa yana kan aikin yace ‘Ba mu mayar ba muna dai kan hanya. To shi ne kuma ka biya mata Hajji. Ya ɗago ya dube ta yace ‘Eh, akwai matsala ne? ‘Gani dai na yi bai dace ba tunda babu aure a tsakaninku. ‘Wannan ra’ayinki kenan. Ta kula so yake ya yi mata wulaƙanci don haka ta miƙe ta zauna sosai tace ‘Ina fatan dai ka san yanzu ita ɗin ba muharramarka ba ce.

Kuma ina fatan ka san ba zai yiwu ina nan gida ina maka biyayya wai ni matar aure ba ka dinga zagayewa wajen tsohuwar matarka wadda ka saka da hannunka, ba zan ɗauka ba gaskiya.’

Ya ɗago ya kalle ta rai a ɓace yace ‘Sai ki ɗau mataki a kai. Ta kula kamar haushinta yake ji sai dai ba ta san dalili ba, don lafiya ƙalau suka rabu da safe ya ajiye ta a office sannan ya fice; to meye ya harzuƙoshi hakan daga yin magana? Kada fa ka gaya min magana daga tambaya, na dai gaya maka ba zai yiwu ba ina nan ka kulle ni a gidanka a dinga ganinka a gari kana yawo da wata matar banzan.

Ta faɗa tana miƙewa tsaye. A fusace yace ‘Khadeejan kike cewa matar banza saboda wulaƙanci? Sai dai kafin ya rufe bakinsa ta fice daga ɗakin ta rufe masa ƙofar; wanda wannan ɗabi’arta ce idan dai ya ɓata mata rai sai ta gaya masa magana mai zafi sannan take fita daga inda yake. Ya yi tsaki ya cigaba da aikinsa don so yake ya gama aikin kafin ya kwanta.

Haka rayuwarsu ta cigaba. Khadeeja ta ƙi yarda a mayar da aurensu sannan shi kuma ya kasa tunkarar Baffanta da maganar don ya san ba za a yi mata auren dole ba. Amma kuma ya ƙi ya daina bibiyarta; har ta kai ba ya iya sati bai neme ta yaganta ba. Idan ya je gidansu wajen Hammad ta ƙi fitowa to tabbas zai same ta a office. Waya kuwa daman ba ta yankewa don idan ma ta ƙi ɗauka haka zai yi ta kiranta har sai ta gaji ta ɗauka.

Duk wata kalma da zai yi amfani da ita wajen ganar da ita ta yarda su mayar da aurensu ya yi amma ta sanar da shi ba za ta iya komawa ba. Duk lokacin da ta ji kamar za ta haƙura su koma idan ta tuna yanda yake banzatar da ita a gidan kuma ta tuna yanzun ma sai da ya rasa yanda zai yi da gidan sannan ya fara nemanta sai kawai ta ji ta fasa.

Tana sane da duk wata rigima da ta faru a gidan tunda kusan duk Asabar a wajenta Habib yake wuni, duk abinda ya dame shi sai ya je ya same ta ya gaya mata. Lokaci zuwa lokaci tana samun masu nuna sha’awar aurenta sai dai auren gaba ɗaya ya fice mata daga rai; don haka yawancinsu ba ta ma bari su zo gidansu.

Kuma duk inda ta je idan dai ba an santa a wajen ba to tana gabatar da kanta ne a matsayin matar aure don ma kada wani ya zo mata da wata magana; don haka mutanen da suka santa sai suka kasu kashi biyu, wasu suna ganin tana da aure wasu kuma suna ganin ba ta da aure. Amma kuma yawancin mutane kasa tambayarta suke yi.

Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Uku

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Uku
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Ƙarshe
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.