Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Takwas

0
9

Duk yanda take cikin damuwa da yanda take so ta yi wa Mustapha tijara game da yanda ya ɓoye mata maganar aurensa da Naja haka ta haƙura ta danne zuciyarta. Domin ita kanta ta kasa ganin maslahar yi masa maganar; tunda dai ita ce ba ya so ta sani gara ta rabu da shi ta gani ko za a ɗauro auren ne a kai amarya sama jannati saboda kada ta sani.

Cikin da take ɗauke da shi ma kasa gaya masa ta yi, domin ba ta ga alamar yana farin cikin kasancewarta matarsa ba. Gaba ɗaya ma cikin ya zo mata a wani lokaci ne da take jin cewa da ba ta same shi ba za ta iya haƙura da haihuwa a gidan Mustapha har sai ta fahimci inda auren nasu ya sa gaba.

Ko da yake dai ta san ana cewa idan namiji zai ƙara aure matarsa da take gidan sai ta yi matuƙar haƙuri; to tabbasa ta ji a jikinta cewa lokacin nata haƙurin ne ya kama yanzun. Da kansa ya kula da yanda take mu’amalarta kwana biyu cikin kasala ga shi ba ta ma son magana, don haka ya tasa ta a gaba ya kai ta asibiti.

A nan aka tabbatar masa da cewa tana ɗauke da ciki sati shida. Suna zaune a mota yana tuƙo su a hanyarsu ta dawowa ya dube ta yace ‘Kin gani ko, kin sami cikin a kwanciyar hankali ba tare da kin je nemansa a asibiti ba ko? Allah ya sa dai ba mai wahala ba ne? Ta ɗan yi gajeran murmushi tace ‘Amin ya Allah.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci, ya dube ta yace ‘Wai ya na ga duk kin yi wani shiru ne? kamar ba abin nema ne ya samu ba? Ta kawar da kai tana murmushin yaƙe tace ‘Bana jin daɗi ne, bacci ma nake ji. Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar ta rufe ido, don haka shi ma ya ƙyale ta ya mayar da hankali a wajen tuƙinsa.

A haka Khadeeja ta dage ta cigaba da mu’amalarta tana yin duk wata hidima da ta saba. Ko a wanne yanayi ta tashi haka take daurewa ta yi duk wata hidimarta don ba ta shirya drama da Mustapha ba. Ta riga ta san idan dai tana numfashi a gidan nan to duk wata hidima da matar gida take yi ba yafe mata zai yi ba; don haka ta daure ta cigaba da dagewa tana yi.

Musamman da yake duk wani aiki da ta saba yi a gidan ta riga ta koyawa Rashida kuma ta iya sosai, ga shi yarinyar ba ta da ƙyashi ko ɗaya, don haka abubuwa suka zo mata da sauƙi sosai. Sai dai fargabarta ɗaya iyayen Rashida suna maganar ko da wane lokaci za a iya zuwa a ɗauki Rashida saboda aurenta ya kusa; duk da dai an ce za a kawo mata ƙanwarta to amma ta san akwai aiki.

Haka ta cigaba da rayuwarta tana goyon cikinta. A hankali ta fahimci lokutan da yake zuwa zance wajen Naja, kuma da yake shi yake kai ta makaranta da ta shiga motar take gane Naja ta fita a motar ko kuma sun fita tare. Daidai lokacin da za su fara jarrabawar ƙarshe a lokacin cikinta ya shiga wata na takwas; ga hidimar gida, ga karatu kuma ga shi tana ƙoƙarin haɗa project ɗinta.

A dai-dai lokacin ne kuma Mustapha ya gama gyara gidansa wanda yake fatan da zarar sun koma za a yi bikinsa da Naja. Sau biyu yana kai su gidan ita da yara, kuma duka zuwa biyun sai ta tambaye shi ko aure zai yi ne yake yin gidan kamar da zubin mata biyu. Amma duk lokacin da ta tambaya sai yace mata ko da zai yi auren to ba yanzu ba; ta rasa gane dalilin da yasa yake son ɓoye mata aurensa da Naja.

Don haka ma ta daina tambayarsa gaba ɗaya. Ranar Asabar ce kuma tun dare ya sanar da ita da safe yara su shirya zai fita da su, don haka tun wajen tara na safe bayan da suka ci abinci ta sallame su ta koma ta kwanta. Ya dai ce mata gidan Hajia za su je kuma su ma yaran haka suka gaya mata; amma a ‘yan kwanakin nan yana yawan fita da yaran ranar da babu aiki yace wajen Hajia zai kai su.

Ta riga ta gane wajen Naja yake kai su, sai dai ba ta ga dalilin da zai sa ta yi masa magana ba tunda ‘yayansa ne sannan kuma gaya musu da yake su ce mata gidan Hajia suka je su yake cutarwa ta hanyar koya musu ƙarya. Gaba ɗayansu suka fice banda Habib, wanda dama ya riga ya saba duk lokacin da za su yi wannan fitar shi baya bin su.

A gida yake zama tare da Khadeejan da Rashida. Sai wajen ƙarfe biyar na yamma sannan suka dawo, lokacin ta riga ta gama abincin dare ta zuba a flask tana kwance a ɗaki. A ɗakinta yaran suka same ta tana kwance tana hutawa, suka sanar da ita sun dawo. Shukra kuwa sai ta wuce ta haye gadon ta kwanta kusa da ita tana cewa ‘Bacci kike yi Anti?’

Tace ‘A a, hutawa nake yi. Ta ɗan matsa jikinta tana gyara kwanciya, Khadeejan ta ɗan gyara kwanciyarta tana kawar da Shukran daga cikinta. Ta yi dariya tana cewa ‘Na matsa ko Anti, kada na lotsewa ƙanina hanci. Ta yi dariya saboda ita ce ta saba gaya mata hakan a duk lokacin da take son kwanciya a jikinta tunda cikin ya fara girma; domin Shukra yarinya ce mai son jikin tsiya kuma ta samu Khadeejan ba ta ture ta.

Tace ‘Yauwa, ashe dai kin gane. Kada a dinga ce miki yayar mai lotsattsen hanci. Suka yi dariya gaba ɗaya; Shukra ta ci gaba da wasa da hannun Khadeejan guda ɗaya yayin da Khadeejan take riƙe da waya a ɗaya hannun tana chatting. Jimawa kaɗan cike da damuwa tace ‘Anti.’

‘Umm.’ Ta amsa ba tare da ta bar abinda take yi ba. Tace ‘Gaskiya ni ba zan koma wajen Anti Naja ba, a wajenki zan zauna ko? Ta ajiye wayar tace ‘To wa yace za ki koma wajen Anti Naja kuma? Ai muna nan tare, ko ba gamu ba a gidanmu. Cike da damuwa tace ‘Ai ita ma tace auro ta Abbanmu zai yi ta dawo gidanmu. Amma sai mun koma sabon gida.

Shi ne yau da muka je wajenta take cewa Yaya Afaf idan ta tare duk wajenta za mu koma. Gaskiya ni dai ba zan koma ba ko? Ta ɗan yi shiru tunani yana nema ya birkita ƙwaƙwalwarta; duk da bai gaya mata ba ta san yana kai yaransa wajen Naja, amma maganganun da Najan take gayawa yaran ba sa kama da maganganun da ya dace a gaya musu a daidai wannan lokacin.

Sai dai ta san babu yanda za ta yi tunda shi ya ba ta dama. ‘Anti.’ Muryar Shukra ta katse ta tana kiran sunanta. Bayan ta amsa Shukran ta cigaba cikin damuwa ‘Tace saura wata biyu ta tare, gaskiya idan ta zo ki gaya mata ni a wajenki zan zauna ba a wajenta ba. Kuma ma na ji tana gayawa Yaya Afaf idan an koma sabon gida sama take so ke ce a ƙasa, na gayawa Yaya Afaf mu ne a sama mu da ke tace min wai da Allah can.

Gaskiya ki gaya musu mu ne a sama. ‘Hmm! Zan faɗa musu Shukra, ai mu ne a sama kada ki damu. Ta cigaba da surututa tana ba wa Khadeeja labarin irin abubuwan da suke yi idan suka je gidan Naja. Duk da Khadeeja ba ta yi mamakin jin cewa Naja ta san da sabon gida ba amma ta yi mamaki da ta ji cewa har Naja ta zaɓi part ɗin da take so yayin da ita kuma har yanzu bai ma gaya mata ita da wata matar za su zauna a gidan ba.

Ta kasa gane dabarar da Mustapha yake jin ya yi da ya ƙi gaya mata zai yi aure; amma dai za ta cigaba da binsa ta ga ƙarshen wulaƙancinsa. Ko da yake a ‘yan kwanakin nan ma yanda yake ƙara tubure mata ta tabbatar da tana biye masa da kullum sai sun yi faɗa.

To sai dai ba ta da wannan lokacin tunda ga project ɗinta wanda take so ta gama kafin su fara jarrabawa wanda tana fatan Allah ya sa kada haihuwa ta zo mata har sai tayi final paper. Haka ta ajiye wannan ma a ranta tana jiran ranar da za ta titsiye Mustapha tunda haka ya zaɓa.

Tun kafin su fara jarabawa ya sanar da ita idan ta haihu aka yi suna aka gama zuwa barka za su koma sabon gida, saboda ba ya so a je a ɓata masa gida. Ita ma tsarin ya yi mata don haka ba tare da wata matsala ba ta amsa. Kuma kamar yanda ya ba ta umarni ta fara haɗa kayanta da za ta tafi da su duk da cewa ya gaya mata ya saka sabbin furniture a gidan.

Ranar da za ta yi jarrabawar ƙarshe ya kama yara suna hutun makaranta, kuma sai 2pm za su shiga paper. Don haka yace idan babu matsala yana so ta shirya da wuri su tsaya a sabon gida ta ga furniture ɗin da ya siyo in ya so sai ya ajiye ta a makaranta shi da yara su wuce wajen Hajia. Ta riga ta gama karatunta don haka tun wajen sha ɗaya ta shirya suka shiga mota gaba dayansu suka kama hanya.

Saman gidan yana ɗauke da parlor guda biyu ƙarami da babba da kuma ɗakuna guda uku sannan da kitchen, ɗaki daya da parlor suna tare da juna wanda dama ya sanar da ita nan ne nashi part ɗin. Ƙasan kuma parlor ne guda daya me haɗe da ɗakuna biyu da kicin kamar na saman, sai wani babban parlor ɗin kuma da ɗakuna guda biyu waɗanda suke kusa da juna.

Parlor ɗin ƙasan duk a nan aka sauke furniture ɗin; duk da kusan kowanne yana cikin kwalinsa. Suna shiga suka ɗan yayyage kwalin ita da yara suka gani. Ya dube ta yana nuna ɗakunan ƙasan yana cewa ‘Sai ki zaɓi a wane dakin za a saka miki gadon, in ya so ɗaya dakin kuma sai a ɗauko gadonki na tsohon gida a saka.’

Ta kama hanyar sama tana cewa ‘Eh hakan ma ya yi; ɗakin wanda yake jikin nakan sai saka min sabon gadon a nan in ya so na kusa da shi sai a gyarawa ‘yan mata na ko? Shi kuma Yaya Habib sai a ba shi ɗaya daga cikin wannan na ƙasan. Shukra ce kawai ta biyo ta shi yana tsaye a inda yake. Ta dan juyo tana cewa ‘To ka zo mu je mana ka gani.’Ya yi ‘yar dariya yace ‘Na zata za ki fi son waɗannan ɗakunan na ƙasa ai, kin ga sun fi girma.

Kuma ai ina ga zai fi min privacy a ce ɗakin ki yana nan ƙasa a madadin yana kusa da nawa idan kin yi baƙi ina jiyo ku. Ta yi dariya tace ‘Haba dai, kuma don ni ce duk faɗin gidan nan sai na rasa wajen sauke baƙi sai bedroom? Ai dama sama ba wajen saukan baƙi ba ne tunda nan ƙasan ma da parlor.

Amma dai can ne ɗakina, in ya so idan ma ba ka so yaran su hau sama za a iya barinsu a ƙasa. Shukra tace ‘Gaskiya Abba mu ne a sama mu da Anti, in ya so ita Anti N…’ Kafin ta ƙarasa Afaf ta katse ta cikin ɗaga murya tana cewa ‘To ba ki ji me Abban yace ba, ƙasan ya fi girma ne da space. Khadeeja tace ‘To mu dai ba ma son ƙasa, muna sama abin mu.’

Ta ja hannun Shukra suka haye saman. Habib wanda yake tsaye a kusa da Abban nasu ya dube shi yace ‘Haba Abba, dama ai sama na Anti Khadija ne.’ Kallon da Abban ya yi masa ya sa ya kawar da idonsa da sauri ya waske yana cewa ‘Bari na je na taya su zaɓen ɗakin. Haka ya haƙura shi ma ya bi su saman inda khadeeja ta nuna masa ɗakin da yake jikin nasa tace shi take so, ɗayan kuma wanda yake gefe ɗaya sai a bar wa yara.

Ba shi da wata hujja da zai ba ta a kan hana ta ɗaukan ɗakin sama, kuma har yanzu ba ya jin ya shirya gaya mata cewa zai ƙara aure, ya fi so sai ta haihu tukunna saboda kada ma ya ji tausayinta idan tace za ta tayar masa da hankali. Haka suka gama zagayensu a cikin gidan sannan suka shiga mota suka nufi BUK don su kai ta.

Har suka isa makarantar ba ta daina mamakin Mustapha ba; ta kasa gane sai yaushe zai daina yi mata wannan ƙaryar. Kuma ta kasa gane dalilin da yasa yake fifita buƙatar Naja da son zuciyarta a kan tata, amma dai haka za ta cigaba da biye masa ta ga gudun ruwansa.

Kwanansu biyu da gama jarrabawa Khadeeja ta haifi yaronta, don haka ko kwana ba ta yi a asibiti ba aka wuce da ita gidanta. Sai daga baya aka kawo mata Anti Binta wadda kanwa ce a wajen Mommy. Tun a asibiti Mustapha ya sanar da su ya sakawa yaro suna Muhammad; sunan Baffan Khadeeja. Daga baya Nabila ta yi masa laƙabi da Hammad.

Nan da nan aka shiga hada-hadar shirya bikin suna; kuma a lokacin Mustapha ya sanar da ita idan an yi suna da sati biyu za su koma sabon gida. Ranar kwana biyu da haihuwa Mustapha ya sameta a dakinta da daddare, tana zaune a gefen gado da baby a cinyarta tana kallonsa tana murmushi. Ya ajiye shopping bag ɗin da ke hannunsa sannan ya zauna a kusa da ita ya shafa kan baby yace ‘Shikenan kuma kin mayar min da yaro abun kallo kamar wata TV ko?’

Ta yi ‘yar dariya tace ‘To ina laifi, ina yaba halittar Allah ne. Ya matsar da ledar kusa da ita yana cewa ‘Ga wannan ‘yan office ɗinmu ne suka bayar a kawowa Baby. Ta karɓa ta ɗan buɗa ta leƙa sannan ta mayar ta ajiye tana cewa ‘Mun gode, Allah ya saka da alkhairi. Ai dole Muhammad ya kawo tukuici tunda an yi masa takwara.’

Ya yi dariya. ‘Wannan ma ba na Muhammad ba ne, sauran ma’aikatana ne dai. Shi yace sai gobe za su zo da matarsa. ‘Allah sarki mun gode, Allah ya bar zumunci. Suka ɗan taɓa hira sannan ya fita. Yana fita ta ɗauki ledar ta zazzage kayan; rigunan Baby ne masu kyau da tsada guda biyu, sai set ɗin kayan sanyi guda ɗaya, set ɗin huluna da kuma set ɗin kayan wasa.

Ta taɓe baki ta mayar da kayan cikin ledar, jikinta ya ba ta wannan kayan Naja ce ta bayar don haka ko burge ta ba su yi ba. Rawar kan da yake yi da ya shigo da kayan kaɗai ta isa ta sa ta san cewa daga wajen Naja kayan suka fito. Ta tsani yarinyar gaba ɗaya ta tsani ta tuna ta, ba ta ko son jin sunanta. Haka ta ajiye kayan da niyyar da zarar an gaya mata haihuwa ita ma za ta yi barka da su.

Lafiya ƙalau aka gama taron suna; musamman da yake Khadeeja ta kawar da kanta daga abubuwa da yawa. Domin hatta abincin sunan Yaya Jidda cewa ta yi ya ba su za su yiwo su zo da shi, shi kuma ya hau kai ya zauna. Tunda ta ga haka ta gayawa Mommy kada su yiwo gayya da yawa, sannan Baffa ya ba su kuɗi suka shirya nasu abincin wanda suka taho da shi.

Ko da Yaya Jidda ta gansu da kulolin abincinsu sai ta soke duk wani wulaƙanci da ta shirya yi musu, haka aka gama taro kowa ya watse lafiya. Bayan kwana biyu tana kwance a ɗakinta tana hutawa da daddare wayar Mustapha ta shigo; ta riga ta san yana cikin gidan don haka ta san kiranta yake yi. Haka yake yi tunda Anti Binta ta zo; baya shiga ɗakinta sai dai ya yi mata waya ita ta same shi a ɗakinsa.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta miƙe ta nufi ɗakin. Ta ƙarasa ta zauna a gefen guda kusa da shi tace ‘Gani. To sannunki da zuwa.’ Ya faɗa yana bin idonta da kallo yana ƙoƙarin karanto yanayinta. Ta yi murmushi tace ‘Godiya nake, a ba ni abinda aka kawo min. Suka haɗa ido na dan lokaci, ya ɗauke nashi idon ya ɗan cije leɓe sannan yace ‘Ya shirin tashi, saura kwana biyar fa.’

‘Ai ni na gama shiri, maƙota ma duk na gama sallama da su. Sai mun tare zan yi musu kwatance su zo ganin gida. To da kyau. Suka yi shiru na ɗan lokaci; ita tana sauraronsa don ta kula da magana a bakinsa yayin da shi kuma yake ta sake tauna maganar bakin nasa yana tunanin ta inda zai fara. Ya kalle ta suka haɗa ido ya yi gajeran murmushi, ita ma ta mayar masa da murmushin. Cikin sanyin murya yace ‘Um ki yi haƙuri ki saurare ni kuma ki fahimci maganar da zan gaya miki.’

Ta kalle shi na ɗan lokaci da mamaki a fuskarta tace ‘In sha Allah.’Ya sake gyaran murya sannan yace ‘Um Khadeeja aure zan yi, don maganar da nake miki ma saura sati biyu a ɗaura auren. Idan mun tare a sabon gida da sati ɗaya ita ma za ta tare. Suka haɗa ido, ta yi murmushi sosai sannan ta zare hannunta daga nashi tana cewa ‘Allah sarki, abun ya zo kenan. Toh Allah ya sanya alkhairi.’

Buɗe baki ya yi yana kallonta saboda tsabar mamakin yanda ta nuna halin ko in kula da maganar tasa kamar dai wadda yake cewa gobe Litinin a ranar Lahadi. Ta miƙe za ta fice ya riƙe hannunta yana cewa ‘Um wani abun kike yi ne kike saurin tashi. Ta koma ta zauna tana cewa ‘A a, na zata ka gama maganar da za ka faɗa ɗin.’

Ya ɗan sunkuyar da kai saboda gaba ɗaya ya kasa haɗa ido da ita, wannan halin ko in kula ɗin da ta nuna yasa duk ya firgice; gaba ɗaya ta goge masa haddar kalaman da ya tsaro don ya ba ta haƙuri. Cikin sanyin murya yace ‘Um baki ma tambayi wacece wadda zan aura ba. Ta ɗan yi dariya tace ‘Oh, Naja ce mana. Ko ka fasa auren nata ne?’

A jigace ya amsa ‘Ita ce. Ta daga gira cikin halin ko in kula tana shirin miƙewa tace ‘Allah ya sanya alkhairi. ‘Um, wai dama kin san zan yi auren ne ko na ga kamar kin sani tun tuni. Ta yi ‘yar dariya ta koma ta zauna tace ‘Na sani mana, ko bai kamata na sani ba? Ya jiijiga kai ‘No, ina dai mamaki ne. Suka yi shiru na ɗan lokaci.

‘To don Allah wa ya gaya miki?’ Muryarsa ta katse mata tunani yana tambaya. Ta yi ‘yar dariya tace ‘Oh, ka san fa na ɗauka kai ka gaya min; ashe ba kai ba ne. Ina jin dai a cikin waɗanda ka gayawa ne kace kada su gaya min aka sami wani ya gaya min. Ya sunkuyar da kai domin ya kasa haɗa ido da ita; wato duk wannan tsawon lokacin ashe kallonshi kawai take yi duk abinda yake ɓoyewa ta sani.

Ba ƙaramin mamaki ya yi ba. Kafin yace wani abu suka jiyo kukan Hammad daga cikin gidan, don haka ta dube shi tace ‘Ka ji yarona can yana kuka, bari na je na gani. Ta fice ba tare da ta saurari amsar shi ba. Tana fitowa daga ɗakin Mustaphan ta tarar da Anti Binta a parlor tana ta jijjiga Hammad, tun kafin ta ƙarasa wajensu tace ‘Yunwa yake ji, zo ki ba shi ya sha.’

Ta karbe shi ta shige ɗakinta Anti Binta tana biye da ita. Haka ta daure ta haɗiye malolon da ya tokare mata maƙogoro har ta gama ba shi nono suna hira da Anti Binta. Sai da ya sha ya ƙoshi sannan ta miƙawa Anti Binta shi tana cewa ‘Ga shi Anti Binta, banɗaki nake son shiga. Ta karɓe shi ta miƙe tana cewa ‘To muna can ɗakin yara muna hira da mutuniyata.’

Ta fice ta ja mata ƙofa sannan ta miƙe ta shige banɗakin don ta san idan dai tana cikin ɗakin nan wani sai ya zo nemanta, idan kuma ta rufe da mukulli za a yi ta faman tambaya. Tana shiga banɗakin ta turo ƙofar ta jingina a jikin kofar, take hawayen da take riƙewa suka ƙwace kamar an kunna famfo. Ta haɗa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta tana jijjiga kai, saboda tsabar takurar da zuciyarta ta yi har wani ɗaci take ji a bakinta.

Yaushe Mustapha ya raina ta haka? Wannan ma ya fi ƙarfin raini ya koma wulaƙanci. To me yasa ya yi mata haka? Daman can ba ya sonta ne ko kuwa son da yake mata ne ya ƙare? Ba ta taɓa tunanin za ta auri miji ta zauna ita kaɗai ba amma dai ta ɗauka idan ka auri mutum zai cigaba da girmama ka yana ganin mutuncinka har ƙarshen tarayyarku.

A halin yanzu ta rasa wanne za ta yi; murna ta haihu ita ma ta sami yaro ko kuwa jaje za ta yi wa kanta tunda ko babu komai wannan yaron da ta haifa zai ƙarawa alaƙarta da Mustapha tsawon rai. Ba ta san tsawon lokacin da za ta iya ɗauka tana jure wulaƙanci irin wannan da Mustapha yake mata ba, amma dai ta san tabbas ba za ta iya jurewa har abada ba.

Ga shi shi ba dukanta yake ko zagi ba, wani irin wulaƙanci ne yake mata yana nuna cewa komai normal ne, kuma a mafi yawancin lokuta ma idan ta yi magana sai a dinga nuna mata haka maza suke. Domin kowa ce mata kawai yake idan dai namiji ne ba ta ga komai ba. Ta bar wa Allah al’amarinta kuma za ta jira su tare ta ga yanda yanayin zaman zai kama; amma tabbas idan aka cigaba a haka ba ta jin za ta iya zama da Mustapha.

Zuwa yanzu kuma duk wasu alamu sun nuna mata cewa ba zai taɓa yi mata adalci ba ita da Naja, kamar ma dai yanzu ne ya yi aure na soyayya wanda yake sa ran zai more rayuwarsa a ciki; tunda ta gama yi musu wahala ta raini yaransa lokacin da suke tsananin buƙatar uwa. Yanzu sun girma sun zama mutane don haka sai ya aure wadda yake so ta zo su more rayuwarsu ita kuma a mayar da ita saniyar ware.

A hankali ta zame a jikin ƙofar ta zauna ta sake fashewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ba wa kanta haƙuri ta wanko fuskarta ta fito daga banɗakin.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Bakwai

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Bakwai
Labarin na GabaWasu Kayan Kiɗan Hausawa
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.