Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Uku

0
26

Ba a daɗe da sallacewa ba kuma aka buɗe gari, a hankali kowa ya koma harkokinsa. Ranar Lahadi da daddare bayan yara sun yi bacci; suna zaune a parlor shi yana kallon ball a TV yayin da ita kuma take chatting a waya; ta ɗago daga kallon wayar ta dube shi tace ‘Babe gobe fa za a koma makaranta.’

Ba tare da ya ɗauke kai daga kallon TV din ba yace ‘Kin gaya min fa tun last week, kuma na siyo duk wani abu da ake buƙata. Ta gyara zama ta ajiye wayar tace ‘Ni ma zan shiga school ɗin na gano, wata ƙila an kafe timetable, amma sai wajen goma zan fita.’
‘Ok, to za ki dawo kafin 12:30pm kenan ko? Saboda ɗauko ‘yan makaranta tunda ni kin ga ina office.’

‘Eh, zan yi ƙoƙari na dawo kuma idan ban dawo ba ma kafin na fita zan je da Rashida ta ga makarantar tasu idan lokaci ya yi ban dawo ba sai ta je ta ɗauko Nasreen. Ya gyara zama ya kalle ta kamar a firgice ‘Wai wannan yarinyar ce za ta dinga ɗauko yaran daga
makaranta kuma ta zauna ta zauna da su a gidan ita kaɗai?’

Cikin halin ko in kula tace ‘To ya za a yi, ai ka ga dai ni ma dole na je makaranta ko? They will be fine fa, yarinyar tana da hankali sannan kuma ka ga ga Afaf tana nan idan ta dawo. Su ma ita da Habib na gaya musu idan an tashi daga makaranta su taho tunda na ga ko ni ce ma na je ɗauko su idan muka rasa napep a ƙasa muke tahowa.’

Ya ƙare mata kallo sanna yace ‘Wai me kike faɗa ne? Su Afaf ɗin ne kike so su dinga tahowa daga makarantar su kaɗai kuma a ƙas, sannan har da Nasreen? Wadda sai an tashe ta da minti talatin sannan a tashe su? To babe ya za mu yi? Ai ka ga dai kamar Afaf ba shi da wani amfani a ce sai Rashida ta je sannan za su taho tare ko?

Ni kuma duk lokacin da ta kama ina gidan zan je na ɗauko su. Suka yi shiru na ɗan lokaci kowa da abinda yake tunani. Jimawa kaɗan yace ‘Ni barin wannan yarinyar taki ma a gidan ita kaɗai gaskiya bai yi min ba, ya za a yi duk mu fice a barta ita kaɗai kuma a bar mata mukullin gidan? Ai idan muka dawo sai abinda muka gani kenan, za ma ta iya fara shigo da maza gidan ko a yi mata wayo a yi mana ɓarna idan aka gane ita kaɗai ake bari a gidan.’

‘To yanzu ya kake so a yi? Ka ga dai da ni da yaran ai dole duk mu je makaranta ko?’
‘Ni ma ban sani ba, kece za ki san yanda za ki yi. Za ki ma iya fita da ita ki rufe gidan in ya so sai ku dawo tare ki ɗauko yaran, duk yanda dai kuka yi. Amma dai gaskiya wannan tsarin na barinta a gidan bai yi min ba.’

Ranta ya fara ɓaci; me yake nufi ne? So yake yace ta bar makarantarta kawai saboda ta zauna masa da yara ko kuwa mai aikin yake so ya korar mata? Wannan bayanin da yake yi ma sam ba zai yiwu ba gara dai ya sake lissafi ko kuma shi ya dinga baro office yana zuwa yana ɗauko su.

Tace ‘Uhm, to ai ka ga ba ni nake rubutawa kaina timetable ba, wani malamin ma sai 1pm yake fara lecture kuma dole na yi attending idan dai ina son na gama degree ɗin. Sai dai ko ka kawo wata dabarar da kai kake ganin za a yi da ɗauko su in ya so ita Rashida idan zan fita sai na fita da ita duk lokacin da na gama lecture sai mu dawo tare.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan ya tashi ya jefar da remote ɗin TV ɗin da yake hannunsa ya shige ɗaki. Ta bi bayansa da kallo tana mamaki; wai me mutumin nan yake nufi ne? Shikenan sai ta jingine rayuwarta ta zauna ta kular masa da yara? To ai ita ko ‘yayan da ta haifa ma haka ko tana so ko ba ta so za ta dinga barinsu da mai aikin ta tafi makaranta tunda dai haka ta ga masu yaran suna yi.

Ko kuwa da yake ta auri tuburarre haƙura za ta yi da komai ta zauna sai yanda suka yi da ita? Haka suka kwana a wannan daren kowa da abinda yake ransa. Ko da gari ya waye tun asuba ta tashi ita da Rashida wadda ta taya ta nan da nan suka shirya
yara sannan suka haɗawa kowa abinci.

Kamar yanda ya saba sai ƙarfe bakwai da kwata sannan ya fito, zuwa lokacin sun shirya suna jiransa; ya kwashe su ya kai su ya dawo. Sai wajen ƙarfe tara da rabi sannan ya gama shirinsa, lokacin fitowarta kenan daga wanka saboda sai da ta tsaya ta gama abincin rana ta juye a flask sannan ta fara shirin. Ya same ta a ɗaki tana shafa mai riƙe da mukullin motarsa, yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Ni na fita.’

Ta juyo da sauri tana cewa ‘La! Babe don Allah bari na yi sauri na saka kayana sai ka ba ni lift. No ba ta hanyarku zan bi ba, ki wuce kawai sai na dawo. Kada ki manta min da yara.’ Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin. Ta bi bayansa da kallo da baki buɗe; lallai ma mutumin nan.

Ƙiri-ƙiri dai shi baya son ya ɗauke ta a motarsa idan dai makaranta za ta, in banda haka ai ko ba hanyar makarantarsu zai bi ba ya sauke ta a bakin titi ya rage mata tafiya. Ta juya ta cigaba da shiryawa cikin sanyin jiki tana tunanin son kai irin na Mustapha. Allah ya so ta ma Baffa magana ya tura mata kuɗi kuma ya sanar da ita duk wata zai dinga turo mata kuɗi saboda karatunta, idan tana son wani abu sai ta yi masa magana.

Tabbas ta san da a ce da Mustapha ta dogara da sai dai ta haƙura da karatunta ta zauna ta kular masa da yara. Nan da nan ta ƙarasa shiryawa ta fito ta sallami Rashida wadda ta bar su tare da Shukra bayan ta yi mata duk wani bayani da take buƙata sannan ta kama hanya zuciyarta cike da damuwa da wasi-wasi.

Kafin sha biyu ta gama duk wani abu da take yi a makarantar sai dai ba ta son ta dawo ta ɗauko yara; ba wai yaran ne ba ta son ɗaukowa ba amma ba ta son ta ɗauko su Mustapha ya ga kamar faɗansa ne ya sa don haka duk lokacin da za ta fita ya za ta zai yi mata faɗa ta dauko masa yara.

Don haka suka nemi inuwa ita da ƙawayenta suka zauna suna hira, sai wajen 1;30pm sannan suka ƙarasa masallaci suka yi sallah kowacce ta kama hanyara gida. Ko da ta zo gida ba ta tarar da wata matsala ba, Rashida ta kai Shukra gidan su Ummi ta ɗauko
Nasreen daga makarantar kamar yanda ta ba ta umarni. Su kuma Afaf da Habib kusan tare da ita suka shiga gidan.

Ko da ya dawo tana jin sa yana tambayar yaran wanda ya ɗaukosu daga makaranta suna ba shi amsa, musamman Shukra wadda yake ta tambayarta me suka yi ita da Rashida a gidan bayan Anti ta fita. Haka ta yi banza da shi ta cigaba da harkokinta.

Haka suka cigaba da yi, sai ya zama kuma da yake ba a fara lecture sosai ba sati biyun farko kullum Khadeeja ba ta fita da wuri sanna kuma tana dawowa kafin ya dawo gidan, don haka matsalarsu da sauƙi tunda zai zo ya tarar da ita tana ta hidimar yara.

Sati ɗaya da komawa aka kafe wa su Khadeeja timtable, kuma da yake babu lokaci sosai timetable ɗin a matse take. Haka dai suka cigaba da karatun. Ranar Alhamis shi ne take da lecture 8am to 6pm, don haka ta san dole ta shirya ta fita tare da yara. Tun dare ta gama komai, ta yi rabin aikin abincin safe sannan ta fitowa da kowa kayansa.

Ta yi wa Rashida duk wani bayani da take buƙata tunda yaran idan sun dawo daga makarantar boko babu islamiyya don haka nan za su wuni a gidan. Tun kafin asuba ta tashi suka fara aiki tare da Rashida. Bayan Mustapha ya dawo daga masallaci
sallar asuba ya same ta a kitchen, tana ta fama kai wa da kawowa tsakanin dankalin da take soyawa da kuma haɗawa yara abincin makarantarsu a lunch box.

Bayan ya amsa sannu da zuwanta yace ‘Wai kin yi sallah kuwa? Na ga kamar a nan na bar ki fa. Ta yi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, na yi sallah mana. Sauri nake na gama saboda yau 8am to 6pm ne da ni kuma 8am din nan idan Prof. ya riga ni shiga aji rufe min ƙofa zai yi wallahi shi yasa nake ta sauri don kullum sai ya yi attendance.’

‘Oh kenan yau sai 6pm za ki dawo gidan? Eh.’ Ta amsa a gajarce tana kwashe dankalin da ya riga ya soyu. Ya ƙara haɗe girar sama da ƙasa sanna yace ‘To a ina za ki bar yara wuni guda? Ba ta son hayaniyarsa don ba ta son abinda zai ɓata mata rai, ba tare da ta bar abinda take yi ba tace ‘A nan mana gidansu; Rashida za ta ɗauko Nasreen su kuma su Afaf idan suka dawo za su same ta a gidan sai su yi zamansu kafin na dawo, they will be just fine.’

‘Haba ai daɗewar ta yi yawa, kenan haka za su zauna su yi duk abinda suka ga dama ba tare da wata kulawa ba.’ Ya faɗa a fusace. ‘Kada ka damu Rashida za ta kula da su.’
Kafin ya ba ta amsa suka jiyo ihun Nasreen daga ɗakinsu tana cewa ‘Wayyo Anti.’
Ta riga ta san rigimar Nasreen, idan dai aka tashe ta da sassafe zuwa makaranta sai ta yi kuka ko ma waye ya tashe ta, shi ma kuma ya san da haka.

Amma ba tare da ɓata lokaci ba ya nufi ɗakin da sauri. Ganin haka ita ma Khadeejan ta ajiye abinda take yi ta bi bayansa, kusan a lokaci ɗaya suka shiga ɗakin. Nasreen tana zaune a kan gadonsu da hawaye shaɓe-shaɓe a idonta yayin da Rashida take tsugune a gaban gadon tana riƙe da towel. Me aka yi miki kike kuka Nasreen?’ Ya tambaya kafin ya karasa shiga ɗakin.

Khadeeja tana shiga ɗakin ta sauko daga kan gadon ta rungume ta tana cewa ‘Anteee.’
Ya shafa kanta ‘Me aka yi miki? Cikin shagwaɓa tace ‘Rasheeda ce. ”Ya juya ya dubi Rashidan a fusace yace ‘Me kika yi mata? Nan da nan jikinta ya hau rawa tana gyara tsuguno, kafin ta yi magana Khadeeja ta shafa kan Nasreen tace ‘Nas me Rashida ta yi miki?’

‘Tashi na ta yi daga barci. To ai kin ga shirya ki za ta yi ki tafi school ko? Ko kina son ki makara Uncle ya koro ki gida ne? Ya yi tsaki ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Ta lallaɓa Nasreen ta tura ta banɗaki sannan ta juyo za ta fito, kafin ta fito ta jiyo shi yana dawowa ɗakin yana cewa ‘Dankalin da kika bari a wuta ya kone, ki je ki duba na kashe miki wutar.’

Ta wuce shi ta ƙarasa kitchen ɗin da gudu inda ta sami dankalin ya ƙone, ta kwashe sannan ta sake kunna wutar ta ɗora. Ya ƙaraso ya tsaya a kofar kitchen ɗin, ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta tana zubawa yara abincin rana wanda ta sauke a babban flask. Jimawa kaɗan yace ‘Kin ga irin abinda yasa bana son ki bar su da yarinyar nan ita kaɗai ko?

Ya za a yi ta iya kula da yara tunda ga shi nan ba ta ma iya tashinsu daga bacci ba?’
Ta kalle shi cike da mamaki tace ‘Nasreen ce fa, ko kai ne ma ka tashe ta sai ta yi rigima, ko ka manta ne? Kuma kai ne ka ce ba ka son Rashida ta dinga yi maka girki kuma ka ga dole abu ɗaya zan yi a lokaci guda ba zai yiwu ina girka muku abinci ba kuma ina shirya yara.’

Ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba. Ta ja tsaki ta share ƙwallar da ta taru a gefen idonta sannan ta cigaba da aiki. Ba ta ma san me take ji ba, ƙoƙari kawai take ta fita daga gidan idan ta je makaranta ta samu ta yi tunani ta fahimci me take ji. Bayan ta gama abinci ta wuce ɗaki ta same shi bayan ta zubawa yara abinci suna ci.

Yana kwance a gefen gado yana fama latsa waya ta wuce har ta kusa shiga wankan yace ‘Idan na kai yara dawowa zan yi kin sani, sai wajen 10am zan fita, ita wannan yarinyar taki haka za ki bar min ita a gidan daga ni sai ita? Cikin halin ko in kula tace ‘Eh, ita da Shukra za su zauna idan za ka fita kawai ka gaya mata don ta san cewa ka fita ta cigaba da aikinta.’

Har za ta shige banɗakin yace ‘Gaskiya ba na so, kuma ke ma kin san bai dace ba ki bar ni a gida daga ni sai mai aikinki mace. Irin haka ne kuma idan an ce za a auri mai aikin ku ce ba ku yarda ba. Duk ɓacin ran da take ciki sai da ya ba ta dariya, duk da dai dariyar takaici ce tace ‘to ai ga ka nan ga ta nan ka aure ta mana, ai ita ma mace ce.’

‘Ni dai na gaya miki bana son ki bar ta a gidan idan ina nan tunda ke ba kya nan, ki sami inda za ki ajiye ta idan na fita sai ta dawo gidan. ‘Uhhm!’ Ta amsa sannan ta shige wankan cike da takaicinsa, har ji take kamar zuciyarta tana turiri. Zuwa makaranta lecture kawai ya zama wata drama.

Nan da nan ta ƙarasa shiryawa ta shirya yaran, ta haɗa tea ta zauna tana sha. A haka Mustafa ya fito ya same su lokacin 7:15am. ‘Ku tashi mu je.’ Ya faɗawa yaran.
Ta miƙe riƙe da kofin shayinta tace ‘Bari na ɗauko hijab dina na saka ku rage min hanya.’
‘A a za ki makarar da mu ne fa, ga shi ko shayi ba ki gama sha ba kuma kin san idan suka makara koro su za a yi.

Ya juaya ga yaran wadanda sun riga sun miƙe kowa da kayansa a hannu yace ‘Mu je.’
‘Anti sai mun dawo.’ Suka faɗa sannan suka juya suka fice ya bi bayansu. Ta bi bayansa da kallo cike da mamaki; ta kasa gane motarsa ce ba ya son ta dinga shiga ko kuwa tsabar baƙin ciki ne a kan za ta fita yake hana shi rage mata hanya.

To amma kuma yana kai ta unguwa, kodayake wannan fita ce da shi ya ga dama kuma kusan duk inda za ta tunda ta aure shi tare yake kai ta da yaran suna biye da ita. To me yasa idan dai makaranta za ta tafi sai ya san yanda ya yi ya tafi ya bar ta ba tare da ya ko da rage mata hanya ba?

Haka har ta gama shirinta ba tare da ta samo amsar tambayarta ba; ta fito ta sami Rashida a kitchen tace ‘Idan babansu ya dawo ki koma ɗaki ki zauna in ya fita sai ki fito ki cigaba da aikin; idan Shukra ta zauna a wajensa shikenan idan kuma ta taho wajenki to don Allah kada ki bari ta yi kuka ya ji.’

Ta yi mata sallama ta fice tana sauri saboda 7:20am ta riga ta yi kuma ba ta da tabbas ɗin za ta iya kai wa BUK kafin 8:00am. Ta kusa isa titi Mustapha ya karyo kwana ya shigo layin, ta ɗauke kanta daga kallon inda yake; ba ta sani ba ko ya ganta ko bai ganta ba.

Ta ƙarasa titi cikin sanyin jiki ta hau Napep tambayoyi daban-daban suna ta yawo a kanta; wai ina babe ɗinta ne? Wanda yake son ta? Wanda kafin aurensu har so yake ya ɗauko ta daga makaranta ya kai ta unguwa ko ya kai ta gida don dai tana hana shi ne saboda ta san Baffa ba zai bari ba a lokacin. To shikenan soyayya ta ƙare ko me
Mustapha yake nufi da ita? Shekara ɗaya fa kenan da ‘yan watanni da aurensu.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyu
Labarin na GabaKira A Kan Haɗin Kai
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.