Mijin Marigayiya Babi Na Uku

0
40

khairatu.shehu

Ranar Juma’a suna gida da yake yara babu islamiyya; ranar ne kuma suke gyara gashin yaran mai kitso za ta zo. Tun da wuri Afaf ta tsefe nata kan, ita kuma Shukra da yake tun suna makaranta Khadeejan ta tsefe mata babu wanda ya ji kansu. Tun da suka gama cin abincin rana take faman lallaɓa Nasreen ta bari a tsefe mata amma har aka kusa kiran la’asar guda biyu suka tsefe. Bata  son a taɓa gashinta kwata-kwata don haka ta ƙi ma zama a tsefe.

Khadeeja ta kamo hannunta tace ‘Zo kin ji Nas, kin ga fa Shukra za ta fi ki kwalliya tunda ta tsaya  an gyara mata nata. Ta zauna, har an fara tsifar ta zame kanta ta matsa tana zumɓura baki. Afaf tace ‘Anti wallahi  idan ba ki zare mata ido ba haka za ki yi ta fama da ita, sai a yi sati ana tsefe kanta a gidan Mama.’

Ta cigaba da lallaɓata amma sam ta ƙi tsayawa; don haka ta kama hannunta ta zaunar da ita  tana cewa ‘Idan kika sake tashi sai na zane ki Nasreen, ko na sa almakashi na aske gashin kan  ya koma kamar na Yaya Habib.’ Ta dubi Afaf tace ‘Yaya Afaf ɗauko min slippers mai zafi idan  ba ta tsaya an tsefe ba zane ta zan yi.’

Da sauri Afaf ta ɗauki slippers ta zo ta ajiye a gaba Nasreen wadda ta fara shessheƙar kuka tana  fizge-fizge. Khadeeja ta ɗan riƙe gashin tace zan dake ki fa Nasreen, ki rufe min baki bana son  jin kukanki.’

Nan da nan ta haɗiye kukanta tana shessheka aka cigaba da tsifa Shukra tana mata dariya.

Daga masallacin Juma’a ya wuce gida don ya gaida Hajia, da ya gaishe ta sai ya wuce gida don  Khadeeja tace idan ya dawo zai kai su saloon ita da yara a wanke musu kai da yamma kuma  akwai mai kitso a maƙota dama ita take musu.

Yana shiga gidan ya sami Yaya Jidda da yaranta biyu ‘yan mata Naja da Farida, bayan sun gaisa  gaba ɗaya Yaya Jidda ta dube shi tace ‘Gidanka fa za mu tafi yanzu ni da yara, Hajia tace mu je  mu dubo su Afaf.’

Yace ‘To ai sai ku tsaya mu tafi, don ni ma gaisawa kawai za mu yi na wuce.’  Kafin minti goma sun gama, suka shiga mota ya ja su suka kama hanya, suna tafe suna hira.  ‘To ya yaran? Ana kula da su dai ko?’ Ta tambaye shi.

‘Ah Alhamdulillah, gaskiya tana ƙoƙari.’ Ya faɗa cike da fara’a.To ai haka ake so, Allah ya sa ta ɗore.’ Tun a bakin gate ya yi hon, gaba ɗaya yaran suka fito ban da Nasreen. Habib ya taya shi buɗe  gate, bayan ya shigo da motar gaba ɗayansu suka yi masa sannu da zuwa.

A nan suka fara gaida Yaya Jidda, bayan ta amsa tace ‘Ina Nasreena?’ Afaf tace ‘Tana ciki tsifa Anti Khadeeja take mata.’

Suka wuce gaba ɗaya suka shiga gidan; kafin Khadeeja ta amsa sallamarsu Nasreen ta fizge  kanta wanda saura ɗaya a gama tsefe shi ta tashi tana share hawaye tace ‘Abbaaa.’ ta faɗa tana  zumɓura baki.

Da sauri ya rungumeta ‘Ya haka na ganki wujiga-wujiga? Wa ya taɓa ki?’ Shukra ta tintsire ta dariya ta daga slippers ɗin da aka ajiye tace ‘Kukan tsifa take Abba shi ne  Anti za ta zane ta da slippers, ka ga nawa Anti yalash ɗin ko kuka ban yi ba har aka tsefe yanzu za  mu je saloon amma ban da ita. Anti tace tunda ba ta so a taɓa kanta aske shi za ta yi kamar na  Yaya Habib.’ Sannu da zuwa Yaya.’ Khadija ta faɗa tana karkaɗe jikinta. Yauwa.’ ya amsa ba yabo babu fallasa.

Ta ƙare musu kallo tana ƙoƙarin zama tana cewa ‘To yanzu kuma tsifar ce sai an yi zaniya ni ‘ya  su?’ Kafin Khadeeja tace wani abu Afaf tace ‘Anti wallahi idan aka biye mata sai an yi sati ana wannan  tsifar, kullum haka ake fama da ita.’ Khadeeja tace ‘Ai ba a ma yi zaniyar ba ta bari an tsefe.’ Ta tsuguna ta gaida ita yayin da shi kuma ya ja hannun Nasreen ɗin suka shige ciki.

Sai da ta kawowa Yaya Jidda ruwa sannan ta bi shi ɗakin. Tana shiga ta same shi a tsaye yana  cire kaya yayin da Nasreen take kwance a kan kujerar ɗakin, kafin tace wani abu yace ‘Wai me  yasa ne sai an yi duka sannan za a yi tsifar? Na ga tun tuni dama ana mata kitson ban taɓa ji an  doke ta ba.’ Tace ‘Yanzun ma ba a doke ta ba, ko Nasreen? Ta dai ƙi tsayawa a tsefe ne na takurata na tsefe  mata, amma ba a yi duka ba.’

Ya kawar da kai ‘Ni dai bana son dukan yara, don Allah duk abinda yaro ya yi kada a dokar min shi. Uwarsu ma ba ta dukansu, ba na bari gaskiya.’ Ta sunkuyar da kai cikin ƙosawa tace ‘In sha Allah za a kiyaye.’

Ta ajiye masa ruwan da ta kai masa tana cewa ‘Lunch ɗinka yana nan a table.’ sannan ta fito ta  bar shi a ɗakin.

Bayan ta dawo parlor ɗin ta tarar Yaya Jidda tana ta yi wa Afaf tambayoyi, ta wuce su ta shige  kitchen. Ta tsaya a tsakiyar kitchen ɗin gaba ɗaya kanta ya kulle; daga shigowarsu suna nema suce ta  doki Nasreen, to yanzu haka suke so a bar Nasreen ɗin ta dinga yawo da kanta? Ga shi Afaf tace makarantarsu ana duba kitso duk ranar Monday. Ta jijjiga kai ta ƙarasa ta ɗauki saucer ta zuba  cake da cin-cin ta ɗebo lemo a fridge ta jera a tray ta kawo wa Yaya Jidda da yaranta, bayan ta  ajiye a gabanta tace ‘Ya wajen su Hajiya?’

‘Lafiya ƙalau.’ Ta amsa ba yabo babu fallasa. Suka yi shiru sai surutun Afaf da take ta bawa Naja labari. Shukra ta matso ta kwanta a jikin  Khadeeja tace ‘Anti ni ma lemon.’ Ta shafa kanta ta dubi Afaf tace ‘Yaya ki ɗauko mata lemon wanda babu sanyi.’ Ta miƙe, har ta kama hanyar kitchen ɗin Yaya Jidda tace ‘Ku ba za ku sha lemon ba?’ Afaf tace ‘Ai da shi muka je school.’

Shukra tace ‘Anti tace idan an kawo wa baƙi abinci mutum ya daina cewa zai ci, ni ma dai kawai  lemon zan sha.’ Khadeeja tace ‘Ki ɗauko muku lemon idan kuna so.’

Jimawa kaɗan Abbansu ya fito daga ɗakin ya wuce dining ya zauna ya fara cin abinci; yana cikin cin abincin ya juyo yace ‘Kai Habib kun ci abinci ne?’ Yace ‘Tun ɗazu Abba, acici har ta yi round 2.’ Ya faɗa yana zungurar Nasreen.

Khadeeja ta miƙe ta shige ɗaki, don gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Ta kula ƙiri-ƙiri neman laifinta ake yi; kamar ma Yaya Jiddan zuwa ta yi ta bincike ta. Ta ƙarasa ta zauna a kan gadonta ta zuba  tagumi. Bayan ya gama cin abincin ya shiga ɗaki ya fito da mukullin motarsa, ya dubi Khadijan yace ‘Idan  kun shirya muje na kai ku saloon ɗin.’

Gaba ɗaya suka fice har da su Yaya Jidda, ya ajiye su a hanya sannan ya wuce. Tun daga wannan lokacin kuma sai Yaya Jidda ta mayar da shi ɗabi’a, duk Juma’a sai ta zo gidan.  Haka za ta zauna a parlor ta yi ta ƙare musu kallo tana kula da duk wani motsinsu, ga tambayoyi  waɗanda idan ta gama yi wa yaran za ta bi Khadeeja da neman ƙarin bayani. Sai dai ba ta taɓa  samun wani abu na zargi ba kuma Khadeejan ba ta taɓa ba ta dama ta yi wata fitna ba don duk abinda ta tambaya tana daure zuciyarta ta ba ta amsa gwargwadon iko, kuma cikin girmamawa.

Ranar Talata ce kuma a ranar Khadeeja take sa ran za ta koma makaranta, tun dare ta sanarwa Mustapha. Ya amsa mata ba tare da wata matsala ba.

Haka ta tashi tun kafin asuba ta shirya yaran tsaf, suna tafiya makaranta ta yi maza ta yi wanka sannan ta ɗan rage aiki don tana da lecture 9am. Bayan sun gama breakfast ta miƙe daga dining table tana tattara plates ɗin tana cewa ‘Babe bari na saka hijabi na sai ka yi dropping ɗina a school.’

Yace ‘Ok, but kada ki ɓata lokaci don kada ki makarar da ni.’ Kusan a lokaci guda suka fito daga ɗakin kowa a shirye, sun kawo tsakiyar parlor ta dube shi tace ‘Yau kai za ka ɗauko yara ko? Don ni ina da lectures 9am to 4pm.’

Ya ɗan ɓata rai cikin nuna damuwa yana cewa ‘I thought za ki dawo ki ɗaukosu, kin san ni sai 5pm nake tashi daga wajen aiki.’ ‘To ai ka ga ni ma sai 4pm zan tashi, kuma I can’t miss these lectures don last week ma ka ga ban je ba. Gara dai ka sami wani ya ɗauko su kawai.’

Ya buɗe motar ya zauna yayin da ita ma ta zauna a kujerar gaba, yace ‘To ai ko an ɗaukosu ma wajen wa za a kawo su tunda ba kya gidan?’ ‘Haka ne fa, most days ma lectures ɗina har 4pm ne.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci; gaba ɗaya ma shi ya manta tana wata makaranta. Yanzu ya take so ya yi da yaran? Wa zai ɗauko su kuma wa zai zauna da su? Wannan ai shi ne an gudu ba a tsira ba. Muryarta ce ta katse masa tunani tana cewa ‘Babe ka ga da muna da mai aiki sai ta ɗaukosu ta shirya su su tafi islamiyya kafin na dawo; musamman idan Babba ce.’

Cikin jin daɗi yace ‘Ƙwarai kuwa, zan yi wa Yaya Jidda magana sai a sami mai aikin kafin next week.’ ‘No, ka bari idan na yi wa Mommy magana za ta sa a samo mana a garinsu, mutanen suna da amana sosai ga aiki.’ Ba tare da ya kalle ta ba yace ‘Ki bari tukunna idan aka rasa a wajen Yaya Jidda sai a gayawa Mommy ɗin.’ Ba ta ji daɗin wannan maganar ba kuma ta san da ya kalle ta da zai gane sai dai son zuciyarsa ne a gabansa; don haka sai kawai ta yi shiru. Ba ta son abinda zai haɗa ta da Yaya Jidda don gaba ɗaya matar ta fice daga ranta, ta kula kamar tana neman laifinta ne ido rufe.

A bakin department ƙawayenta Maryam da Jamila suka tare ta, ana ta ihu ana murna ga amaryar Babe. 9am to 11am suka fito daga lecture, wanda zai yi musu 12pm to 2pm ya aiko aka gaya musu ba zai zo ba. Don haka suka wuce hostel ɗakin su Maryam. Suna shiga Khadeeja ta nemi waje ta kwanta, Jamila ta taɓata tace ‘Ke da za ki bamu labarin amarci kuma sai ki kama wani bacci.’

Ta bige hannunta tana cewa ‘Bar ni wallahi baccin da yake kaina ya fi na wata guda.’ Maryam ta yi dariya tace ‘Bar ta Jamila, kin san kwanan ibada take yi.’ Haka suka yi ta hirarrakinsu a kanta tana ta faman bacci. Har suka gama hirarrakinsu tana bacci, don haka ba su tashe ta ba suka fice sayen abinci. Basu daɗe da fita ba ta farka, bayan ta wanke fuska ta yi alwala ta yi Sallah. Ta zauna a kan dadduma tana tunani; tun ba a yi nisa ba ta gaji da auren Mustapha. To amma tana son shi, matsalarta kawai yaransa kuma da yanda ba zai bari ta yi musu tarbiyya ba. Kusan tun da ya kawo mata yaransa ba ta huta ba, wannan baccin da ta yi ji ta yi kamar an ɗauke wani dutse da ta daɗe tana dakonsa. Ko ina a jikinta ciwo yake, fatan ta kawai a samo mai aikin nan ko za ta huta. Duk da tana tsoron a kawo mai aiki daga gidan Yaya Jidda; gani take kamar CCTV camera ce kawai za a kawo mata.

Tana zaune tana wannan lissafin wayar Yaya Mama ta shigo; bayan sun gaisa tace ‘Ya na ji ki haka ne amarya? Ko bacci kike yi ne?’

‘Wallahi ina hostel Yaya, kin ganni gyangyaɗi na gama.’ ‘To ya maganar mai aikin, tunda dai gaskiya aikin gidan nan ya fi ƙarfinki ga yara huɗu.’

‘Ya ce yayarsa za ta kawo mai aikin.’ ‘To ai shikenan, duk ɗaya ne. Kawai dai idan ta zo sai ki sa ido, kada ki bari ta shisshige miki; ke ko a cikin gidan ki kula kada ki kuskura ki dinga barinta tana shigar miki ɗaki, kitchen da store ma duk ki kula da motsinta. Yaran ma ki dinga kula da alaƙarta da su idan ba haka ba sai ta zame muku fitna.’ Yaya Mama ta faɗa.

Cikin sanyin murya tace ‘To Yaya.’ Yanda ta ji muryarta bai gamsar da ita ba tace ‘Ko da wata matsala ne?’ No, ba wani problem. Ni ga ni ma a school na dawo sai yamma zan koma gidan.’’Ok, Mommy ma tace min kun je weekend ke da yaran naki.’ ‘Eh.’ Suka dan taɓa hira daga baya suka yi sallama suka ajiye wayar.

Khadeeja ta bi wayarta da kallo kawai sai ji ta yi tana hawaye; ta yi kewar gida sosai, gaba ɗaya a yanzu ma ba ta san me take so ba, kawai dai ta gaji. Motsin su Maryam ya sa ta share hawayenta ta basar.

Kwana biyu da yin maganar kuwa sai ga mai aiki; dattijuwa ce Baba Habi. Yaya Jidda da kanta ta kawo ta. Sai da ta tafi sannan Khadeeja ta nuna mata ɗakin yara inda a nan za ta dinga kwana.

Ta nunnuna mata ayyukan kafin yaran su dawo daga islamiyya. Nan da nan ta fara ba tare da nuna wata kyuya ba, ga shi tana da hanzari wajen yin aikin.

Yan kwanakin nan gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikinta, gaba ɗaya ba ta san me yake damunta ba. Ranar Laraba ce, tana jin Mustapha yana tashinta daga bacci kafin asuba yana cewa ‘Ki tashi yara za su makara fa.’ Ta juyo tana yamutsa fuska tace ‘Babe bana jin daɗi wallahi, daga kwancen nan ma ni jiri nake ji ga headache. Bana jin zan iya tashi yau.’

Ya miƙa hannu ya taɓa jikinta yana cewa ‘Subhanallah, me yake damunki?’ Ni ma ban sani ba, ta amsa muryarta na rawa. Ya matsa ya leƙa fuskarta, sai kuma ya sauka daga kan gadon yana cewa ‘Bari na gama da yara sai na kai ki asibiti, amma ki daure ki tashi ki shirya.’

‘To, ka bari gobe ma je asibitin mana.’ No, yau za mu je kin ga ana maganar za a saka lockdown saboda COVID 19 idan aka rufe ban san lokacin da za a buɗe garin ba. Gara mu je mu gama komai a siyo miki magani yanzu haka malaria ce.’ Ya faɗa sannan ya fice daga dakin.

Baba Habi ce ta shirya yaran, duka da kasancewar ita ba ta iya girki ba haka suka haƙura Afaf ta nuna mata ta dafa musu indomie. Bayan sun sha shayi da burodi ta zuba musu indomie a lunchbox. Duk yanda ya so ya koma baccin bayan asuba ranar haka ya hakura ya zauna a parlor ɗin yana taya su shiryawa. Bayan ya kai su makaranta ya dawo ya shirya, ya taimakawa Khadeeja ita ma ta shirya suka wuce asibiti suka bar Habi a gidan.

Suna zuwa likita ya tabbatar musu da cewa ciki ne da ita, aka ba ta magungunan suka taho. Kafin su isa gida sai da ya siyo magungunan, suna dawowa ya miƙawa Baba Habi magungunan ya yi mata bayani. Ya shiga ɗakini inda Khadeeja take kwance ya tsaya a kanta yace ‘Ki daure Habi ta haɗa miki abinci ki ci ki sha magani, shi ne za ki ji daɗin jikinki. Kin ga waɗannan magungunan ita Ma’u idan tana sha ko laulayin kirki ba ta yi, haka take ci gaba da harkokinta har ta haihu.’

‘Yanzu zan fito ai.’ Ya yi mata sallama ya tafi office. Indomie ɗin dai Baba Habi ta dafa mata sannan ta shiga ɗakin ta taso ta, ta sha maganin ta ɗan ci abinci sannan ta koma ta sake kwanciya. Kafin Habi ta ɗauko yara daga makaranta ta ɗan ji ƙwari, zuwa dare rashin ƙwarin jikin ya ragu don da kanta ta lallaɓa ta yi musu tuwo miyar kuka. Kwana biyu laulayin ya yi wa Khadeeja sauƙi don tana dagewa tana shirya yara makaranta kuma tana shiga kitchen ta yi abinci da taimakon Baba Habi.

Ranar laraba suna zaune a parlor da magriba ita da yara da Abbansu; tana zaune a tsakiyarsu tana yi musu homework yayin da shi kuma Abbansu yake zaune a kan kujera yana ta faman danna waya yana kuma kallon labarai a BBC. Baba Habi ta fito daga dakin yara da sallama, bayan Khadeeja ta amsa sallamarta ta tsuguna daga gefe ta dubi Khadeeja tace ‘Uwar dakina ina so zuwa gida gobe, na ji an ce za a kulle garin. Zan je na dubo yarana idan na kwana ɗaya sai na dawo kafin a rufe garin.’

Abbansu ya ɗago kansa daga kallon wayar yace ‘Baba ai da kin bari mu ga abinda hali zai yi tunda kin ga ita ma Khadeejan ba ta da lafiya.’ Ta juya Kai ‘To ai Yallaɓai kafin a kulle garin, na baro yara gara na je na dubo tunda ana maganar idan an rufe garin za a yi watanni kafin a buɗe.’

Kafin ya yi magana Khadeeja ta dube shi tace ‘Ka bari ta je ai na ɗan ji sauƙi, gara ta je ta dawo kafin a rufe garin ga azumi ma yana tahowa.’ ‘Haka ne.’ Ya amsa ya cigaba da abinda yake yi.

Gari yana wayewa bayan ya dawo daga kai yara makaranta ya ba wa Baba Habi kuɗin mota Khadeeja kuma ta haɗa mata abin da za ta ba ta ta kama hanya a kan jibi za ta dawo.A ranar da daddare aka sanar da total lockdown a Nigeria, an hana duk wata zirga zirga sai dai kowa ya zauna a gida a ga abinda hali zai yi.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na biyu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTa’aziyyar Hauwa Ƙamshi
Labarin na GabaAsalin Yadda Aka Samo Sunan Hausa Bakwai Da Banza Bakwai
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.