Mijin Marigayiya Babi Na Huɗu

0
53

khairatu.shehu

Da farko Khadeeja ta yi tunanin idan ta sami ciki Mustapha zai yi ɗoki kuma ya ba ta kulawa ta musamman kamar ko wacce amarya, sai dai ga mamakinta hakan ba ya samuwa. Wani lokacin ma sai ta ga kamar bai san ma tana da ciki ba ko kuma ba da son ransa ta sami cikin ba; halin ko in kula ɗin da yake nuna mata ya yi yawa.

Tunda aka saka lockdown sai ya zamana kullum suna gida ita da shi da yara, ta so sosai ta je gida ta wuni kafin a kulle garin amma ba ta sami dama ba. Duk da haka kullum sai sun yi waya da Mommy da Yaya Mama; don tun satin da za a fara lockdown su Nabila suka zo mata wuni da suka je gida suka gaya wa Mommy ciki ne da ita. Don haka kullum da safe sai ta kirawota ta duba ta.

Hayaniyar da su Afaf suke yi a gidan ba kaɗan ba ce don haka idan gari ya waye ko gyangyaɗi ba ta samu ta yi; ko ta fara baccin ma haka za a yi wata hayaniyar a tashe ta. Ba ta gane yanayin da jikinta yake ciki, ita dai kawai ta san tana shan wahala. Kullum jikinta babu ƙwari ga shi ba ta son cin abinci, ga shi kullum cikin jin bacci take. Ga hidimar yara, wadda duk ranar da ta nuna ba za ta iya ba haka Mustapha zai yi ta ƙunci yana kin kula ta.

Haka take dagewa ta yi duk wani abu da ya kamata. Kullum wuni suke kallon TV saboda ana samun wuta sosai, idan dare ya yi kuma Abbansu ya tada inji su cigaba da kallo. Ita dai ba ta isa ta canza channel ba don da ta canza za a fara kuka wanda ba ta son ji sanna kuma a take ubansu zai fito ya yi magana. Ta gaji da zaman haka barkatai don haka ta daure take saka yaran a gaba su yi karatun kur’ani.

Da safe a jagwale take tashi don haka ta san ba za ta iya da safe ba. Amma kullum bayan sallar azahar idan sun ci abincin rana sai ta kashe TV ɗin kowa ya ɗauki kur’ani ta biya masa. Nasreen ce kawai ba ta son zama don haka sai Khadeeja ta ƙyale ta saboda a halin yanzu ba za ta iya ba. Amma har Shukra ake biyawa karatun.

Duk wani motsinsu idonsa a kai, da zarar ya ji wata hayaniya ko ya ji su shiru zai leƙo ya duba. Kullum yana kwance yana faman latsa waya. Yau ma haka suka tashi tun asuba suke ta guje-guje, TV kuma dama tana kunne don da zarar wani ya kashe ta za a yi ƙorafi. Shinkafa da wake ta dafa da manja da yaji; bayan sun gama cin abinci kowa ya yi Sallah ta saka su a gaba kowa da kur’aninsa. Sai da suka yi tilawa sannan ta ƙarawa kowa aya biyar amma banda Nasreen.

Ba za ta iya surutu ba saboda yanayin jikinta da kuma yanda yawu yake yawan taruwa a bakinta, sannan kuma idan ta ɗaga murya tana mata faɗa Abbansu ba ya so. Don haka sai ta ƙyaleta, suna zaune gaba ɗayansu sun kewaye Khadeeja suna karatu, har da Shukra; amma Nasreen tana zaune a kan kujera ta zuba kayan wasa a gaba tana yi wa ‘yar tsanarta kitso.

Shiru ya ji sai muryoyinsu kaɗan-kaɗan suna karatu don haka ya taso ya fito parlor ɗin. Ya kare musu kallo sannan ya sami waje ya kwanta a kan 3-seater. Ya dubi Khadijan yace ‘Ita Nasreen ba a biya mata karatun?’ ‘Tace sai ta gama yi wa ‘yar tsanarta kitso.’ ta ba shi amsa ba tare da ta dube shi ba. Nasreen tace ‘Na ma iya karatun Abba, kitson nan nake so na gama tukunna.’

Ya yi dariya ya cigaba da danna wayarsa. Bayan sun gama karatun ta koma ɗaki ta kwanta su kuma suka cigaba da kallonsu na TV.

A kwance take a gefen gadon da alawar tomtom a bakinta saboda yawu, ya zauna a kan kujera. Ta juyo ta kalle shi ta koma ta cigaba da kwanciyarta don ba ta son magana. Jimawa kaɗan ya kirawo sunanta, ta amsa sannan ta juyo. Ya kalle ta yace ‘Wai me yasa bakwa karatun ne da Nasreen?’ Tace ‘Bata so ne, ni kuma ba daɗi nake ji ba shi yasa ba zan iya surutu da ita ba kawai na kyale ta.’

‘Ya kamata idan ma wani abu kika saka a ranki game da Nasreen ki cire, duk abinda za ki yi wa yaran nan ki yi musu gaba ɗaya kuma ki yi musu adalci. Ina kula komai za ki yi sai ki ƙyale Nasreen, idan banda haka ya za a yi a ce Shukra ma da ba ta shiga islamiyya ba kina biya mata karatun amma ita Nasreen kin yi banza da ita.’

Tun da ya fara zancen ta miƙe ta zauna a kan gadon tana kallonsa, maganganun da take so ta faɗa masa suna da yawa sai dai tana buɗe bakinta yawu ya cika bakin. Ta taune ‘yar guntuwar tomtom ɗin ta haɗiye da ƙyar, ta taɓe baki ta kawar da kai kawai tace ‘Ka yi hakuri za a gyara.’ ‘Ya kamata dai ki dinga yi musu adalci don dukansu ‘yayana ne.’ ya faɗa.

Ta zame ta kwanta zuciyarta har turiri take saboda takaici; shi yake hanata takurawa Nasreen, shi yake nuna ba ya son a dinga yi musu faɗa amma kuma yanzu yana mata maganar ba a karatu da ita. To ya za ta yi da ita? Ita adalci ne wannan yake mata da zai ce ta dinga yi wa ‘yayansa adalci? Ta share ƙwallar da ta gangaro a idonta tayi ƙwafa. Jimawa kaɗan ya tashi ya fice daga dakin.

Wannan wunin da kowa yake yi a gida ba ƙaramin takurawa Khadeeja yake yi ba; tana cikin laulayi sannan ga hidimar gida da ta yara. Wuni suke cin abinci don haka gidan kullum kaca-kaca ga wanke-wanke ba ya yankewa. Wasu lokutan tana samu ta ɗan gyara amma wasu lokutan haka take ƙyalewa saboda ba za ta iya ba.

Yau kwana biyu kenan dan almajiri da ta ɗauka yake zuwa ya yi mata wanke-wanke da sharar tsakar gida bai zo ba; ba ta sani ba ko suma lockdown ɗin ya shafe su don da dai suna fitowa tunda makarantarsu nan cikin unguwa take. Gidan gaba ɗaya yayi kaca-kaca don kitchen har warin lalatacce abinci yake yi.

Suna gama cin abincin safe Abbansu ya miƙe ya shige ɗaki. Nan da nan ta saka yaran a gaba suka taya ta suka fitar da wanke-wanken suka kai fanfon waje, ta turasu waje ta gyara cikin gidan tsaf. Tana yi tana hutawa tana tofar da yawu, zuwa ƙarfe goma na safe ta gama.

Ta fito tsakar gidan ta tara yaran a waje ɗaya, ta dube su tace ‘Afaf mu je fanfo ni da ke mu wanke kwanukan can, kai kuma Yaya Habib ɗauki tsintsiya ka share compound ɗin nan, ka fara daga kan baranda. Nasreen da ke da Shukra ku tsince toys ɗinku ku zuba a kwando, duk wadda ba ta tsince ba ba zan ba ta sweet ba.’

Nan da nan kowa ya fara aiki. Ta saka kujera a bakin famfo tana wanke kwanukan Afaf tana mata ɗauraya. Sai da suka cika ƙaramin kwando da kwanukan ta kirawo Habib wanda ya kusa gama sharar tace ‘Ya Habib zo ka ɗauki wannan kwandon ka kai kitchen ka kwashe kwanukan a kan sink sai ka dawo da kwandon mu cigaba da zubawa.’

Ya ɗauka a nufi cikin gidan; a kan baranda suka ci karo da Abbansu yana fitowa. Ya ɗan ja baya don ya ba wa Abban hanya ‘Kai ina za ka da kwanuka haka.’ ‘Anti ce ta wanke zan kai mata cikin gida.’ Yana ɗaga kansa ya hango Afaf a tsakiyar kwanuka suna ta wanke-wanke ita da Khadeejan. A fusace ya ƙarasa wajen, cikin tsawa yace ‘Ke Afaf me kike a nan? kalli yanda kike jiƙa jikinki sai kin gama ki yi ta mura.’ Ya dubi Khadeeja yace ‘Ina yaron naki?’

Ta tofar da yawun bakinta a gefe sannan tace ‘Kwana biyu bai zo ba, ni ma ban san dalili ba.’ Ya dubi Afaf wadda ta cigaba da aikinta ba tare da ta kula da shi ba, ya daka mata tsawa yace ‘Ki fita daga cikin ruwan nan nace, me kika iya? Sai sanyi ya kama ki kina ta faman jiƙa jiki. Fice ki je ki canza kaya kuma kada ki sake fitowa nan.’Ta dube shi tace ‘Kwanukan ne da yawa, ni ɗin kuma ba daɗi nake ji ba idan muka gama gaba ɗaya za ta canza kayan ai.’

Habib ya ƙaraso ya ajiye kwandon yana cewa ‘Anti ga shi.’ Ya juya ya cigaba da shararsa. Abbansu ya sake dakawa Afaf tsawa don haka ta fice daga wajen wanke-wanken ta shige gida. Har ya buɗe baki zai cigaba da magana ya hango Habib yana kwashe shara ‘Kai Habib wa ya saka sharar nan?’ Yace ‘Anti ce Abba, ai na ma gama kwashewa zan yi.’

‘Ajiye tsintsiyar nan ka shige cikin gida ka ba ni waje.’ ya faɗa a fusace. Ya jefar da tsintsiyar ya shige gidan. Ya juya kan Khadeejan wadda take cigaba da wanke-wankenta yace ‘Wai me kika mayar da yaran nan ne? Habib ne zai iya share wannan tsakar gidan ga ƙura ga komai. Ita ma Afaf ɗin wannan uban ruwan ai sai ta yi mura. Ke kika ce a bar mai aikinki ta tafi gida, da kin bari ai da yanzu tana nan; sannan kuma ki dinga ba su aikin da ya fi ƙarfinsu?

Ba na son irin wannan; ba na son ki dinga yi wa yaran nan kallon wasu manya, ki ɗauke su kamar ke kika haife su shi ne za ki iya yi musu adalci. Idan an ji wani almajirin yana bara sai a kirawo shi ya ƙarasa wannan aikin ko kuma tunda kun kusan gamawa ki ƙarasa zuwa gobe a sami wani almajirin.’ Ko kallonsa ba ta yi ba ta cigaba da wanke-wankenta, ya ja tsaki ya juya ya nufi cikin gidan.

Ta share hawayenta ta cigaba da wanke-wankenta. Ba za ta iya dogon surutu ba sannan kuma ba ta son tana biye masa suna faɗa a gaban yara, ita yanzu duk wani abu da zai sa a yi magana ma ba ta so; shi yasa ta gwammace ta yi masa shiru. Sai da ta gama wanke-wanken nan tsaf sannan ta kwashe sharar, ta ɗebi kwanukan ta shigar cikin gida.

Suna zaune a parlor suna kallon TV. Tana kitchen ɗin tana kife kwanukan Afaf ta shigo ta same ta, ta ɗauki kwanukan ta fara kifewa. Ta dube ta tace ‘Afaf je ki zauna ai na kusa gamawa.’ Tace ‘Bari na taya ki Anti, ai nan babu ruwa.’ Ba don ta so ba ta ƙyale ta sai da suka kife kwanukan gaba ɗaya ta mayar da komai inda yake sannan ta wuce ɗaki su kuma suka cigaba da kallonsu. Can wajen 1pm bayan sun yi sallar azahar ta fito daga ɗaki ta shiga kitchen; tuwon alkama da miyar ɗanyar kuɓewa ta dafa jiya da daddare amma duk sai suka ƙi ci.

Da yake akwai biscuits da cake sai kowa ya ci ya sha lemo, ita da abbansu ne kawai suka ci tuwon ga shi ta dafa shi da yawa. Da safe kuma da kwaɗayi ta tashi don haka wainar fulawa ta soya kowa ya ci. Wannan ragowar tuwon shi ta ɗauko daga fridge ta ɗumama shi, ta ɗumama miyar wadda ta sha kaza da nama. Ta zuba wa kowa abincinsa sannan ta kirawosu kowa ya ɗauki nasa suka zauna a table.

Kallon tuwon kawai Habib yake yi yana juya shi amma ya ƙi ya fara ci, tana kallonsa ta yi banza da shi ta cigaba da kai lomarta tana ba wa Shukra don ita tuwon ya yi mata daɗi. Jimawa kaɗan ya dube ta yace ‘Anti tuwon jiya ne fa?’ ‘Eh, shi ne, ko ci ko bari.’ ta faɗa a gajarce ta ci gaba da cin abincinta.

Daidai nan Abbansu ya fito ya zauna a table ɗin, ta tura masa flask da plate. Ya buɗe flask ɗin ya kalli fuskokin yaran sannan ya kalle ta yace ‘Wannan ai tuwon jiya ne, ba a yi abincin ranar ba ne?’ ‘Shi ne abincin ranar ai, ɗumamawa aka yi tunda babu abinda ya yi.’ Nasreen wadda ita ma take ta juya nata tuwon tace ‘Abba wallahi tuwon ba daɗi, ni bana son baƙin tuwo gaskiya.’

Shi ɗin yana son tuwon alkama don shi ne ma ya sa aka yi tuwon da daddare, don haka ya zuba malmala guda ya fara ci. Ya sake duban fuskokin yaran, bayan ya haɗiye lomar da take bakinsa yace ‘Yanzu ba wani abu da za a iya dafawa yaran nan, Afaf ce kawai take cin tuwon nan.’ Ba tare da ta kalle shi ba tace ‘Babu.’

Ta cigaba da cin tuwonta kamar ba ta san da su ba a wajen. Jimawa kaɗan Nasreen tace ‘Abba ni a haɗa min cornflakes.’ Ya dubi Khadeeja yace ‘Akwai cornflakes ko?’ Cikin halin ki in kula tace ‘Akwai.’ ‘Da Allah a haɗa mata ta samu ta ci kafin a yi abincin dare.’ Tace ‘To.’ Ta ci gaba da cin tuwonta tana ba wa Shukra a baki, yayin da ita kuma Nasreen ta tashi ta koma gaban TV.

Jimawa kaɗan Habib ma ya mike, ya ɗauki kwanonsa da na Nasreen yana cewa ‘Abba ni ma na sha cornflakes ɗin kawai. ’Ya wuce ya kai kwanukan kitchen ya dawo shi ma ya zauna a gaban TV. Bai daɗe da tashi ba kuma ita ma Khadeejan ta gama cin nata tuwon, ta ɗauke kwanonta ta kai kitchen. Ta fito daga kitchen ɗin ta wuce ɗaki ba tare da ta kalle su ba. Tana shiga ta saka pillow ta kwanta a tsakiyar gadonta, da yake ta gaji sannan kuma ta koshi tana rufe ido bacci ya kwashe ta.

Ba ta sani ba ko ta daɗe da kwanciya ko ba ta daɗe ba, kamar a mafarki ta ji Mustapha yana ɗan buga ƙafarta yana cewa ‘Khadeeja, Khadeeja, barci ma kike yi? Kin bar yara da yunwa fa ki zo ki haɗa musu cornflakes ko ki dafa musu indomie.’ Ta ɗan janye kafarta tana ƙoƙarin tashi; kafin aurensu fa ba ya kiran sunanta sai dai yace ‘yan mata, mekyau ko kuma yace babe.

Ta yi zaton idan sun yi aure next level za su shiga a ƙara mata matsayi amma za ta iya cewa tunda ta shigo gidan nan sau ɗaya ya kirawota da babe a daren da suka tare. Yanzu kam ya ci dubu sai ceto don gatsal yake kiranta Khadeeja. Ta gyara zama tace ‘Me kake cewa?’

‘Ba ki ba wa yara abinci ba kin zo kin kama bacci.’ Tana jijjiga kai tace ‘Kowa fa na ba shi abinci ba ka gani ba ne?’ ‘Habib da Nasreen nake magana fa.’ ‘Oh, ba sun ce cornflakes za su sha ba, ai akwai a kitchen ɗin.’ ta faɗa tana ƙoƙarin kwanciya. ‘To ai sai ki zo ki haɗa musu ko?’ Ta gyara kwanciyarta a cewa ‘Wallahi babe na gaji, idan ban yi baccin nan ba ko abincin dare ba lallai na iya dafawa ba.

Su je su haɗa cornflakes ɗin mana ko su ci tuwon da kowa ya ci.’ ‘Ya ina miki magana kina kwanciya Khadeeja, haka za ki bar min yara da yunwa.’ ya faɗa a fusace. Ta gyara kwanciyarta ta yi banza da shi. ‘Ina miki magana kina ji na fa Khadeeja bana son wulaƙanci.’ Ta tashi zaune, lokacin ya riga ya miƙe tsaye. Ta gyara zama tace ‘To me zan ce maka?’ ‘Ba za ki zo ki haɗa musu cornflakes ɗin ba kenan?’

‘Haɗa cornflakes ɗin ba wani aiki ba ne shi yasa nace su haɗa kawai, wallahi kaina ciwo yake.’ Ta ture abinda ta rufa da shi ta sauko daga kan gadon ta wuce banɗaki saboda yanda bakinta ya cika da yawu, ta mako kofar banɗakin ta tsaya a gaban sink; wallahi babu wani abinci da za ta haɗa sai dai ya yi duk abinda zai yi. Tana ji Nasreen ta leƙo tace ‘Abba yunwa nake ji.’

Ya ja tsaki ya kama hannun Nasreen suka fice daga ɗakin bayan ya maka mata kofar a fusace. Haka ya je ya haɗawa yaran cornflakes ɗin suka zauna suka ci. Tun da ya haɗa musu cornflakes ɗin nan kuma sai ya shiga share Khadeeja, gaba ɗaya ya ƙi kula ta ko zama inda take. Ta kula da hakan don haka ita ma sai ta ja jikinta, domin ba ta cikin yanayin ma da zata iya saurarensa.

Ko da dare ya yi ma har ta kwanta a ɗakinta sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, tunda dai bai kore ta ba kuma ita ba fushi take yi da shi ba shi kaɗai yake fushinsa. Don haka bayan ta kwantar da yara sai ta shirya ta wuce ɗakinsa ta kwanta. Can wajen sha biyun dare motsin shigowarsa ya tashe ta, yana tsaye a gaban wardrobe yana saka kayan bacci. Ta sauko daga kan gadon ta wuce banɗaki don ta yi fitsari ta kuskure baki.

Tana fitowa ta wuce ta kwanta, ta kalle shi yana zaune a gefen gadon yana dannan waya; so take ta ce masa “good night Babe” kamar yanda ta saba amma bakinta ya ƙi furtawa saboda yanda take cike da haushinsa. Don haka sai kawai ta juya masa baya ta kwanta. Kamar wanda yake jira ta kwanta sai ya gyara zama a kan gadon yace ‘Tashi mu yi magana Khadeeja.’

Ta juyo ta kalle shi sannan ta tashi zaune ta jingine da jikin gadon; tana baƙin cikin yanda yake kiranta Khadeeja gatsal sai kace shi ya yanka mata ragon suna. Bayan ta zauna ya ƙara tsuke fuska sannan yace ‘Bana son yanda kike yi min taurin kai da neman kawo min raini a gaban yara, idan ma wani abu ne a ranki gara ki fito ki gaya min.’ Da mamaki take kallonsa don gaba ɗaya ma ta manta me ya kawo wannan maganar; ta yi zaton ma zai tambaye ta dalilin da yasa ba ta ci abincin dare ba ne domin taliya ta dafa kuma ta kasa ci don haka ruwa kawai ta sha ta kwanta.

Ta yi murmushin yake tace ‘To, sai dai ban san lokacin da na yi maka taurin kan ba.’ ‘Dazu nace ki haɗawa Habib da Nasreen cornflakes kin ƙi, nan kika shige banɗaki kika bar ni a tsaye ina miki magana.’ Ta kalle shi suka haɗa ido ta kura masa ido har sai da shi ya kawar da kansa, ta buɗe bakinta wanda ya fara tara yawu tace ‘To in sha Allah zan kiyaye, amma ni ma don Allah ka dinga sauƙaƙamin rayuwa a gidan nan. Idan ba ka yi min saboda ƙauna ba to ka yi min saboda yanayin da nake ciki tunda ni ma ba lafiya ce ta ishe ni ba duk abinda ka ga ina yi daurewa nake yi.’

Ya ɗan fara saukowa yace ‘Duk don na nema miki sauƙin ne ai nace a kawo mai aiki, kuma da ta dawo za ta cigaba da taya ki. Ita ma mahaifiyarsu haka take kula da su ko da kuwa tana da ciki don wannan ba wani abu ba ne a wajen macen da ta san me take yi. Bana son ki dinga yi musu abubuwan da za su ji maraicin uwarsu, ki riƙe su kamar ke kika haife su. Shi ne abinda zai samar da zaman lafiya tsakanin mu.’

Ta gyaɗa kai tana kallonsa cike da tsananin mamaki tace ‘To.’ Ta sauka daga kan gadon ta shiga banɗaki ta tofar da yawun bakinta ta ɗaurayo bakinta ta fito ta kwanta bayan ta kashe fitila. Tana kwanciya hawaye ya fara bin idonta; wannan wace irin rayuwa ce? Wai dama haka ake aure ko kuwa ita ce ba ta dace ba? Shikenan shi da ‘yayansa ne kawai mutane? Ƙiri-ƙiri sai a ƙirƙiri laifi a ɗora mata kuma a saka ta ba da haƙuri.

Da ya bar ta da yaran tabbas ta yi niyyar ta riƙe su kamar ita ta haife su, domin har addu’a take yi kada Allah ya ba ta ikon cutar da su. Sai dai zuwa yanzu gaba ɗaya sun fice daga ranta, duk wata ƙauna da ta tana da don ta nuna musu ba ta jin za ta iya tunda ga dukkan alamu ma ba zai bar ta ba. Shi ba so yake ta nuna musu ƙauna ba so yake kawai ta bauta musu, ba ta jin za ta iya hakan kuwa.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Uku

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Razana A Cikin Barci
Labarin na GabaMalamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.