Mijin Marigayiya Babi Na Biyu

0
44

khairatu.shehu

Kamar yanda aka yi alƙawari ranar Asabar 18th February, 2020 waliyyan Mustapha suka sami  karɓa ta girmamawa a gidan kakan Khadija. Bayan sun gaisa an musu maraba suka gabatar da  sadaki N100,000 da kuma kuɗin aure N50,000. Baba Sani ƙanin mahaifin Khadija ya sa hannu ya karɓi kuɗin ya matsa ya ajiyesu a gaban mahaifinsu Alhaji Baba. Cike da fara’a da murmushi Alhaji yace ‘Ma sha Allah, Allah ya sa albarka Allah ya nuna mana.’

Gaba ɗaya mutanen da ke wajen suka amsa da Amin. Baba Safiyanu wanda Yaya ne a wajen mahaifin Khadija ya yi gyaran murya yace ‘Alhaji ni ina ga tunda ga sadaki an kawo kuma ga waliyyan ango ai sai kawai a ɗaura auren nan yanzu. Yanda  abubuwa suke tafiya rufe garin nan fa za ayi, tunda ka ga ƙasashen duniya suna ta rufewa fa.  COVID 19 ɗin nan ana maganar ta shigo ƙasar nan sosai, ko da wanne lokaci za a iya shiga lockdown.’

Alhaji yace ‘Ikon Allah, kace abun ya zo mana kenan. To Allah ya tsare mu da zuri’ar mu.’ Ya dubi  waliyyan Mustapha yace ‘To idan a shirye kuke sai a ɗaura auren ai, nan da sati mata sai su yi bikinsu su kai amarya kafin a ce an kulle ƙasar.’

Cike da murna Alhaji Muhammad wanda shi ne Babba a waliyyan ango yace ‘Ah ai mu a shirye muke, hakan ai ya fi sauƙi Alhaji, Alhamdulillah Alhamdulillah. Shi Mustapha ai a shirye yake, lefe  ma da sauran kaya duk gobe sai mata su zo su kawo.’

Nan da nan suka gyara zama, Baba Sani ya kirawo mahaifin Khadija ya sanar da shi wanda shi ma a take ya amince, sannan ya kirawo maƙota da wasu daga cikin dangi. Su ma ‘yan uwan Mustapha suka sanar da shi ya taho shi da abokansa mutum biyu. Kafin minti talatin guest room ɗin Alhaji ya cika da mutane ana ta murna. Ba tare da ɓata lokaci ba aka ɗaura auren Khadija da Mustapha.

Tana kwance a parlor ɗinsu a kan doguwar kujera tana chatting a waya yayin da ƙanwarta Nabila take zaune tana kallon TV; ƙaninsu Ahmad ya shigo parlor ɗin da gudu yana ihu ‘Ta zama matar aure, Ya Khadija ta zama matar aure…’ Zumbur ta miƙe daga kujerar yayin da ita ma Nabila ta miƙe tana cewa ‘Kai fa kana da matsala, don Allah ji yanda ka firgita ni.’

Khadija tace ‘Wai me kake cewa ne?’ Yana dariya yace ‘Wallahi an ɗaura miki aure da Mustapha yanzu a gidan Alhaji.’ Ta buɗe baki tana kallonsa cike da tsananin mamaki. Nusaiba ta daki kafadarsa tace ‘Kai Ahmad  ka ji tsoron Allah.’ Yace ‘Wallahi da gaske nake, kirawo Baffa a waya ki tambaye shi.’

A take Mommy ta fito daga ɗaki riƙe da waya jiki a sanyaye, Ahmad ya kalle ta yace ‘Mommy ai an ɗaura auren Yaya Khadija ko?’ Ta ɗaga kai tana cewa ‘Eh, yanzu Baffanku yake gaya min an ɗaura auren.’ a juya ta dubi Khadija  tace ‘Khadija kin zama matar aure.’

Ta faɗa kan kujera kamar wadda aka tura, to murna za ta yi ko me? Bata taɓa zata za a ɗaura aure yau ba, ta zata za a yi yanda aka saba; a kawo kuɗin aure a zo a sa rana sannan a shirya biki a nutse. Shikenan yanzu ta zama matar Mustapha? Ikon Allah. Ta kai hannu ta shafa kwarmin idonta inda ta ji danshi; ƙwalla ce ta faɗo. To kukan me take yi?  Murna take yi ko kuwa tsabar mamaki ne?

Nabila ta zauna ta doro hannunta a kafaɗarta tana kallon Mommy tana cewa ‘To Mommy sai mu fara shirin bikin kenan ko kai ta kawai za a yi haka?’ Ta banka mata harara tana cewa ‘Sai kace wata kaza?’ Mommy tace ‘Uhm, sai dai mu jira Baffanku ya dawo mu ji.’ Ta koma daki ta bar su a nan.

Gaba ɗaya tunanin Khadija ya tsaya, wannan ɗaura auren da aka ce an yi mata yana nufin nan  da ‘yan kwanakin za ta tare a gidan Mustapha. Fatanta ɗaya Daddy ya bari a yi biki don gaskiya tana son biki. Ƙarar wayarta ne ya katse mata tunani, tana kallon wayar ta yi murmushi “My love” shi ne sunan da ta yi saving lambar Mustapha da shi.

‘Hello.’ ta amsa murya ƙasa-ƙasa. Muryarsa zaƙwai cike da farin ciki yace ‘Ya na ji ki haka? Ko ba kya farin ciki ne? Alhaji ya hutar da mu, kin ga next weekend kawai sai a kawo min amarya ta.’ Ta yi dariya ‘I was just not expecting it to happen today, but Alhamdulillah. Ai babu abinda ya fi zama da masoyi daɗi.’

‘Haka ne. So me kike buƙata na bikin, ki sami Yaya Mama ku yi lissafi zuwa an jima sai ki gaya min na turo miki ta account ɗinki. In sha Allah ranar Tuesday za a kawo lefe.’ ‘Ok, hakan ya yi.’ ‘Common, ni ina so na ji muryarki ta yi zaƙi zaƙwai kamar tawan nan.’

Tayi dariya ‘Ka kirawo ni in an jima kafin nan na sha zuma za ka ji zaƙin da muryar za ta yi.’ Suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta a kan gadon cikin sanyin jiki. Dab da azahar Yaya Mama ta ƙaraso tare da yaranta Anisa da Jawad. Ita ce Babba a ‘ya’yan  gidan su Khadija. Bayan ta gama tsokanar Khadija ta shige ɗaki inda ta tarar da Mommy tare da  ƙanwarta Anti Naja’atu suna ta tattauna bikin; don Baffa ya sanar da su a shirya a yi biki ranar Asabar da Lahadi idan an gama sai a kai amarya.

Bayan ta gaishesu ta zauna suka cigaba da tattaunawa a kan bikin. Jimawa kaɗan Yaya Mama tace ‘Ni wallahi Mommy tausayi ma Khadija take ba ni, Allah ya sa dai da gaske yake sonta kuma ya cigaba da kula da ita. Ga yara har huɗu yana shirin haɗa mata da  su, ai sai a hankali.’

Anti Naja tace ‘Kada ki damu ai mace komai ƙanƙantarta raino ba ya gagararta.’ Mommy tace ‘Yaran ma fa yana kawosu nan wajenta, kamar suna da tarbiyya da sauƙin hali ma.’ ‘To kin ji ma. Kada ki yi mata magana ma ki sa ta zata wani tashin hankali ne don na ganta tun da  aka ce an ɗaura auren nan jikinta ya yi sanyi.’ Haka suka gama tattaunawarsu suka tashi.

Ranar Lahadi bayan Magriba aka shirya Khadija a ka kai ta gidan Mustapha. Bai zo da abokansa ba sai mutum ɗaya wato Badaru, ba tare da ɓata lokaci ba suka sallami  ƙawayen amarya Badaru ya kwashe su. Bayan ya rufe gidan ya dawo ya same ta tana ta faman share hawaye. Ya zauna ya lallasheta har tayi shiru sannan suka yi Sallah ya buɗe musu abincin da ya zo da shi suka ci. Da kansa ya kwashe kayan da suka gama cin abincin sannan ya dawo ya same ta a zaune a inda ya bar ta.

‘Yauwa, tunda mun ƙoshi taso na nuna miki gidan naki kafin mu kwanta.’ ya faɗa yana murmushi. Ta miƙe a kunyace, har sun kama hanyar fita daga ɗakin ya juyo ya dube ta yana murmushi yace  ‘Bari mu fara daga nan, nan ne ɗakinki.’ Ta yi murmushi murya ƙasa-ƙasa tace ‘Ok.’

Ya wuce ta bi shi a baya ya nuna mata ragowar gidan; bayan ɗakinta sai ɗakinsa sai kuma ɗakin yara inda nan ne kuma ɗakin baƙi. Sai kuma parlor guda ɗaya da dining area a dai-dai kofar  kitchen. Bayan sun gama zagayawa ya kashe fitulun sannan suka wuce ɗakinsa inda za su kwana.

Ranar da Khadija ta cika kwana uku da tarewa a ranar bakin danginsa da suke ta zuwa ganin amarya sun lafa, don tunda gari ya waye babu wanda ya zo har azahar ta yi. Suna zaune a parlor suna hirarrakinsu aka fara kiran Sallah, ya miƙe yana cewa ‘Bari na je masallaci na dawo.’

‘Ok, by then ni ma na yi sallar na yi serving lunch.’ ta amsa ita ma tana miƙewa. Ta yi masa a dawo lafiya ya fice ita kuma ta shige kitchen. Kafin ya dawo ta yi Sallah ta gyara kwalliyarta sanna ta jera abincin a kan dininga table. Yana  dawowa ta yi masa sannu da zuwa sannan ya zauna a dining table ta zuba abinci suka fara ci.  Fried rice ne tare da sauce ɗin hanta da salad, daga gefe kuma ga haɗaɗɗen zobo.

Shiru suka yi kowa yana ta kai loma, sai da Mustapha ya kusa cinye abincin nasa sannan ya ajiye cokalinsa ya ɗauki zobon da ta zuba masa a kofin tangaran ya kora. Yana ajiye kofin ya ɗauki cokalinsa yana gyara abincin ya dube ta yana cewa ‘Umm! Kin iya girki fa.’ Ta yi dariya tace ‘Ai da na zaci santin kurma kake da ka kasa magana.’

‘Au ashe ma sa min ido kika yi.’ ya faɗa yana sake cika baki da abincin. Ta yi dariya ita ma ta cigaba da cin abincin. Bayan ya haɗiye na bakinsa yace ‘Ina ga ai ya kamata in an jima mu je mu ɗebo su Afaf ko? Tun da suka ji an kawo ki suke ta zumuɗi.’

Ta kalle shi tana wasa da cokalinta a kan abincin saboda ta riga ta ƙoshi, tace ‘Babe ai na zata za a bar su sai mun ɗan huta, ka ga shekaran jiya fa na tare. Ko gajiyar biki ma ai ban gama hucewa ba.’ ‘Haba, ai sai ku huta tare, kin san su ma fa they missed home don tunda mahaifiyarsu ta rasu rabonsu da gida.’

‘Allah sarki, ni kaina ina ɗokin dawowarsu nan but babe please ka bari koda zuwa next week ne na ɗan gama kwance kayana.’ ta faɗa da muryar magiya da lallashi. Ya ture farantin gabansa ya sake cika kofinsa na zobo, ya ɗan gatsina fuska yace ‘Ok, amma dai  ba za su ji dadi ba. Ɗazu muka gama waya da su suna ta ɗokin dawowa wajenki.’

Ya miƙe ya nufi wajen TV yayinda ita ma ta miƙe ta fara tattara kwanukan tana cewa ‘Allah sarki,  in sha Allah next week da ni za mu je mu ɗaukosu ka ga daga nan ma sai mu biya gaba ɗaya mu gaida Mommy mu gaida su Hajiya sai mu dawo gida.’

‘Umm!’ ya amsa yana canza channel ɗin TV. Ta cigaba da kwashe kwanukan tunani kala-kala yana yawo a ƙwaƙwalwarta; ta yi zaton yana ɗokin kasancewa da ita, ta yanda zai bari su ɗan ƙara fahimtar juna kuma su more amarcinsu kafin ya ɗauko yaran amma shi yana maganar yau. Babu ƙananan yara a gidansu amma kusan  kullum suna tare da yaran Yaya Mama, ta san yara ba za su bari ta mori amarcinta ba tunda su rayuwarsu suna buƙatar kulawa ne kullum.

Musamman tunda ga Shukra mai shekaru uku kacal.  Sati ɗayan ma da tace a ƙara kawai dai daurewa ta yi don ita da a tunaninta ta sami kamar wata uku a gidan kafin ya kawo mata yara tunda a can ma inda suke ana kula da su. To amma bata da wani zaɓi, zuwa next week ɗin sai ta bi shi su je su ɗauko yaran.

Ana fara kiran magriba ya yi alwala ya ɗauki mukullin motarsa, ya same ta a kitchen tana tsugune a tsakiyar kitchen ɗin tana tuka tuwon shinkafa. Motsinsa ya sa ta saurara da tuƙin tuwon ta juyo, ta dube shi tace ‘Fita za ka yi? Ko masallaci za ka je?’

‘Eh, daga masallacin zan wuce na dubo yara sai kuma na wuce wajen Hajiya.’  Ta ɗan langabe kai ‘Babe ai da ka dawo, ni ma sai na shirya mu je na gaida Hajiyan.’ ‘No ki bari next week za mu je tare.’ Ya amsa yana duba wayarsa.

Ta saki tuƙin tuwon ta miƙe ta nufeshi da niyyar ya rungume shi, sai dai ya ɗan kauce don haka ta gefe ta rungumo shi. Jikinta ya ɗan yi sanyi ta sumbaci kumatunsa tace ‘A dawo lafiya Babe, I  will wait for you idan ka dawo sai mu yi dinner tare. Ka gaida su Hajiya.’ ‘Ok.’ ya amsa sannan ya fice.

A parlor ya sami Alhaji, bayan sun gaisa suka ɗan taɓa hira. Alhaji yace ‘Wai ka ɗebo yaranka  kuwa?’ ‘Ban ɗebo su ba, tace a bari sai zuwa next week idan ta gama hutawa.’ Yana wani kau da kai. ‘To babu laifi; amma fa idan ka ɗaukosu to ka saka ido, ka san mata yanzu ba sa son riƙo. Idan  ba ka yi wasa ba haka za a mayar maka da yara kamar almajirai a gidanka.’

‘In sha Allah zan kula, duk da ma na kula kamar ba ta da muguntar.’ ‘A a, basu fa da tabbas, kai dai ka sa ido. Kuma ka dinga bincikar duk motsinsu.’ Ya faɗa yana nuna shi da yatsa. Suka ɗan sake hira sannan ya shiga wajen Hajiya inda ya same su ita da Yaya Jidda suna hira; da yake ita gidanta kusa da gidan ne wataran ma sai an yi sallar Magriba take zuwa.

Bayan sun gaisa suka cigaba da hirarsu gaba ɗaya. Jimawa kaɗan Yaya Jidda tace ‘Musty ina amarya? Tsohuwar sirikar taka ta baka yaran ko har yanzun ba za ta bayar ba?’ Ya gyara zama yace ‘Haba, sai kace ita ta haifa min su ai dole ta ba ni su.’ Hajiya tace ‘Sai yaushe za ka ɗauko su?’

‘Tace wai a bari ta huta zuwa next week, don ni da yau ma na so a ɗaukosu. Yanzu ma idan na fita zan je na kai musu biscuits ɗin da na saya musu.’ Yaya Jidda tace ‘Wai wacece tace a bari ta huta? Khadeejan?’ Yace ‘Eh, tace wai a bari ta huta ta gama ware kayanta kafin a kawo su.’ ‘Kai Musty! Yanzu kai har ka ba ta dama su da gidan ubansu sai ta ga dama za a kawosu, to me  ta yi ya gajiyar da ita har take buƙatar hutu.’

‘To ni ma dai haka na gani, amma dai zan ga yanda za mu yi.’ Ya faɗa yana kauda kai. Hajiya tace ‘To ka dai dinga kula sosai don kada ta dinga cutar da su, ka sa ido sosai don yanzu  mata ba tausayi ne da su ba.’ Yaya Jidda tace ‘Musamman gashi tun yanzu ta fara iyayi da kafa dokoki, a jira ta huta kafin a kawosu gidan ubansu.’

Haka suka gama hirarrakinsu suna jaddada masa ya sa ido sosai kada Khadeeja ta cutar da yaransa; ya yi musu sallama ya wuce gidan iyayen Ma’u wajen yara. Sai da ya tsaya a hanya ya saya musu yoghurt da gasasshiyar kaza sannan ya wuce.

Yana shiga bayan sun gaisa da Mama ta turo masa yaran suka same shi a guest room. Suka karɓi kajin da yoghurt suka kai wa Mama; wadda ta riga ta saba idan ya kawowa yaran abu to ba zai ba ta ba sai dai ya ba wa yaran a hannunsu su su kai mata; sannan suka dawo wajensa suna ta murna don su sun shirya kayansu tsaf yau za su tafi wajen Anti Khadeeja.

Hakan ya yi masa daɗi don dama hakan yaso. Nan da nan suka sheƙa cikin gida suka fara fitowa da kayansu, Anti Nihla kanwar Ma’u ta taya su duk suka fito da akwatunansu. Mama ta fito ta same shi, bayan ta zauna tace ‘Ga mutanena nan tunda suka ji uwarsu ta tare sun kasa zaune sun kasa tsaye fa, ni da muka yi da su sai an kwana biyu amma ka ga suna ganinka sun fara fito da kaya. Kayan nasu ma fa wasu suna wajen wanki.’

‘Wallahi kuwa, ai babu komai daga baya sai na zo na karɓar musu sauran, kuma ma ai za su dinga zuwa in Sha Allah.’ Ya ba ta amsa. Haka aka gama fitar da kayan aka zuba masa a mota ya kwashe su suka kama hanya, suna ta murna za su je wajen Anti Khadija.

Tunda ta gama tuwo ta yi Sallah sai ta yi wanka ta shirya cikin bum short ɗinta da wata figalalliyar riga, ta sha turare sai ƙamshi take yi ga gidan ma ta yi fes da ko ina ta kunna turaren wuta ƙamshi sai tashi yake a hankali.

Tana kwance a kan three-seater tana danna waya ta jiyo motarsa ya buɗe gate yana shigowa, ta tashi zaune ta ɗan gyaggyara tana jiran ya shigo ta taro shi daga bakin kofa. Mintuna kaɗan ta fara jiyo motsinsu a kofar shigowa parlor, ya zura mukullin yana ƙoƙarin buɗewa yana cewa ‘Afaf riƙe hannun Shukra na buɗe kofar.’

Ta ɗan yamutsa fuska tana ƙoƙarin ta gane shi da su waye; tas ta jiyo muryarsu gaba ɗaya. Ta ɗan rikice kaɗan tana mamakin dalilin da yasa ya taho da su bayan ya amince sai next week. Ta  jiyoshi yana zare mukullin daga jikin kofar; ta kalli jikinta yanda take kusan tsirara. Ta yi wuf ta zaga bayan kujera daidai lokacin da yake sako kai cikin parlor ɗin, ta ɗauki jilbab ɗinta wanda yake ajiye a saman kujera ta saka.

Tana ƙarasa saka jilbab ɗin suka shigo da gudu bayan ya shigo, suka haɗa baki gaba ɗaya ‘Anti  Khadeeja, Anti Khadeeja.’ Suka karasa da gudu suka rungume ta suna murna. Haka ta yashe baki tana amsa gaisuwarsu, ta ɗauki Shukra tana cewa ‘Shukra baby, ya Mama?  Kin baro ta tana kuka ko?’

Cikin muryarta ta gwaranci tace ‘Ba kuka take ba, ta ce ma na gaisheki.’ ‘Ina amsawa.’ Ta ajiyeta ta kama hannun Habib tace ‘Ya Habib, welcome.’ Ta kalli Mustapha suka haɗa ido, ya yi sauri yace ‘Sun ƙi bari na na taho sai da suka biyo ni, ga  kayansu nan sai ku shigar.’ ‘Uhm, bari mu gani.’ Ta amsa murya ƙasa-ƙasa.

Ta ɗauki babban akwatin nasu ta ja ta nufi ɗakin yaran tana cewa ‘Afaf ɗauko wannan jakar mu kai ɗaki.’ Afaf ta kama jakar tana ƙoƙarin ɗagawa Abbansu yace ‘Ke ajiye jakar nan ba za ki iya ɗauka ba.’ Suna tsaye a ɗakin a gaban wardrobe tana tambayar Afaf ina jakar Abbansu ya shiga ɗakin ɗauke da jakar, yace ‘Ga ta nan, gani na yi ba za ta iya ɗaukowa ba na ɗauko mata.’

Ta yi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, Yaya Afaf ai ba raguwa ba ce, jakar ma da babu nauyi.’ Suka yi dariya gaba ɗaya, ya ja yaran suka fice daga ɗakin suka bar ta ita kaɗai tana ƙoƙarin samarwa akwatin kayansu waje. Bayan ta ajiye akwatin a kusa da mudubi ta ɗan ja baya ta ƙare  wa ɗakin kallo; komai tsaf yake tunda an share lokacin da ana kafi sai dai ba a shimfiɗa zanin gado ba a kan babban gadon nasu. Bata san a ya suke kwana ba kafin a aurota amma dai tana  jin a kan gadon suke kwana duka. Ta fito ta same su a parlor sun baje suna kallo suna ta yi wa  Abbansu surutu.

Ta dube su tace ‘Bari na ciro hijabin nan Afaf sai ki tayani mu gyara ɗakin. Abbansu yace ‘Wannan ce za ta yi wani gyaran ɗaki? Babu abinda ta iya fa.’ Ta yi ‘yar dariya tace ‘Bari ka gani.’ Ta shige ɗakinta; tana shiga ta cire hijabin ta jefa kan gado, ta ƙarasa gaban wardrobe ta buɗe tana duban babban rigar da za ta saka. Wani malolo ya tokare mata maƙogoro saboda takaici; to ta ina za ta soma? Haka kawai ya kwaso mata yara a wannan daren. Da ya gaya mata ma ai da tuni ta gyara ɗakin. Ta ja gajeren tsaki a Fili.

Motsin shigowarsa ne ya katse mata tunanin, ya nufota yana cewa ‘Na zata a nan ɗakinki za su kwana ai.’ Ta ɗan goge idonta ta juyo tana cewa ‘No, gara kawai na gyara musu ɗakinsu tunda babu wata ƙura da yawa a ɗakin sai su kwanta a can.’ Ya ɗan taɓe baki ‘Ok, amma dai za ki dinga zuwa kina duba su ko?’

‘Eh mana wannan ai dole ne.’ Ta amsa tana ɗan juya jikinta. Ya juya ya fita ba tare da ya ko kalli jikin nata ba. Ta kalle jikinta ta ɗan murguɗe baki; yau dai  kwalliyarta ta tashi a aikin banza kenan. Ta janyo babbar riga a wardrobe ɗin ta saka, ta sa hula ta rufe gashinta sannan ta fito. Kai tsaye  ta wuce kitchen ta ɗauki tsintsiya da parker, ta fito parlor ɗin ta dube su tace ‘Taso Afaf, maza mu gyara ɗakinku ku sami wajen kwanciya.’

Ta wuce ta barsu, a tunaninta yarinyar za ta biyo bayanta. Sai dai har ta shiga ɗakin ta fara ƙoƙarin sharewa babu motsin tahowarta, ta ɗan dakata da sharar da take yi ta kwala mata kira. A maimakon yarinyar ta amsa sai Abbansu yace ‘Abinci muke ci.’

Ba tare da ta amsa ba ta sunkuya ta cigaba da sharar, har ta ɗan yi nisa a sharar sai kuma ta tuna cewa ya yi abinci suke ci fa; to wanne abincin? Tuwon da ta tuƙa da shinkafa gwangwani 1 da Rabi ɗin ya tasa yaransa a gaba suke cinyewa? Bayan ta gaya masa za ta jira shi ya dawo su ci abincin dare tare? Tuwon ma da gaba ɗayansa malmala uku ne ta tuƙa saboda ta san miyar ba za ta isa su ci ɗumame ba.

Har ta ajiye sharar ta nufo parlor ɗin sai kuma ta tuna idan ta zo me za ta yi a kai, don haka sai  kawai ta cigaba da sharar ta tana fatan Allah ya sa su rage mata tuwon. Ta share ɗakin ta karkaɗe ko ina sannan ta shimfiɗa zanin gadon da ta ɗauko daga ɗakinta. Ta kalli ɗakin ta ga ko ina ya yi tsaf, sannan ta ɗauko sharar da ta kwashe ta fito.

Suna zaune a kan dining table suna ta cin tuwo shi da ‘yayansa, kafin ta yi magana Abbansu ya dubeta yace ‘Yauwa ɗan ƙaro mana tuwon nan Habib bai ƙoshi ba, ga Shukra ma kamar za ta ƙara.’ Ta ɗan zaro ido tace ‘Wai kun ciye na flask ɗin?’ ‘To nawa yake, ai ba shi da yawa.’ Kafin ta ba da amsa Nasreen tace ‘Kuma miyar ta yi daɗi Anti.’ Ta yi murmushin yake tace ‘Shikenan dama na dafa, ko ni ma ban ci ba.’

Habib yace ‘Abba ni fa ban ƙoshi ba, dama bamu ci abincin dare ba lokacin da muka taho gashi mun manta ba mu karɓo kazar mu ba a wajen Mama.’ Abbansu ya dube ta yace ‘Yanzu ya za ki yi da Habib? Yunwa yake ji.’ ‘Akwai ragowar bread sai mu raba ni da shi mu sha da tea, don gaskiya yanzu ba zan so ɗora tukunya ba.’ ba tare da ta saurari amsarsu ba ta wuce kitchen da sharar a hannunta.

So take ta sami waje ta yi kuka ko ta ji sanyi a ranta, don haka ba tare da ta kalli wajen ba ta jefa sharar ta juya sink ta fara wanke hannunta. Abbansu ta jiyo a bayanta yace ‘Khadeeja, daurewa fa za ki yi ki dafa wa Habib Indomie don shi ba ya cin bread kuma kin ga ai ba ya kwana da yunwa  ba.’

Ta kalle shi suka haɗa ido tace ‘Babe na gaji ne wallahi, ni ma ina son tuwon amma na haƙura zan ci bread.’ Ta ɗan saurara tana kallon yanda yake ƙara haɗe rai, sai kuma cikin sanyin murya tace ‘Amma Afaf ta zo na kunna mata cooker ta dafa musu Indomie ɗin.’

Ya kalle ta sheƙeƙe yace ‘Wai ke me kika ɗauki Afaf ne she’s only eleven babu abinda ta iya na aikin gida. Idan ta girma dai ta koya but ki daure kawai ki dafa masa.’ Ta juya ta ba shi baya saboda hawaye ne yake shirin ƙwace mata, ya juya ya fice ya bar mata  kitchen ɗin.

Ta share hawayenta ta sauko da tukunya ƙarama ta zuba Indomie ɗin da ruwa da komai ta kunna wuta ta ɗora. Ta koma ta jingina da sink ta tsaya ta kafa tagumi; yanzu shikenan har ta gama amarcin, ko awa biyu yaran nan ba su yi da zuwa ba amma sun gundire ta, anya kuwa za ta iya wannan rayuwar. Ko da yake dai yanzu suka zo ta san ba su fahimce ta ba ita ma kuma ba ta fahimcesu ba; amma dai za ta ɗora su a saiti kwanan nan.

Tana cikin juye Indomie ɗin suka shigo kitchen ɗin suka wanke hannuwansu, sai dai abinda ya b ata mamaki babu wanda ya ɗauko plate ɗin da ya ci abincin ya kawo kitchen ɗin; duk a dining table ɗin suka baro mata. Ta gama juye Indomie ɗin ta miƙawa Habib bayan ya gama wanke hannu; haka ta fito ta kwashe kwanukan daga dining su kuma suna zaune suna kallon TV. Ta  haɗo shayi ta ɗauki guntun bread ɗinta ta wuce ɗaki.

Bayan ta gama shan shayin ta ɗauko kofin ta fito, tana isa gaban sink ɗin za ta ajiye kofin ta ga Indomie ɗin da ta dafawa Habib ko rabi bai ci ba kuma ga dukkan alamu ya ƙoshi kenan. ‘Mtsewww’ ta ja tsaki a Fili. Ta wanke hannunta ta fito daga kitchen ɗin. Har za ta wuce ɗaki Abbansu yace ‘Ki zo ki shirya su sun fara jin bacci kin ga goma har ta gota.’

Ta juyo ta dawo, ta ɗauki Shukra wadda ta riga ta fara gyangyaɗi Afaf, Habib da Nasreen suka bi bayanta. Sune suka nuna mata kayan baccinsu ta taimaka musu duk suka yi brush sannan suka shirya, ‘yan matan gaba ɗaya suka haye gadon. Ta kalli gadon ta ga ma ba zai ishesu ba don haka ta koma dakinta ta dauko katifar da aka kawo mata saboda baƙi ta shimfiɗawa Habib a ƙasa. Ta gama tsaf za ta kashe musu fitula Nasreen yace ‘Anti ba a kashe mana fitila sai mun yi barci.’

Ta mayar da fitilar ta kunna musu sannan ta fice daga ɗakin, ta wuce Abbansu a parlor ta shige ɗakinta. Ta riga ta gaji sosai don haka ita ma kayan bacci kawai ta saka ta rufe ɗakin nata ta wuce ɗakinsa, ta kwanta ta rufe idonta.

Lokacin da Khadeeja ta fito daga ɗakinsa ya zata ɗakinsu Afaf za ta koma don su kwana tare, amma sai ya ga ta shige ɗakinsa. Ya tashi ya shiga ɗakin yaran inda ya tarar dukansu sun yi  bacci, don haka ya kashe musu fitilar ya fito daga ɗakin. Ya kashe fitilun falon ya shige ɗaki.

Tana kwance a kan gado kamar ma bacci take yi, don haka ya ƙyaleta. Bayan ya gama shirinsa ya kwanta, ya miƙa hannu ya taɓa ta, ta juyo ta buɗe ido tace ‘Babe, ka shigo?’ ‘Um.’ Ya amsa a gajarce. Ta fara ƙoƙarin matsowa jikinsa, ya tashi zaune yana cewa ‘Kin baro yara su kaɗai, kin ga daga nan ma ai ba lallai ki jiyo motsinsu ba. Ni da na zata ma tare za ki kwana da Shukra a ɗakinki fa,  she’s just 3 ba ta saba kwana ita kaɗai ba.’

Ta ɗan matsa ta koma inda ta baro tana cewa ‘No, they will be fine fa, ba ka ga a tsakiyar yayunta na sata ba kuma duk fa sun yi bacci. Ka ga na ma saka alarm wajen biyun dare zan je na dubasu sai kuma da asuba.’ ‘Uhm, amma dai da kin daure kin kwana da su ɗin.’

‘Kada ka damu ina jinsu.’ Ta faɗa sannan ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya ta rufe ido.  Haka kawai zai ce ta je ta kwana a cikin yara; to ai ko ‘yar da ta haifa ce shekara uku ai raba wajen kwana za su yi. Ba zama ta fara wannan aikin ba balle ya sallamawa yaran ita.

Har barci ya fara ɗaukanta suka ji an murɗa ƙofar, ya riga ya murɗa mukullin da ya shiga don haka sai ƙofar ba ta buɗe ba. Aka ƙwanƙwasa a hankali, suka tashi zaune tare shi da Khadeejan. Kafin suce wani abu Nasreen tace ‘Abba Shukra ce ta tashi za ta sha shayi.’ Ya kalli Khadeeja yace ‘Oh, na manta ban gaya miki ba tana farkawa shan tea da daddare, tunda  aka yaye ta ta saba. Ki je ki haɗa mata shayi, daga ta sha za ta koma bacci.’

‘Shayi? A wannan daren? Ko fa 4 hours ba su yi ba da cin tuwo, ikon Allah.’ ‘Idan ba ki ba ta ba haka za ta yi ta yi wa mutane kuka har sai an ba ta, kije ki haɗo mata gobe sai  ki haɗa ki sa a flask kafin ta kwanta.’ Ya faɗa yana sake ɓata rai. Ta ɗaura zaninta a ƙirji ta sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin cike da takaici.

A tsakiyar gadon ta sami Shukra tana kuka, duk yanda zuciyarta ta kai ga ƙuna a wannan lokacin dole ta danne fushinta. Ta miƙa mata hannu tana ɗan murmushi tana cewa ‘Ahh! Sorry Shukra, ya aka yi? Kukan me kike yi? Cikin shessheƙar kuka da gwarancinta tace ‘Tea.’

Ta zauna a gefen gadon ta rungume ta tana shafa bayanta tana mata magana cikin lallashi ‘Ya  isa, ya isa. Da safe ke zan fara haɗawa shayi kin ji Baby Shukra, kin ga dare ya yi ko? Mu yi bacci da safe sai mu sha tea ko, har da bread ma da ƙwai ko?’

Ta gyaɗa kai alamar eh, amma fa hawayenta ya ƙi daina zuba har da shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallaɓa ta yayin da Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara ɗaukanta. Abbansu ya ya turo ƙofa ya shigo ɗakin, Shukra ta leƙo ta kafaɗar Khadija cikin shessheƙa tace  ‘Abba tea zan sha.’

Ta ƙwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya ɗauke ta ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti ba ta ba ki shayin ba?’ ‘Tace sai da safe.’ ta faɗa tana shessheƙa. Ta mike ta rungume hannuwanta a ƙirjinta ta kalle shi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka bar ni da ita za ta koma bacci kuma a hankali za ka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallaba ta idan ta yi bacci zan taho.’

Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka za ta kwana da yunwa. She’s only 3, idan ta girma da kanta za ta daina duk yayyenta ma haka babarsu take rainonsu.’ Cikin ƙosawa tace ‘Kai dai ka bar ni da ita mana, I promise you she will be just fine.’

Ta ƙaraso kusa da shi, ta miƙa hannu ya dafa kafaɗarta yana cewa ‘Kin ga, ki yi haƙuri ki haɗo mata shayi kada ki saka ta kwana da yunwa tunda ba ta saba ba. A hankali za ki ga da kanta za ta daina.’ Murya ƙasa-ƙasa tace ‘Ohkk!’

Ta wuce ta bar shi a nan ta nufi kitchen; tea at 1pm, wannan wane irin tashin hankali ne? Idan da ya kyale su ta san tabbas za ta raba ta da wannan shan tea ɗin amma har wani cewa yake yi kada ta barta da yunwa. Ta ƙarasa kitchen ɗin ta haɗo mata tea a kofi ta ɗauko ta fito. Tana zuwa ta same shi zaune a gefen gadon ragowar yaran duk suna ta baccinsu yayin da yake zaune rungume da Shukra; har bacci ya fara ɗibanta amma tana shiga ya ɗagata yace ‘Yauwa  Baby tashi ga shayinki.’

Ta tashi tana muttsike ido, ya miƙe tsaye ya nunawa Khadijan wajen ta yana cewa ‘Zauna sai na ajiye miki ita idan kin gama ba ta tayi bacci kya taho.’ Ya ajiye mata ita a kan cinyarta ta fara ba ta shayin sannan ya fice ya bar su.

Bayan ta gama ba ta shayin ta saka ta ta yi fitsari sannan ta kwantar da ita ta ɗan jijjigata bacci ya  fara kwasarta sannan ta wuce ɗakin. Ko da ta shiga ɗakin ya riga ya yi bacci, don haka ba tare da  ta kunna fitila ba ta lalubi waje ta kwanta a gefen gadon. Motsin kwanciyarta ne ya farkar da shi, ya ɗan matso ya rungumota ta baya yana sumbatar bayan wuyanta. Ta ɗan motsa tace ‘Mmmm!’

Yace ‘Kin san gobe yara za su school ko? Sai ki tashi da wuri don ki shirya su.’ A take jikinta ya yi sanyi; gaba ɗaya ma ta manta da wannan tunda ita ta riga ta sanar da ƙawarta su yi mata attendance ba zata koma ba sai ta yi sati. Ya cigaba da lalubenta tana ƙoƙarin zamewa, saboda ita gaba ɗaya ma komai ya fita daga ranta;  a halin yanzu ma kuka take son yi. Sai dai haka ta haƙura ta bar shi ya yi yanda ya so sannan ta  kwanta tana fargabar yanda za ta tashi nan da awowi kaɗan ta cigaba da hidima.

Ana fara kiran assalatu ya tasheta daga bacci, sai da ta yi da gaske sannan ta iya saukowa daga kan gadon. Ta yi alwala ta wuce kitchen tunda da ɗan sauran lokaci kafin a tada Sallah. Ta tsaya a tsakiyar kitchen ɗin tana tunanin inda za ta fara; a hankali dabara ta faɗo mata; macaroni da sauce za ta dafa musu in ya so sai ta dafa indomie da kwai su yi breakfast. Nan da nan ta ɗora  sannan ta ɗebo tsofaffin flasks ɗinsu da ta gani a store ta wanke sannan ta je ta yi Sallah.

Ta zata idan ya dawo daga masallaci zai tsaya ya taya ta shirya su amma ga mamakinta sai ya wuce su a parlor ya koma ɗaki ya kwanta ya cigaba da baccinsa. 7:15 am ta gama komai duk ta yi musu wanka sun shirya, suka zauna a dining table ta kawo musu abinci ta zubawa kowa Indomie da dafaffen ƙwai guda ɗaya. Daga fuskokinsu ta san ba  indomie suka so ci ba, suna cikin cin abincin yayin da ita kuma take zaune a table ɗin tana ba wa Shukra a baki Nasreen ta kalle ta tace ‘Anti da ma dankali da ƙwai kika soya mana.’

Ta kalle ta tana murmushi tace ‘Saboda kar ku makara shi yasa na yi sauri na dafa Indomie, but insha Allah weekend idan babu makaranta sai a soya muku dankali kin ji. Yanzu maza ki cinye kafin Abba ya fito ya kai ku school.’

Suka cigaba da cin abincinsu. Jimawa kaɗan Abbansu ya fito yana riƙe da mukullin mota, suka haɗa baki gaba ɗaya suka gaishe shi. Bayan ya amsa yace ‘Maza ku gama mu wuce school kada ku makara.’ Ya kula da ragowar ƙwai a plate ɗin kowa banda Habib, ya dube shi yace ‘Kai ina naka ƙwan?’ Yace ‘Shi na fara cinyewa Abba.’ Nasreen tace ‘Abba ni ina son dankali, Anti tace ba za a dinga soya dankali ba sai weekend.’ Ta  langabe kai kamar abun tausayi.

Ba tare da ya kalli Khadeejan ba yace ‘No, za a dinga soyawa kada ki damu, maza ki ci abinci mu tafi.’ Tana jinsu ta kawar da kanta, don sai dai idan shi zai dinga tashi ya soya ita ba za ta iya soya dankali da sassafe ba. Nan da nan suka gama; Habib ne ya fara miƙewa har ya juya tace ‘Ɗauke plate ɗinka da cup ɗin ka kai kitchen.’

Ya ɗauke plate ɗin ya tafi da shi, suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta miƙe sai ta ɗauke plate ɗinta ta wuce da shi. Suka ƙarasa shiryawa suka fice tare da Abbansu. Kafin ya dawo ta soya dankali da ƙwai ta jera a dining table sannan ta wuce ɗaki; wanka za ta shiga sai kuma ta tuna ko da ta yi wankan dai kitchen za ta shiga ta yi wanke-wanke ga shara, don haka ta ga gara ta bari idan ta gama aikin ta yi wankan.

Sai da ya yi wanka ya shirya sannan ya fito a shirye, kai tsaye ta riga ta shirya abincin a dining  table don haka suka zauna. Yana buɗe kwanon yace ‘Sai da suka tafi kuma kika soya dankali?  Sun fi son soyayyen abinci idan za su tafi school.’ Ta ɗan langabe kai ‘To ai Babe ba zan iya soya wani abu before 7am ba, da a ce ma dai ina da mai aiki ne. Amma hakan ma weekend zan soya musu in sha Allah.’

‘To ai da kin bari sai weekend ɗin ma ci gaba ɗaya, yanzu idan sun dawo ai za su ga ɓawon ba daɗi ai kuma ma Shukra za ta gaya musu tunda ita ta ci. Mai aikin ma kuma za a ɗauka.’’Uhm.’ Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba.

Gaba ɗaya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba za ta ba wa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta. Ya gama cin abincin ya fice ya bar su ita da Shukra. Sai wajen 10am ya kirawo ta a waya, bayan ta ɗauka yace ‘Mantawa na yi ban gaya miki ba idan 1pm ta yi sai ki je ki ɗauko yara daga school.’

Ta ɗan yi shiru don ta zata shi zai ɗaukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a ƙasa?’ ‘No, kin san school ɗin ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’ ‘Ok.’ Suna gama wayar ta miƙe ta ɗora abincin rana don ta gama da wuri. Lokaci yana yi ta ɗauki  Shukra suka tafi suka ɗauko ‘yan makarantar. Suna dawowa bayan sun huta ta shirya su suka tafi  islamiyya.

Dab da magriba ya dawo. Bayan ya huta yana zaune a parlor shi da yaran tana jiyo shi yana  tambayar Afaf abinda aka yi da baya nan, an ɗauko su da wuri daga school? Sun ci abincin rana?  Me suka ci? Sun makara a islamiyya? Haka dai ya cigaba da tambayoyinsa tana kitchen tana jiyo su, kamar ta fito ta yi magana sai kuma ta share ta cigaba da abinda take yi; tunda dai ta san  ba ta yi musu komai ba. A haka suka ƙarasa satin nan tana bakin ƙoƙarinta wajen kula da yaran nan gaba dayansu.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Cire Tufafi
Labarin na GabaGyara Kayanka
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.